
Hijab na saka, gashi towel ɗin ƙarami ne, baya rufe mani cinya ta, ai kuwa na soma faɗar “Daddyn Shuraim! Daddy Shuraim..! Kazo Allah ni ba zan yarda ba, haka kawai a ce, na rasa kayan da zan saka sai wannan kayan haba ɗan Allah, kuma kace naje na zauna kamar wata marar kunya? “
Ido rufe nake ta masifa, shi kuwa ya shiga cikin ɗakin ya harɗe hannayen sa, yana bina da ido, ganin ba zan dai na masifar bane, kuma ba zan buɗe idon bane, ya saka shi yin wani makirin murmushi, ya matso dab dani, ya fisgen hijab ɗin, ya riƙe a hannun sa, ya zuba mani ido kallona ya keyi tun daga sama har ƙasa, ko ƙyafta ido ba yayi.
Ni kuwa mutuwar tsaye nayi, cikin fir gici na, buɗe ido na zaro su waje, ganin abunda ban shirya ba, a kuwa da gudu na juya zan faɗa toilet na rufe kawai, taku biyu yayi ta tare ƙofar shiga bayin na faɗa jikin sa, ai ban san lokacin da na kwatsa masa wank uban ihu ba, sai da ya rufe mani baki da hannun sa.
Ya ce, “wallahi idan baki saka wannan kayan ba, yau sai dai ki zauna da wannan towel ɗin kuma ba zaki saka wannan hijab ɗin ba, ke nama fasa kada ki saka wasu kayan kiyi zaman ki a hakan kin fi ma burge ni, wallahi “.
Ai tun da naji yayi rantsuwa kuma dai naga ya ɗaure fuska kawai, na ce, “dan Allah Daddyn Shuraim kayi hakuri Allah zan saka kaga bama zanyi sallar ba, kaje kayi sallar kawai ni na yarda in dan wannan kayan ne Allah “.
Dariya ya yi, ya ce, wato dai aboki na ne ya zo, ashe dai nan da wata tara zaki sake haifo mani yan biyu, ko ƙuratul aini? “.
Jin nakeyi kamar na nutse saboda tsabar kunya amman Daddyn Shuraim ya sauya mani lokacin ƙan ƙani, kwata_kwata, ya ajiye kunya a gefe, sai zuba mani fitsara yakeyi.
Kuka na fara harda hawaye, ya ce, “ashe ko dai zan cire wannan towel ɗin yan zun sai naga yan da ake kukan shagwaɓa”.
Ai haɗiye kukan nayi, na ce, “nifa kukan yunwa ne nakeyi ba wani kukan ba”.
Dariya yayi yace, “haba dai ƙurratul aini, ai nasan halin basajar ki, yan zun jeki ki saka kayan bara na kawo maki pad da fant, na tausaya wa yar yarinyar nan, kai na gode wa Allah fa, na Auri yar shekara sha shidda gani da ɗa kusan shekara biyar kuma ita matar yan zun zata cika shekara ishirin kai nikam ɗan baiwa ne, yan zun take zama cikak kiyar mace, wayo Allah na….!, kai ƙurciya zallar ta “.
Rasa bakin magana nayi, daman tsokana ta ce, yakeyi kuma tsokanar ta samu shiga, dan hawaye naci gaba dayi”.
Da dariya ya mai dani gefe, ya je ya ɗauko kayan ya bani ya fita yana dariyar keta gashi da hijab ɗin ya fita, hawayen na shiga sharewa, shigo wa ya sake yi ya bani leda ya fita yana, lasar baki yana shafa sajen sa, da harara na bisa har yaja ƙofar.
Haka na shiga na shirya, na saka kayan rigar mai haɗe, da gidan bra, kuma hannun bra ne da ita, iyaka cibiya, ta tsaya, sai wandon iya karsa, cinya, kasa fito wa nayi, nayi zama na a cikin bayin gajiya yayi da jira na, yazo ya buɗe bayin ya shigo yaja hannu na muka fito waje bai bari muka haɗa ido dashi ba, muka dawo cikin falon ya zauna akan kujerar ya zaunar dani akan ƙafafuwan sa, ya janyo abincin da yayi order aka kawo masa, ya buɗe ya soma bani, a baki, ganin bai ma damu yanda nake shigewa cikin jiki na ba saboda kunya, sai da ya tabbar da na ƙoshi ya bani ruwa, sannan ya soma ci, har ya ƙoshi.
Ya ce, “to ki tashi kije ki shirya sai ki dawo muyi fira kuma idan baki dawo ba, da kaina zan je kin dai san sauran “. ya kanne ido ɗaya.
Tashi nayi jiki babu lakka na nufi cikin ɗakin, naje nayi sha, fa mai na fesa turare da humra nayi, sai yar powder da jan baki, na tashi gashi ina jin kunyar sa, haka na fito na samesa yana kallon labarai, naje na zauna a kusa dashi yasa hannun sa, ya dawo dani sosai a jikin sa, mukaci gaba, da kallon a tare, har naji bacci, a jikin sa na kwata ya gyara mani kwanciya, a take nayi bacci.
Shi kuwa koda ya gama kallon ya kashe kayan kallon, ya ɗauke ni, ya kaini, ɗaki ya kwantad dani shima ya shiya ya kwanta yayi muna addu’a, nikam saboda tsabar gajiya bacci sosai nasha, sai a suba na falka, ina buɗe ido kawai na tsinci kaina, kwance a jikin mutum da sauri na yuƙura zan gudu ya janyo ni nadawo ya ce, “gudun na miye madam? Bayan duk kin bi kun shure ni da ƙafafuwan ki, kin zubo mani yayun bacci “
Nikam ban san lokacin da na ce, “wallahi ban yarda ba, ina da ja ni bani da nauyin bacci kuma bana saleɓa, kai sai dai idan kaine kake yi, ni rabu dani, naje na gyara jiki na, malam, haka kawai kazo kana yi mani cin kashin kaji? “.
Dariya ya yi, daman burin sa ke nan yaga ina masifa, kuma iyakar gaskiya ta na keyi, tashi nayi nace, “ka bani kayan da zan sauya ni kam, wallahi ko kuma ka nuna mani inda suke kaji? “.
Ya ce, “aa malama zo ki doke ni, ki ɗauki kayan kin ji…? Matar Salman? Uwar ya’yan Salman yar yarinyar Salman, mai ƙuruciya, shagwaɓaɓbiya t…. Maman Shuraim ƙurratul aini, nikam yau dai da kai na zan yo maki wankan nan fa bari na tashi dai na cire maki wannan kayan “.
Ai at 3√6o na faɗa jikin sa, na rufe ido na shige jikin sa, sai dariya yakeyi, ganin ya samu abunda ya keso naji, kunya, sannan ya ce, “ni tashi mani a jiki kada ki karya ni, kin ga kayan ki can a wan can seat ɗorowar, kuma sau ran kan yan suna a ɗaya dorowar, maza jeki ki fito kizo muyi baccin safe”.
Kayan naje na ɗauka, na ce, “halan kayi sallar ne da zaka sake yin baccin? “.
Ya ce, “kina can kwance kiji fata mai laushi a baki sanin na tashi ko ban tashi ba, amman zan rama nikam dan ba zan yarda ba “.
Kyalesa nayi na shiga ciki bayin nayo wanka, da brush na shirya na fito, koda na fito yayi bacci, nadawo na kwanta a gefen sa, na kwanta sai bacci.
Sai sha biyu muka fito muka nemi abunda zamuci, bayan mun ci, muka fito muka nufi falo, ya ce, “muje ki sauya kayan nan mu fita ki gano gari”.
Cike fa farin ciki muka dawo cikin ɗakin ya ɗauko mani sweater da dogon wando, da gyale nayi rolling ɗin gyalen, shima irin shigar mu ɗaya, har ta kalmi, muka fito, hannu na a cikin nasa hannun, muka fita yawon shaƙatawa, kai nikam sai dai na ce Alhamdulillah.
Birnin london kam mun zaga shi sosai nida Salman tattali da soyayya da kulawa duk ina samu, a gurin Salman, ga tsokana kamar miye? Wata rana har sai taga ina kuka yake dawowa yayi lallashi, babu abunda na nema ba rasa a gurin Salman, gidan su Mom munje ya kai sau nawa, a gurin su ma nida Shuraim gata suke nuna muna, har gurin dan gin Mom ya kaimu, a masarautar su Mom kuwa kwana biyu ne kawai muke tsallakewa.
Zaune muke nida Daddyn Shuraim ina sha masa ƙamshi shi kuma sai famar dariya yakeyi, ya ce, “ke kuwa wannan haɗe ran fa ba zai hana anjima na sake yi maki wani wa’azin ba, keda naga harda su kabbara kikeyi mani, saboda tsabar ɗaukar wa’azi, ai my love, kin iya bada hankali gurin ɗaukar wa’azin Mr Salman Daddyn su Shuraim da ‘yan uwan sa “.
Filo na jefa masa ya ci, gaba da dariya, yana tsokana ta, na ce, “yau ma nawa ga wata ne? “
Ya ce, “oh zaki fara lissafin cikin wata nawa ne? Yau dai kwana ɗay… “
Da sauri na haye saman jikin sa, muka shiga ko kawa, dashi ina son rufe masa, baki, shi kuma yana son ƙasawa, sai da muka gaji muka baje a gurin.
Haka dai rayuwar mu, taci gaba tafiya cikin kulawa, da tattali da ƙaunar juna muna kiyaye duk wani abun da zai bamu matsala a zaman mu dashi, cikin ikon Allah watan mu biyar a ƙasar, wata ranar labara na tashi da ciwon ciki mai tsanani, a ruɗe ya ɗauke ni, ya kaini asibiti gwajin farko, aka sami kyakykyawan result, Allah ya bamu ƙaruwar cikin wata, ukku, da sati biyu, murna a gurin mu ba a faɗa, su Mom ya kira ya sanar dasu, ai kuwa koda muka dawo gida a nan muka same su harda Muhseen Mom Dad Shuraim,