NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Shiru duk sukayi cikin tausayin halin da na tsinci kaina, sukayi mani alkawarin yin karatu.

Haka dai mukaci gaba da rayuwar mu, a can makaranta su Amrah suka jiyo maganar Auren da za’ayi nasu Yaya Auwal dasu Surajo dasu Shamsiyya da Zuwaira dasu Balkisu wanda duk suna gaba na wasu shekaru biyar suka bani wasu shekaru ukku, bikin wanda aka ce a sanar dani kada na yarda naje gidan naɓata masu biki, ‘yan gidan mu suka faɗawa mutanen gari kuma da Mariya da kanta tazo har gidan mu ita da wasu ƙannen mu, suka sanar damu wannan maganar.

Ita dai Umma ta yarda taje gidan ita dasu Amrah inda suka dawo gidan kamar wanda aka koro.

Hawaye na gani a idon su Amrah cikin tashin hankali na buɗe baki zan tambaye su, kawai naga Umma itama kukan takeyi, da sauri naje ina tambayar Umma hawaye na zubar mani amman Umma bata ce dani komai ba, tabbas nasan babban abune ko miye, daket Umma ta buɗe baki tace……..

Comment And share

Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????????????

???????? NARJEESAH ????????

*RUBUTAWA * ????
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN CE

YA ALLAH KAJIKAN IYAYE NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU DAGA CIKIN DAUSAYIN ALJANNA SU DA DUK KANNIN MUSULMI BAKI ƊAYA AMIN YA ALLAH

BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM

              *5&6*

➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Umma ta ce, “kada ku yarda naji wata magana ta fito daga cikin bakin ku har sai idan naso hakan, wannan umarni na ne! ” kawai ta shige cikin ɗakin ta, ta saki labule.

Tunda mukaji umarnin Umma sai duk jikin mu yayi sanyi babu wanda ya sake cewa komai tashi nayi nima kashige cikin ɗakin mu na kwata, ina nazari, tabbas duk abunda ya saka Umma kuka baƙara min abu bane, amman kuma Umma ta hana nasan ko miye wannan abun, kai koma miye babu shakka duk abunda ya faru nice sanadiyar komai ya Allah kadube mu.

Duk yinin ranar bamu da wata walwala kowa a cikin damuwa yake har aka kwana biyu, yau muna zaune muna fira ni dasu Amrah Nusaiba na goye da yaron yana bacci, sallamar su Inno ce ta katse mu, cikin farin ciki muka tarbe su Inno da Yaya da Mariya, Umma ce ta fito cikin ɗakin ta, tazo ta, tarye su da farin ciki, tabarma aka shimfiɗa masu suka zauna na kawo masu ruwa Amrah taje maƙota ta siyo masu zuɓo ta kawo masu, bayan sun sha aka gai da tambayar ya akaji da hidimar biki suka ce Alhamdulillah angama lafiya taro ya tashi sai dai abunda ya faru ne wanda basu ji daɗin saba.

Umma tace, “ai komai ya wuce”.

Da sauri nace, Inno dan Allah miye ya faru a ranar dan Umma ta hana kowa ya sanar dani, sun barni cikin duhu da tunanin miye yake faruwa, bana bacci ina cikin damuwa, duk da nasan da cewar ba kowa bane ya janyo wannan matsalar ba sai ni.

Inno ta ce, “ai koni ma ba zan iya sanar dake komai ba, da kuma wanda sukayi abun kasan cewar nafi kowa sanin halin ki Narjeesah idan kika san ko su waye da abunda akayi ba zaki ɗauka ba, kasan cewar ki mafaɗa ciya, daman cikin da kike dashi ne yasaka ki yin sanyi amman yanzun nasan zaki iya fafatawa da kowa”.

Yaya ta ce, “tabbas hakane Narjeesah zaki san wani abun amman banda wani abun, ranar a unguwar mu anyi faɗa sosai har makarantar islamiyar ku inda akace malan Abbakar shine ya yi maki ciki kasan cewar sa yana sonki tun kina ƙaramar ki, kuma Baban ku ya sani amman yace, sai in kinyi hankali kin ce kina son sa, to ganin irin yanda idan baki zo makaranta ba yake zuwa ya sakaki a gaba kije makarantar shine aka ce shine ya yi maki cikin yaron nan, shi kuma ya ƙaryara rigima har aka koresa a makarantar duk da kuwa kasan cewar mahaifin sa shike da makarantar”.

Hawaye naji suna zubo mani nace wallahi Inno bashi ne yayi wannan cikin ba kuma wallahi ko kalmar kebewa a wani gurin, ko a makarantar bai taɓa furta mani ba.

Inno tace, “ana cikin wannan rigimar ne, wani mai mota yazo daga ganin sa anga dan shaye_shaye to shine ya ɗauki hankalin kowa inda ya ce, shine wanda ya yi maki cikin yaron nan kuma yazo ya anshi abun sa ne, saboda duk lokacin da ku ka tafi makarantar boko shike zuwa yana ɗaukar ki yana zuwa gidan sa dake har sai da kika ɗauki cikin sa, kuna tare shine ma yace ki zauna ki raini cikin zai Aure ki, to yan zun ya fasa Auren ki yaron kawai yake so ko kiba shi yaron da arziƙi ko kuma yazo da “yan sara suka sai dai su kashe ki da duk wanda yake tare dake su ɗauki yaron! “.

Da sauri na tashi tsaye na fara ja da baya ina zubar da hawaye nace wallahi Inno da Yaya, wannan ba shine uban yaron nan ba, wallahi ba zan bada shi ba! .

Inno da Yaya suma suka tashi tsaye suka haɗa baki gurin fad’ar, “to waye uban yaron nan tunda kin ce wannan bashi bane!? Kuma kina nufin kin san inda uban yaron yake ke nan! “.

Nace wallahi wannan ƙarya yake yi maku bani da wata alaƙa dashi, mutum nan ɓarawon yara ne kada ku yarda dashi.

To wane ne uban yaron nan tunda kin san shi kuma a ina yake kuma ya ya sunan sa? “Inno ce” ta jero mani wannan tambayoyin da suka riki tar dani a take na dabur buce na rasa ma wace irin amsa ce zani bata, gashi duk ankafe ni da ido.

Sai da na haɗiye yawu masu ɗaci ga uwar zufar da take , zubo mani ta kowane saƙo na jiki na nace, a gaskiya duk bani da amsar da zan baku daga cikin wannan tambayoyin amman gaskiyar zance “wannan mutanen ban taɓa sanin sa ba! “

Inno tace, to ya zama wajibi tsakanin yau ko gobe ki sanar damu Baban yaron nan, ko kuma kubar garin nan, sati ɗaya mutumen ya bada zai dawo kuma dawowar sa ba abu bane mai sauƙi dan da alama zai iya aikata duk abunda ya faɗa saboda a tare yazo da maso shaye_shaye harda takubban su”

Daɓas na zauna a ƙasa na fashe da kuka kamar raina zai fita, suma su Amrah kukan ne sukeyi sosai, Umma dai bata ce uffan ba, har su Inno suka dawo a kusa dani suna lallashin mu, kallon Inno nayi nace, “Inno dan Allah ku anshi adireshin sa da number sa ku ajiye mani ita har na tsayin wani lokacin”.

Insha Allah suka faɗa, Inno ce ta kawar da wannan kukan ta ce, yo ni wannan iyayen na daban kuke kuna nufin ba zaku bani maigidan ba na ɗauke sa, ba har sai na roƙa ko? “.

Dariya mukayi, nidai shiru nayi Nusaiba ta sauke shi ta bata shi tace, “gashi nan Inno bama rowar ɗan baiwa”.

Dariya sukayi Yaya tace, “ni kuwa wane suna ne kuka sakawa angon namu dan naji har yanzun baku faɗa ba, kodai sunan bai da daɗi ne ace yaro wata biyar bamu san sunan shi ba? “

Dariya mukayi, “Nusaiba tace suna kam mai daɗin gaske sunan hafizai”.

Inno tace, “um kaji iyayen “ya”ya da kauɗin tsiya, wane suna ne wannan? “.

Amrah tace, “Shuraim ke nan Inno yaro hafizi ga daɗin murya”.

suka haɗa baki gurin fad’ar, “kai masha Allah, Allah ya raya muna Shuraim yaro mai suffar larabawa da sunan larabawa abu ya yi kyau”.

Mariya ce ta anshe sa, tana kallon sa, tace, “kai Inno wallahi wannan bai kama da wannan ƙaton mutumen mai ƙaton hanci kuma gashi baƙin sa ya yi yawa kawai dai ɓarawon yara ne, a gaskiya a gudu da yaron nan daga garin nan ma baki ɗaya, saboda naji ana raɗe_raɗin cewar cikin dare za’a nuna masu gidan nan ni wallahi yaron nan tausayin sa, nakeji! “

Kallon_kallo muka shiga yi nida su Amrah cikin damuwa Amrah tace, “Insha Allah babu maiyi sai Allah, burin wasu ba zai cika ba”

Sai marece su Inno suka tafi, Umma ce taja Nusaiba suka fita, Amrah ta sameni a cikin ɗaki kwance ina tunani ta dafani, na ɗaga ido na kalleta na tashi zaune tace, “Anty nifa a tsorace nake da maganar da naji su Mariya na faɗa nifa ina ganin zan baiwa Umma shawara, ne yau mu nemi gidan da zamu je mu ɓuya a can”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button