NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Umma ce ta kalli Amrah tace, “Amrah kin sheda masa inda zai kai mu ko? “

Amrah ta goge hawayen da takeyi tace, Umma na sanar dashi amman Umma kina ganin su kawu Habu zasu yarda mu zauna a gurin su kuwa? Kin fa san halin sa da zafin zuciya ga rashin fahimta Umma ni wallahi tsoro nake ji”.

Umma dai kallon su kawai tayi ba tare da tace dasu uffan ba.

Sai ƙarfe tara na dare muka ƙarasa unguwar su kawu Habu sai gaban mu ke faɗuwa, dan kowa a tsorace yake, sauka mukayi aka fara sauke muna kayan mu harda mai motar, Umma ta bashi kuɗin sa, muka shiga cikin gidan a tsakiyar gidan muka sami kowa da kowa, Kawu yace, “ina fatan dai ba cikin nan ne aka haife ba, kuma kuka dawo mani dashi gidan nan ku raine shi a gidana ba”.

Shiru Umma tayi kafin ta ce, “kayi hakuri kawu, ka barmu mu kwana anan da safe zamuje mu nemo gidan haya sai mu koma a can kaga dare ne yan zun “.

Matar shi tace, “haka kawai zaku kwaso ƙafar ku harda kayan ku da shege ku zo muna gida cikin dare ai dai kwana ɗaya kika roƙa kuma shi zakuyi ehe! “.

Umma dai batayi magana ba, ɗakin aka bamu ɗaya har kayan mu, nidai ban samu na rimtsa ba dan nasan nice duk silar faruwar hakan, Umma ce naga ta tashi tayo alwala ta fara nafila, da addu’a yaron ne ya motsa wanda yake kwance a jikin Amrah da sauri ta tashi ta kawo mani shi tace, “dan Allah bashi yasha kin ga yaron akwai hakuri”.

Ansar shi nayi na fara gir_giza shi amman kukan yakeyi fitila Umma ta hasko mani, tun da naga hakan nasan mi take nufi, gyara shi nayi na soma bashi, kawai muka jiyo masifar kawu Habu da matar sa, suna faɗar “wannan wace irin jaraba ce haba ya zaku sakawa mutane hawan jini ku hanasu kwana? Nifa wallahi idan naga kun cika damuwar mu muda moƙwota sai dai muce kubar gidan nan “.

Shikuwa bawan Allah harma ya koma bacci, suka gaji da masifar su sukayi koma ɗakin su.

Tun da aka fito sallar Asubahi, muka gaisa da mutanen gidan muka fita ko karya wa bamuyi ba, muka fara neman gidan haya, har ƙarfe tara na safe bamu samu ba kuma bamu ci abinci ba, gashi ina jego, ganin hakan ne yasa Umma ta sai muna ƙosai da koko muka zauna Zauren wani gidan muka ƙarya muka tashi muka shiga yawon neman gidan haya, ga baki ɗaya sai da muka bar unguwar sosai zuwa sha biyu na rana Allah yasa muka dace kuma gidan babu kowa cikin sa ɗaki biyu ne da kichin da bayi, shekara ɗaya dubu, talatin haka muka biya anan aka barni nida yaron suka tafi gurin kwaso kayan.

Zaune nake na buga uban tagumi ina kallon yaron wanda nake jin yan zun ina kaunar sa, to amman ya ya rayuwar mu zata kasan ce ne nida yaro na, zuwa gaba, har yaushe ne zan saka Umma na da yan uwana farin ciki?.

Jin ana shigo da kaya yasaka ni dawowa hayyaci na, kawai na tashi na baiwa Nusaiba yaron ta ansa ta goya sa, ni kuma na taya saka kayan Umma ɗaki ɗaya muka saka mata gadon ƙarfen ta da da wadurof din ta da mu kuwa a ɗaya ɗakin muka saka gado ƙarami da katifa ɗaya, waje kuma aka saka durom naruwa da tukunyar ƙasa.

Kichin Umma ta shiga ta gyara komai da komai, kayan miya ta fito dasu zata fara jajjage da sauri Amrah ta ansa ta ce, “haba Umma kibar shi muyi mana ai ke ya kama ta ace kin futa kawai”.

Umma ta ce, “naga kun gaji da yawa kibar shi kije ku futa, taliya ce kawai zan dafa muna”.

Dariya Nusaiba tayi tace, “Umma Allah ya raba mu da fu kina aiki muna zaune muna kallon ki da ran mu da lafiyar mu”.

Dole Umma tayi dariya wadda rabon da muga dariyar ta tun kafin cikin jiki na ya bayyana sai yau dan haka kowa sakin baki da hanci ya yi yana kallon Umma, itama sai ta daina dariya ta zo ta wuce ni ta shiga cikin ɗakin ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa ta zauna, tashi nayi na shiga cikin kichin ɗin da kaina na fara gyara itace zan fura wutar Nusaiba tazo ta ansa tana faɗar kai Anty su waye suka taɓa barin mai jego na aiki, ai mai jego sarauniya ce ko ya ki ka ce, Anty ƙarama? “.

Dariya Amrah tayi tace, “wato dai ba zaki sauya mani suna ba ko? “

Haka dai suke ta bidirin su abun su, suna gama dafa taliyar suka ɗora mani ruwan wanka, suka zuba wa Umma nata mu kuwa suka zobo muna guri ɗaya abincin muka ci sai da muka ƙoshi Amrah da Nusaiba suka fita suka nemo ganyen bedi suka kawo mani suka kwashe mani ruwan wanka naje nayo kamar yanda su Inno suka fara yi mani, cikin zuciya ta nace Allah sarki ashe dai su Inno gata ne suke yi mani da suke yi mani wankan nan yan zun gashi nice nake yi da kaina.

Koda na fito Amrah ce na sama tana yiwa yaron wanka Nusaiba na ce mata, kiyi masa a hankali mana kada kije kisa sabulu ya shigar masa, ni wallahi inda nice nafi ki iyawa dan nataɓa yiwa Anty Basira wankan saifullah so da yawa”.

ai kuwa nikam dariya na zauna ina yi masu bayan sun gama yi masa wankan aka zo gashin chibi, Umma najin ihun yaron da sauri tasa hannu ta anshe sa ta fara faɗa, “kashe ɗan mutane zakuyi ne waye yace maku da zafi sosai akeyi, dallah ku tashi ku bani guri nayi masa ni bana son hauka! “.

Ba niba hatta Amrah da Nusaiba sakin baki sukayi suna kallon Umma ni kuwa harda murza ido na keyi, fita iskan mu Umma tayi, kamar ba san mun tsare ta da ido ba, gashin tayi masa har sai da yayi bacci Amrah tace, “Anty kayan da zamu sakawa yaron nan fa? Dan naga kamar kala biyu gare shi “yan gobe suna”.

Shiru nayi ban ce da ita komai ba, Umma ce ta tashi ta buɗe akwatin ta, ta ɗauko kayan jarirai har kala biyar kuma masu kyau da zanen goyo na saƙa da kayan sanyi saiti.

Cikin farin ciki Amrah ta kwaso kayan tana tsalle, ita kuwa Nusaiba sai rawar jiki takeyi zata saka mashi kayan da sauri Amrah tace, “nifa zan shirya masa bara na ɗauko masa pampas din sa wanda na ajiye masa”.

Itama cikin kayan ta ta ɗauko pampas da wando na jarirai masu yawa da swafa da fula harda takalmi, itama Nusaiba tace ni dai bari ku gani, cikin kayan ta taje ta kwashe su, ta fara ɗauko mayukan shafawa da powder dasu turare ta kawo ta ajiye a gurin Amrah tace, “nima ga nawa kayan Baby boy a gyara muna abun mu mukam muna son shi”.

Ni kam cike nake da mamaki ba kamar Umma da zan iya cewa wannan shine karo na farkon da ta taɓa yin abun da faran ta mani rai sabo duk wani abun da yake da dan gata da farin ciki na Umma bata taɓa yin saba, ni ada nama ɗauka Inno ce ta haifeni sai da Inno tayi da gaske san nan na yarda da cewar Umma ce ta haife ni dan ko ɗin kin sallah bata yi mani amman Amrah da Nusaiba da Mariya ‘yar ɗakin Inno dan kala biyar_biyar sai tayi masu harda takalmi kala ukku, ni kuwa Inno tayi mani ɗaya sai kuma idan Allah yasa mutanen arziki sun yi mani dan haka duk kowa ya fini yawan kayan ado, wata rana kuma idan antashi yin ankon biki idan ta kai ayiwa su Amrah ɗinkin biki, nike zuwa na anshe turmin zane ɗaya, idan taji sai ta kaiwa Inno ƙarata Inno kuwa tace, tayi mani magana da kanta mana, to anan ne nake samu nasara akan ta.

Umma ce ta gyara masa tayi masa shiri mai kyau wanda abun ya yi ta bani mamaki, Umma kuwa basu yaron ta yi suka ɗauka suka fita, nima ina gama gyara wa, na fita cikin “yan uwa na ina kallon su na ce “Amrah Nusaiba ” kun kam mala jarabawar ne ko kuwa?.

Amrah tace, Anty nifa na ajiye ‘kara tun bokon nan kamar yanda kika ajiye jss 2 kallon ta nayi cikin jin haushin maganar ta nace amman kuwa bakiyi mani adalci ba, ai ni kinga tawa ƙaddarar ke nan, dan haka dan Allah kuyi karatun nan kada ku manta burina bai wuce nayi karatu mai zurfin gaske ba boko da Arabi amman ku dubi yanda na kasan ce, to dan Allah kuyi hakuri kuyi karatun nan kunji!?.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button