NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Kallon ta nayi cike da mamaki nace, “ke ni wallahi duk ƙarshen wata suna yin tafiyar kwana ukku ko huɗu amman ban taɓa sanin nan suke zuwa ba, saboda ya ce, dani wani aikin ne suke zuwa yi, wata ƙasar “.

Amrah tace, “shi yasa nake ƙara godewa Allah da ya sanya kika zamo alkhari haka Shuraim zuwan sa, a rayuwar mu alkhari ne, wannan maganar haka kowa yake faɗar ta, harda wanda suka jahilci abun a can baya “.

Haka dai mukayi ta fira, su Mommyn Humaira duk suna gidan harda moƙota, gidan ya cika sosai biki akeyi sosai ƙaton sa aka yanka da rago huɗu, wai harda na bikin Shuraim za’a haɗa, mukam dariya mukeyi, matan su yayan mu duk suna nan harda Mrs Yaseer a cikin yan bikin, kayan barka kuwa kamar wani company, kai komai cikin nasara akayi sa, yara sun ci sunan Mai martaba muna kiran su, da Sultan da Sultana, kwana biyu mukayi ana bikin saboda naɗin sarautar Daddy wanda Salman yayi masa wayo ya amsa.

Taro ya watse lafiya inda muna zaune dasu Humaira wata ce, ta shigo tace, tana son ganin mu shine, su Mariya suka kawo ta gurin mu, kallon ta, mukeyi a take duk muka tashi tsaye nida Hindu da Humaira, Hindu ta nuna ta, ta ce, Haleema ke ce, daman kina nan!? “

Ta ce, “ina nan ku zauna daman nasan zan sameku a tare”.

Zama mukayi muna kallon ta, duk tayi baƙi ta fita hayyacin ta, Haleema yar gayu ta dawo wata bakar tsohowa dan daga gani tasha baƙar wahala a rayuwar ta.

Ta ce, “nabi ruɗin zuciya ta, na Auri wanda zuciya ta, take mararin sa na bar tsohon zaɓina, zaɓin iyaye na, nayi Aure batare da yardar suba, bada sanin suba, ga yaudar Jafar da nayi, duk haƙƙin sune ya hanani sukuni, munyi zaman soyayya nida zaɓi na, sai gashi watan mu biyu, mun fara samun matsala inda yake bani maganin hana ɗaukar ciki tun ina sha cikin farin ciki har na ƙosa dashi na daina sha, kwatsom ciki ya shige ni, nayi ciwo mukaje asibiti kwajin farki aka tabbar muna da ina ɗauke da cikin wata, biyu, tun daga cikin asibiti ya ɗaure fuska yace, a zubar dashi a take nasha jinin jikina, na fara cewa ba za’a zubar dashi ba,

Tun a asibitin ya soma duka na, har muka dawo gida da belt yake duka na, yana taka cikin ai kuwa yayi sa’ar zubar dashi tun daga wannan lokacin ya dawo kulawa dani, saboda son da nakeyi masa, bana jin haushin sa, kwatsam na sake samun wani cikin, shima ya ce, a zubar a wannan lokacin kam na hana, har dukan da yayi mani cikin bai zube ba, sai ya riƙa zuba mani magani a cikin abinci da abun sha ba tare da sani na ba,

Aikuwa gurin zubewar cikin na kusa rasa raina, asibiti sun so ƙin yi mani aiki, da ket suka anshe ni, tun daga wannan lokacin muka dawo kamar wasu maƙiya a take ya tsiro mani da asalin halin sa, na rashin kulawa da kawo yan matan sa, a cikin gidan, idan nayi magana sai duka, kai da abun ya dameni, sai na fara tunanin, cewar ko dan anyi wannan Auren ne bada albarkar iyaye ba ne, shin ya kawo wannan rashin jituwar, ke wata rana ina ina aikin tunanin makomar rayuwa ta shine ya shigo tare da worgo mani takardar saki, inda na shiga kaduwa, tare da tarin nadamar wannan Auren da nayi, yan zun haka yau zan koma a gaban iyayena,

Bayan na zauna a gidan wata ƙawata, na cika iddah, shine yan zun nace, bari na zo na sameku tunda na sami labarin anyi bikin haihuwar da Nargeesah tayi, shekaran jiya, shine nasan zan sameku a tare, dan Allah Humaira kiyi hakuri ki dawo mani da Jafar nasan da sanin cewar kin Aure sane saboda ni na guje sa badan kuna shiri da juna ba, wallahi nayi maki alkawarin zan kula dashi, kuma zan anshi yaron da kika haifa zan riƙesa tamkar yaron da zan haifa da ciki na!”.

Ta fashe da kuka nukam kallon ta kawai mukeyi, zuwa can na ce, “to nidai ban san miye zan ce dake ba, amman ina iya faɗar Allah ya kyauta kuma Allah yasa yanda muka hana iyayen mu kuka muma, ya’yan mu kada su saka mu kuka, dan son zuciya ɓatan ta”.

Hindu ta ce, “a nufin ki muji tsoron gujewa aikata son zuciyar mu, ko kuma kin kawo muna kukan ki ne? Dan na kasa fahimtar komai “.

Humaira ta ce, “Haleema ke nan to yan zun kam na fahimce ki, wato tunda ga Humairar mahaukata, ai dole ne naci gaba da baki farin ciki na, kina saka ni kuka, kuma dolene yi maki duk abunda kike so, to bari kiji wani abun, Haleema ni da kike gani a yan zun na wuce da sanin ki, wato nasa daukar da ɗana Haniff na baki, uwa uba soyayyar mijina, duk dan ke kiyi farin ciki, to lallai ne sai yan zun na tabbar da kina hauka ne Haleema, ina son Jafar ko nace dake abu Haniff, bana jin zan iya barin wata mace ma ta raɓesa da sunan soyayya ballema ace Aure, ni Ummu Haniff nayi maki nisan da ba zaki iya hango koda wutsiya ta bane, Yaya Jafar nawa ne dan ni akayo sa, ai kin riga da kin koya mani son Jafar dan haka, ba zan ce, ba zanyi zumunci dake ba, amman kada ki yarda zuciyar ki ta ƙara raya maki cewar ni Humaira zan sake sadaukar maki da farin ciki na, eh lallai ne na Auri Yaya Jafar bana son shi shima baya sona, amman kuma abun al’ajab anan kuwa shine a yanzun nida Yaya Jafar mun afka a tafkin soyayya mai zurfin gaske, wanda ko masoyan da sukayi Auren soyayya ba zasu kaimu shauƙin junan mu ba, dan haka ki iya halshen ki Haleema “

Haleema sakin baki tayi tana kallon mu, su Yaya Jafar da suka shigo tun ɗazun ne ya ce, “Haleema kike koma waye, oho!? ban damu ba, Humaira ita ce rayuwa ta ai sai yan zun ma da kika dawo na sake gane hakan, Ummu Haniff ita ɗaya ce, a zuciya ta, dan haka ki ja jikin ki, Humaira taso muje gida dan yau ina jin idan na tsaya a gidan nan za’ayi abun kunya”.

Haniff dake rarrafe ne ya rarrafa yayi gurin Yaya Jafar ya ɗaga shi sama yana yi masa wasa, tashi Humaira tayi suka tafi bayan tayi sallama da kowa haka Hindu tare suka fita itada yaya Aliyu, haka Haleema taja ƙafar ta, tana kuka tabar gidan.

Bayan kwana biyu Inno ke tambaya ta, wai kuwa Salman yana gari kuwa? Dariya nayi nace, “baya nan ai Dad ne ya saka shi ya kammala masa wani aikin a london to da fushi ya tafi shi yasa, suka daina jin sa, ni ce, ma nake kiran sa, ina saka shi ƙara jin haushin tafiyar”.

Dariya aka saka Inno ta ce, “ai kuwa zan rama masa, bari dai zaki gani”

Ban damu ba dariya ma Kawai nake yi, haka har mukayi kwana arba’in da biyu, gyara kam nasha shi, kitso da lalle akayi mani na yawon arba’in, sai gashi Inno da Yaya suka ce, zan je na yiwa Mai martaba barka da wannan matsayin da Allah ya bashi, suka haɗa mani kayan da zamu dasu, suka rakani har mota, ina shiga da Shuraim ya zauna aka ɗora masa Sultana a ƙafar sa, ni kuma Sultan ne a jiki na, muka ɗauki hanya, sai airport inda Yayan mu, ya kaini, muka shiga jirgin, muka ɗaga, sai garin Abuja.

Muna sauka sai alokacin ne na tuno ashefa Abuja muka zo to miye yasaka Yaya Auwal yayi muna bucking na jirgin Abuja? Run gume ni akayi ta bayana, ai da sauri nake ƙoƙarin kubcewa, ina jiyowa sai akan Salman ido na ya sauka ya rungume Hannuwan sa, yana kashe mani ido ɗaya yana ɗaga gira ɗaya, ya ce, “ya dai madam, kin yi mamaki ne? Ai daman nace zan rama gashi dai su Inno sun tayani ramuwa”

Haushi naji na ce, “haba dear ban fayi yawon arba’in ba fa, ni wallahi ba a kyauta mani ba”.

Dariyar shakinyan ci yakeyi ya anshi Sultan yaja hannun na, Shuraim a cikin motar muka same sa nima ya saka ni, ya shiga aka rufe motar muka ɗauki hanyar gidan sa, sai fushi na keyi shida Shuraim sai dariya sukeyi wai ashe haka na iya smile, bai sani ba, Shuraim duba ka gani, yau tafi kullum kyau ko? “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button