
dan Salma ta daɗe da komawa Nigeria, sai tambaya ta sukeyi miye zan ci, ko miye nake so, kuma sun ce, kada ya yarda ya cika matsa mani da takura mani, duk abunda nake so, yayi mani ko a kira su a sanar dasu Shuraim kuma ya ce, ba zai koma ba, a nan zai zauna ai kuwa korar sa, Salman ya yi, wai kada ya takura mani ya riƙa saka ni yawan magana, nikam dariya suke bani, kuma da yaga Shuraim yayi fushi sai ya fasa barin a tafi dashi, dole aka bar sa, daman sun san ba zai bari a tafi dashi ba, dan mun sha zuwa ɗauko ana hana mu.
Haka dai akaci gaba da tarairayya, ta, har Allah yasa cikin ya kai watan haihuwar sa, har kwakin haihuwar da aka bamu ya wuce, zama daket tashi da ket, Shuraim wata rana har kuka yakeyi, idan yaga ina son tashi tsaye na kasa, Salman kuma jin yakeyi kamar cikin ya dawo a jikin sa, wata rana shi da kansa yake ɗauka ta ya tayar dani tsaye mu fara tafiya saboda motsa jiki.
Yau kam tun da na tashi nake jin ba dai dai ba, ciwo_ciwo sama_sama, tun ina jin kamar da wasa har na kasa hakuri, nace, “Shuraim kira wo mani Daddyn ka, wash…! “
Ai da gudu suka iso baiyi wata_wata ba, yazo ya ɗauke ni, Shuraim ya buɗe muna motar muka shiga, sai asibiti ai da sauri muka ƙarasa, yana yin parking, ya fito ya ɗauko ni, abu da ƙasar waje kawai sai ga ma’aikatan asibitin sun zo da gadon ɗaukar masu ciki, suka bar su a nan baya aka shiga dani, aka hana su shiga sai go and come sukeyi tare da addu’a Shuraim kuka kawai yakeyi.
Cikin ikon Allah ko a awa ba’ayi ba Allah ya sauke ni lafiya, aka sami yan biyu namiji da mace ai kuwa zo kuga irin yanda su Salman suke tsalle da hamdala, ɗakin da aka kaini futu suka shiga, idon su, a kaina, sai da suka tabbar da lafiya ta lau sannan suka ɗauki yaran sai dariya sukeyi, sai alokacin ya kira Mom yake sanar da ita, ya kira Dad da Muhseen da Salma sai ya kira Yaya Auwal dasu Jafar, kai Salman kusan sai nace, zaucewa yaso yi sai da na anshe wayar dan photo yake ɗaukar yaran iri daban_daban yana posting ɗin sa.
Mom na zuwa ita dasu Dad kowa guri na ya fara zuwa sai da sukaji lafiya ta, sannan suka ɗauki yaran wanda Muhseen da Shuraim suka kan kane gurin sun hana kowa ɗauka, Mom ce ta anshe yaran ta kore su, awar mu shidda aka bamu sallama bayan a duba lafiya ta da lafiyar yaran, muka dawo gida ai kuwa sai shirye_shiryen zuwa gida Nigeria akeyi wanda Mai martaba ya bada umarni, sake shirya wa mukayi, dan Muhseen ya tafi da Shuraim airport mune kawai ake jira, haka muka fito cikin farin ciki muka nufi airport ɗin, bamu wani jima ba jirgin mu ya ɗaga sai Nigeria.
Da misalin ƙarfe biyu na dare muka iso, ai kuwa motocin Mai martaba ne suka ɗauke mu sai fada, muna isa bakin kofar faɗar kamar rana haka muka sami gurin cike da mutane, fulani ce da kanta ta janyo hannu na, muka shiga cikin gidan wani ɗakin ta nufa dani, muna shiga tace, “ki kwanta kiyi bacci ki futa har zuwa da safe kinji jika ta? “.
Murmushi na sakar mata tare da gyaɗa mata kai na, ta juya ta fita ni kuma baccin gajiya ne ya ɗauke ni akan wannan gadon na alfarma, ban falka ba, sai gurin ƙarfe takwas na safiya, ina falkawa sai a idon fulani ai kuwa da kanta ta kaini bayi, tayo mani wankan da ba zan taɓa manta irin saba, a rayuwa ta, muna fitowa ta shirya ni da kanta, aka kawo yaran duk an gyara su, sai uban ƙamshi suke zuba wa, harda Shuraim a biye dasu, shayar dasu nayi, aka fara jero mani abun kari nama rasa wane zan ci wane zan bari, Mom ce ta shigo cikin ɗakin da kanta ta soma ciyar dani har sai da na ƙoshi.
Anan ne Fulani da Mom suke sanar dani cewar, Mai martaba ya ce, zamu zauna ne a fara yin walima sannan mu tafi gurin su Umma na, dan za’a haɗa ne da bikin naɗin sabon sarki.
Na ce, “babu damuwa duk yan da kuka tsara mu masu biyayya ne”.
Ai kuwa sun ji ɗaɗin wannan maganar tawa, har sai da suka nuna farin cikin su.
Tun daga wannan ranar fulani da Mom sune suke kulawa dani har zuwa yau da mukayi kwana shidda kuma yau ne walimar, walima ce, wadda ta tara manyan malamai sarakai masu mulki da masu muƙamai talakawa da masu kuɗi, samari da yam mata, yara da manya, tsoho da tsohuwa, su Salma da su Humaira dasu Amrah tun daga lokacin da suka zo jiya basu futa ba, sai kai komo suke yi, anyi walimar lafiya an watse lafiya.
Sai shirye_shiryen zuwa gida kawai mukeyi, muna gamawa, aka ɗauke mu cikin motoci na alfarma muka nufi garin Yola domin ƙarasa wannan gagarumin bikin, cike da ɗoki nake son na buɗe ido na, naga irin farin cikin da Umma na zata nuna mani da na cika mata burin ta, su Hindu da Salma sai tsokana ta, sukeyi, ina share su.
Saboda tafiyar Asubanci ce mukayi kuma bamu tsaya ko ina ba, zuwa ƙarfe goma muka iso, ƙofar gidan mu, muna sauka da sauri nabar yaran hannun su Amrah nayi cikin gidan da gudu ina kiran Umma..! Inno…! Yaya….! Gani nazo na ganku”.
Dariya suka sakar mani cike da farin ciki, Mama ta rungume ni, ta ce, tunda ni badani ba, a cikin mutanen da kike kira ni na fara tarbon ki.
Da sauri na rufe ido alamar naji kunya nace, “Afuwan Mama duk cikin mararin ganin kune”.
Inno ce, tace, “munyi farin ciki da ganin ki, amman ki daina gudu ba kyau”.
Dariya nayi na faɗa jikin Inno, haka su Amrah suka same mu, Yaya ma rungume ni tayi, yan gidan kuwa, gurin ɗaukar yaran suka nufa idan wannan ya ɗauka sai wannan ya ɗauka, nikam hayewa sama nayi, na nufi cikin ɗakin Umma, ai kuwa tare da mutane na sameta, suna jin sallama ta, duk suka taryeni tare da yi mani barka, duk suka fita, aka barni nida Umma sai Mama Luba, jikin Umma na faɗa ina dariya ta fara shafa mani kaina, tana murmushi, Baban da ya shigo cikin ɗakin ya ce, “wa nake gani kamar Narjeesah na? “.
Ai da sauri nayi kansa na faɗa jikin sa ina dariya sosai mukayi farin ciki a cikin ɗakin Mama Luba ce, ta ce, “Narjeesah Ashe ansami ƙaruwa Allah ya raya, am sai kuma gashi kin sameni a cikin gidan ku, dan Allah ki yafe ni laifin da nayi maku na cin mutumci ta korar wula’kanci sai gashi kuna barin garin komai nawa ya lalace hayar ma dana ke biya na kasa biya, ke daga ƙarshe ma na rasa komai nawa sai bara nadawo ina yi a rin wannan rayuwar ne, Allah ya kawo mani Umman ku, ita ce ta zo dani har ta bani kuɗin ɗaukar wani gidan hayar, tare da kuɗin siyen kayan ɗaki da sutura, haƙiƙa gaskiyar magana na yarda hassada ga mai rabo taki ce, ku yafe ni “.
Murmushi nayi, na ce, “nikam na yafe maki bana iya riƙe kowa a zuciya ta, Allah ya yafemuna baki ɗaya “.
Kowa ya ce, “Amin”.
Cikin falon muka dawo Baban mu kuma ya fita, muka soma fira da su Amrah har nake tambayar ta sauye_sauyen da nagani, ta ce, “duk aikin Yaya Salman ne, dan dashi da Shuraim duk ƙarshen wata, suna zuwa su kwana biyu, shine ya baiwa Umma dasu Inno jarin miliyan biyu_biyu, su Yayan mu kuwa, aiki ya nema masu, mukam dubu ɗari biyar_biyar ya baiwa mata mu dogora da kan mu, yara dubu hamsin_hamsin,
Sai kuma provision ɗin da buɗawa Baban mu, sannan ya baiwa duk su Yaya mota, harda Baban mu ai kin ga gidan cike da motoci, sannan wan can gidan na gumel ya gyara masu shi, harda su get, su Yaya suna ajiye motocin da ya basu ke harda moƙota duk sun sheda, dasu kawu, wai duk kina nufin cewar baki da labari? “