NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Kallon ta nayi, nace “Amrah “duk nice na janyo maku shiga cikin wannan hatsarin nifa ina ganin zan ɗauke yaron nan nabar garin nan gudun kada azo kashe ni a haɗa daku duka na bani, nayi sanadiyar mutuwar mahaifiyar mu daku kan ku, kuma aje a maida yaron nan wani irin mugun mutum”.

Rufe mani baki Amrah tayi ta ce, “Anty dan Allah hankalin ki ya dawo jikin ki, ai duk inda kika saka ƙafar ki muna sai mun saka dan haka zamu gudu tare mu tsira tare”.

Koda Umma ta dawo, ita da Amrah har mun gama abincin dare mu gyara ko ina, sannu da zuwa mukayi masu.

Da dare bayan munci abinci muka rufe gidan tare dayin Addu’oi sosai muka ɗauro alwalar kwanciya muka rufe ɗakin mu nida Amrah, Umma da Nusaiba suka kwanta ɗakin Inno suka rufe, addu’a sosai mukayi, kafin mu kwanta na shafe Shuraim da addu’a wanda shi tuni yayi bacci.

Can cikin dare muka fara jiyo, motsin ana shirin cire muna ƙofa ta shigowa cikin gidan, ai kuwa duk muka tashi zaune a tsorace addu’a muka somayi, ai kuwa dukan ƙofar akeyi da ƙarfin gaske kuma da makamai ake dukan ƙofar da sau muka diro ƙasa, nasa hannu, na ɗauke Shuraim na goye shi nasa wani zane na taresa dashi, sai muka lallaba, a hankali muka buɗe ƙofar ɗakin mu muka fito anan ita Umma suka fito sai jikin mu ke rawa, addu’a duk wadda tazo bakin mu ita muke yi.

Gashi har ƙofar ta fara alamar da kuwa, ta maƙotan mune aka saƙo tsani, da sauri muka ja da baya dan mun riga da mun san tamu tazo ƙarshe, hannun Amrah naja da niyar mu koma cikin ɗaki mu rufe amman kuma idan mun gudu su Umma fa, duk mun ruɗe dawowa gurin Umma mukayi nace, Umma dan Allah ki yarda mu koma cikin ɗaki ɗaya, mu ruf… Ban kai ga ƙarasa wabane, wasu maza guda biyu ne suka diro ta inda aka saƙo tsanin.

Zaro ido mukayi waje da sauri suka nufo mu mukam mun sadaƙar, har gaban mu suka tsaya cikin rawar jiki suna yi suna kallon ƙofar mutumen ya ce, “kuzo dan Allah mu taimakeku, kafin su shigo ciki dan sunada hatsarin gaske, akwai wanda zasu tarye ku a waje! “

Da gudu muka nufi gurin dan Amrah ta gane mutumen, naji tace, ” to Baban Ahmad”

Abu ga tso wai mune da hawan tsani wanda ko amafalki ban taɓa tsammani haka ba, Umma aka fara ɗorawa kamar walkiya ta haye saman katangar gidan wasu suka taryeta sai, su Amrah suka turani, ni kuwa ina cewa ku fara fita, mutane suka ga zamu saka har a samemu kawai wannan ɗaya mutumen ya ɗagani sama ya taka matattakar tsani nin ya fitar dani, aka anshe ni sai Nusaiba sai Amrah sai mutanen suka ɗauke tsanin suka diro mukuwa tsuru_tsuru a cikin gidan kawai suka bud’e muna wata ƙofar muka faɗa wani gidan inda matan gidan suka maza suka tura mu wani ɗakin suka rufe, Shuraim ne na sauke da sauri gashi ta ko ina jikina rawa yakeyi.

Fitila aka kunna, Allah sarki bawan Allah idon sa biyu yana kallo na, zama nayi a gefen matar dake cikin ɗakin na bashi mama, ya fara sha, matar tace, “Allah ya ƙara tsare gaba “.

Mukace amin, anan muka zauna sai da asubahi aka buɗe kofar ɗakin muka fito, mukayi alwala mukayi sallah tare da godiyar Allah da ya tseratar damu dan wannan ikon Allah ne.

Sai garin Allah ya waye sannan muka fito gidan muta yi masu godiya wadda bamu san irin ta ba, a ƙofar gidan muka riski su Baban Ahmad mukayi masu godiya, suka ce babu komai ai yiwa kaine, wallahi wannan mutanen miyagune, suka bamu shawarar ya kamata mubar gidan.

Tun a ƙofar gidan ne zaka fahinci cewar da sun same mu a gidan nan da sunga bayan mu dan ƙofar sai an sauya wata.

Cikin gidan duk sun har gitse muna kaya amman basu ɗauki komai dan babu abun ɗauka a gidan.

Umma kam fita kawai itada Nusaiba kamar jiya, mu kuma muka gyara gidan da ɓarnar da akayi muna, muka ɗora abun karyawa koda muka gama Umma bata dawo ba zama mukayi muna ta jimamin abunda ya faru a daren jiya.

Umma ce ta shigo tare da wasu mata suka shiga cikin ɗakin ta suka fito, suka dawo cikin d’akin mu suka fita Umma ce ta dawo da kuɗi a hannun ta masu yawa, kallon ta mukeyi nida Amrah, sanin cewar idan nayi magana Umma ba zata bani amsa bane ya saka na ƙyafaci Amrah, da sauri Amrah tace, “Umma kuɗin miye haka? “.

Bata kuɗin Umma tayi Amrah amsa, Umma ta ce, “na sayar kayan ɗakin mune harda katifu kuma kwanonin sai a zuba su a buhuwa, yau nake son mubar garin nan saboda hankali na bai kwanta da wannan mutanen ba dan nasan zasu iya sake dawowa, yauma Allah ne ya kawo muna ɗauk, kuma kunji mutane sun bamu shawarar mubar gidan nan da wuri, gudun samun matsala, gashi ana ta sanar damu cewar yau kada mu kwana a gidan nan, shine ni kuma na ce abunda zamuyi kawai shine yau bar garin nan”.

Ajiyar zuciya muka sauke a take muka hau shiri, Amrah na goye da Shuraim har muka gama komai muka rufe gidan muka baiwa maƙota makullin saboda wanda zasu ɗauke kayan su idan suka kwashe idan ansamu wanda zasu zauna sai basu su ƙarasa wata bakwai wanda ba muyi ba.

Ƙarfe biyar na marece muka isa tasha, mudai Umma muke bi duk inda ta dosa, motar kaduna muka hau ta biya kuɗin sai da Umma tayo muna siyayya muka ɗauki hanya, kasan cewar duk bamu san gurin waye zamu je b, amman bana jin zafin wannan tafiyar, har su Amrah fuskar su a sake take, Shuraim ya hannu na, yana bacci saboda su Amrah a matse suke, shi yasa na anshe sa.

A gaskiya tafiyar dare babu daɗi ko kaɗan, zafi ne ya dami Shuraim ya saka muna kuka na rasa ya zanyi masa, Amrah ta amsa Umma ta ansa Nusaiba ta ansa adawo mani dashi, ni kuma na rasa miye zanyi masa ma wanda zai daina wannan rigimar.

Wani bawan Allah ne da yake a jikin glass ɗin motar yace, “baiwar Allah kodai zafi ne ke damun sa,na buɗe maku glass ɗin kaɗan gudun kada mura ta kama shi? “.

Godiya nayi masa ai kuwa yana buɗe windon tuni ya koma baccin sa, ajiyar zuciya muka sauke, sai da naji iskan yayi yawa nace ya rufe muna mun gode.

Biredi da lemo muka sha da tsire,tafiya mukeyi tun daga jigawa dutse zuwa kaduna, jigawa dutse ma a Kauyen gumil dake cikin garin jigawa.

A tasha muka sauka muka da misalin ƙarfe shidda da rabi na safiya.

Wata unguwar mukaji ana faɗa unguwar kawo, a can muka sauka, Umma ta tsayar damu taje tayo tambaya aka yo mata kwatance, tayi godiya tazo tace, muje, cikin ikon Allah, bamu wani sha wahala ba, muka isa gidan da Umma ke nema, da sallama muka shiga gidan matar ta amsa ta fito, tana ganin Umma ta washe baki tana faɗar lale_lale maraba da zuwan ku haba, Aysha yau kam kin wanke tarin laifin ki a gurina, maraba ku ƙaraso daga ciki mana”.

Cikin falon ta muka sauka kayan mu muka baro su a tsakar gidan, Allah yasa da nefa duk sai muka baje a saman ledar tsakar ɗakin muna futuwa, a take taje ta kawo muna abinci da nasha, nida su Amrah ne mukaci muka ƙoshi, ba mayi wani baƙunta ba, Umma ma haka, dan ma ina zaune a gurin bata wani saki jikin ta ba Shuraim ne ya motsa ya fara kuka, Nusaiba ta sauke shi ta bani, matar ta kafe ni da ido musamman ma da taga na fara shayar da yaron riƙe baki tayi ta kafeni da ido.

Ganin hakan ne ya saka Umma tambayar ta buta zatayi alwala, da sauri matar ta, tashi ta kawai wa Umma ruwan wanka tace, ta fara yo wanka tukun na.

Murmushi Umma tayi taje gurin wankan matar ta ce, “Narjeesah wai ku kuwa har yanzun baku daina yin Aure da wuri haka ba? Kuma fa naga mahaifin ku baya da wannan ɗabi’ar kodan anga baya raye ne shine akayi maki Auren wuri? “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button