NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Kuka mai cin rai Mama ta fashe dashi tana mai dur ƙusawa a ƙasa saman kafafuwan ta, da sauri na ɗago ta, nace, “Mama na daɗe da yafe maki Allah ya yafe muna baki ɗaya “.

Riƙa ta nayi muka dawo cikin gidan a gurin Umma taje neman yafiya kuma Umma tun kafin tayi maga ta ce, ta yafe, haka su Inno duk sun yafe kowa ya yafi kowa, sai zaman lafiya akeyi, da godiya a gurin na, sai da na fara jin haushin hakan har ina ɓuya, sai da suka nemo ni.

Satin mu biyu da dawowa aka sake gyara mani jiki tare da kitso da lalle, kullum cikin nasiha su Inno Mama da YAya sukeyi mani, mai shiga ciki, tattalin miji tsabar ƙirsa iri daban_daban wani lokacin har kunya suke bani, gyaran jiki kam ciki da waje, komai zam_zam sai sam barka.

Yau muna zaune Yaya ta bani zuma ina sha mukaji tsayuwar motoci, Shuraim kuwa da gudu ya sauka jikin Inno yayi waje yana kiran “Daddy Daddy “

Duk mun ɗauka shirmen sa ne, kawai naji muryar Salma tana faɗar, “Antyn mu Narjeesh nayi fushi gaskiya”

A da sauri na tashi na tar yota muka baje a falo suka shiga gaisawa da mutanen gidan, na ce, “Inno Gaggon Shuraim ce, kan war Daddyn Shuraim ce, fa”.

A da sauri su Shamsiyya dasu Mariya suka zazzauna a kusa da ita sai gaisuwa akeyi, Amrah ta kawo mata abun taɓawa, fira kawai mukeyi, Daddyn Shuraim ne ya shigo ɗauke da Shuraim suna dariya Muhseen yana biye dasu, su Mom ne suka shigo harda Dad, da sauri muka tarbe su, suka zazzauna suka shiga gaisawa dasu Inno, Baban mu ne, ya fito cikin farin ciki, suka gaisa dasu Dad, Umma kam ana gama gai sawa ta bar gurin, sai su Inno ne a gurin, Mom tace, “to mufa yau mun zo tafiya ne da ‘yata da jikan mu da fatan zaku yarda da ƙoƙon barar mu”.

Dariya aka shiga yi, nikam jinin jiki na, nasha, Dad ya ci gaba da faɗar, “kuyi haƙuri da abunda ya faru gashi dai suna da Aure amman ba’ayi biki ba, duk da mukam a can london mun sha bikin mu babu ango babu Amarya, gashi kuma shima Shuraim ba ayi hidimar bikin haihuwar sa, ba, amman idan ranar cikin shekara biyar ya zo da haihuwar zamuyi masa bikin sa, dafatan zaku duba yanda abun ya kasan ce, ku daure ku bamu, wannan kyakykyawan irin naku mai albarka, dan ci gaba da samun yaɗo”.

Dariyar manya su Baban mu sukayi, Baban ya ce, “to Alhamdulillah Narjeesah dai ta kuce daman iyayen ta, sun gama shiri, suna jira ne kawai daga gareku, kuma tun da Allah ya kawo ku, sai muce, Allah ya dai daita hankalin su, ya bada zuri’a mai albarka “.

Da amin aka amsa, Yaya tace, “to Salman Narjeesah abunda nake so daku shine, dan Allah ku zauna ku fuskan ci matsalar ku, kada ku yarda ko da Shuraim ne, ya gane cewar bakwa shiri a tsaka nin ku, ku zauna lafiya ku iyaye ne, kuma yan zun kun fara girma tunda Allah ya mallaka maku Shuraim, tarbiyar sa idan ta gyaru daga gare ku ne, idan kuma aka samu akasin hakan, Allah ma ya kyauta duk akan ku haƙƙin yake, dan Allah ku zauna lafiya Allah ya zaunar daku lafiya ya baku zuri’a mai albarka “.

“Amin” aka amsa sosai akayi muna nasiha mai shiga jiki, aka ce, naje nayi sallama da Umma su Amrah su kwashi kayan mu, su fito dasu waje.

Haka naje gurin Umma ina kuka nake neman yafiyar ta, ta janyo hannu na, ta zaunar dani a jikin ta, atake naji wani irin farin ciki ya mamaye ni, ta ce, “bani da matsala da irin tarbiyar da kike dashi, kuma nasan bayanin da zanyi maki su Inno sunyi maki fatana kawai shi, kiyi hakuri ki rungumi mijin ki da ɗanki, kada aji kanku, ina son naji kyakykyawan albshir nan da wasu watan ni daga gareki idan kikayi mani wannan saka makon to ki sanya a ranki, har ƙarshe rayuwa ta, ina cikin farin cikin da kika saka ni a cikin sa, kije Allah ya albarkacin ki da zuri,ar ki baki ɗaya “.

Amin na ce, na ƙara run gume Umma yau nice Umma take baiwa umarni tare da sanar dani burin ta,? A take na saka a raina Insha Allah, Umma zata dauwa ma da farin ciki, indai daga gare ni ne.

Tashi mukayi ta rako ni har gurin su Inno, ai kuwa duk kowa ya tashi tsaye suna dariyar farin ciki, da yabon wannan ranar wanda Baban mu da kasan ya ɗaga hannun sa a sama yana mai nuna godiyar sa a gurin Allah da ya nuna masa wannan ranar, ai kuwa kowa cike da farin ciki yake, hannu na da hannun Salman ta haɗa tayi muna addu’a sannan ta ce, “ku tafi Allah ya kare gaban ku da bayan ku ta kare idon maƙiya a kanku ya albarkacin zuri,ar ku baki ɗaya “.

Haka kowa yake amsawa da Amin cikin tarin farin ciki.

Har a gurin motoci suka rako mu ina zubar da hawaye muna shiga cikin motar, Inno ta rufe aka tayar da motar muka ɗauki hanya, Shuraim sai farin ciki yakeyi idan ya dubeni ya dubi Daddyn sa, sai yayi dariya”

Tafiya mukayi sosai babu mai magana a cikin mu, sai airport abun mamaki jirgin tafiya london kawai muka shiga, muna sauka motoci ne irin na alfarma suka ɗauke mu, nikam cike da al’ajab nake ƙarewa ko ina kallo a wayan ce, bamu tsaya ko ina ba sai a wata haɗɗiyar unguwa, kai Alhamdulillah a gaskiya kam london tayi ba ƙarya, nikam tun ina sa ran akawo, har bacci ya ɗauke ni, kawai can a cikin barci na, naji kamar ina a jikin mutum ai da sauri na buɗe ido na.

Ai kuwa na zaro ido waje da sauri na ce, “dan Allah ka ajiye ni, baka ganin mutane a gurin kuma gashi a tare muke dasu Mom? “

Dariya ya sakar mani ya ƙara shigar dani jikin sa, ya ce, “oh ashe dai ba tare nake da kurma ba, ai na ɗauka ke kurma ce, malama, kuma su Mom kam sun nufi nasu gidan mu ma, yan zun mun kusa isa namu gidan Shuraim yana gurin su, kuma nan ƙasar ba wani abu bane dan miji ya ɗauki madam ɗin sa, babu ruwan wani da wani, dan haka ba zan sauke ki ba, ke wai ma anya kuwa kina cin abinci kuwa”!?.

Nasan ba zai sauke ni ba, dan haka na saƙalo hannu na a wuyan sa, na maƙala, na ce, “aa bana cin abinci kullum sai an rufe ni a ɗaki ake cin abinci “

Ya ce, “haba dai nikam na sani, amman malam maka am, na ɗauki babbar mace amman har Shuraim ya fita nauyi? “

Da sauri na ce, “ai da gaske? “

Ya ce, “anya ma kuwa zakiyi kukan amarci kuwa? Nifa naga idon ki a tsai tsaye sai rainin dake tsakanin mu, anya kuwa ba, tun yau zamu fara amarci ba? “.

Rufe ido na nayi, shi kuwa ya samu gurin tsokana ta, har muka iso bakin get ɗin gidan da zamu shiga sai bashi girma mutane keyi, manya da yara, sunayi masa barka da zuwa, yam mata da samari ma, barka sukeyi masa, tare dani, ina jin su nayi kamar bacci nake yi har muka wuce gurin mutane muka iso bakin nasa gidan, aka buɗe muna ƙaton get ɗin muka shiga cikin harabar gidan, sai a matakalar da zamu taka na ƙarshe ya ajiye ni ya buɗe gidan muka shiga ina daga bayan sa, ya kunna glub a take gidan ya haske ko ina, kwashe kyallayen da aka rufe kujerun mukayi, nikam kwanciya ta nayi, ina kallon sa ya gama kwashe komai shima ya zauna a kujerar da nake kwance, a kusa dani.

Shiru mukayi zuwa can mu ɗan futa na tashi na ce, “mu fara gyara gidan sai muyi wanka muyi sallah mu nemi abincin da zamuci ko? “.

Dariya ya yi yace, “nima hakan naga zai fi”.

Ai kuwa a take muka hau gyaran gidan har ɗaku nan na ƙasa da sama, da kichin da bayi duk sai da muka tsab tace komai, san nan, na haɗa masa ruwan wanka ya shiga ni kuma na dawo falon na kunna kalli sai da ya fito ya saka kayan shan iska, nima na shiga nayo wankan na fito ke nan, naga ya a jiye mani kayan da zan saka na shan iska ina ɗaukar rigar da guntun wandon, na ajiye na ce, “kam lallai ma, taya zan iya saka wannan yan iskan kayan na fito falo, na zauna? Ni kam ba zan iya ba, haba kamar wata yar iska dai! ? “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button