
Kallon_kallo muka shiga yi mu ukku, Amrah ce, “eh ke dai bari kin gafa da ƙurciyar ta anyi mata Auren wuri shine fa mijin yaje ya shawo iskan sa, yazo ciki wata biyar ya sake ta a gaban mu harda su Inno kuma saki ukku, shine ta reni cikin gidan mu, wai yan zun da yaga yaron ya fara wayau wai shi sam bai san lokacin da yayi sakin ba, ina mai baki labari zarya kullum da safe da rana da dare, shine wai kowa sai ta koma ko kuma tabashi ɗan sa”.
Wani uban ashariya matar ta saki, tace, halan ce masu akayi bata da gata ne, kodan sunga Aysha tana share tane, ai Aysha dama ita kunya ne da ita da kawaici ai kuwa tunda kuka baro masu garin nan ba zaku koma ba wallahi bari uwar taku tazo, to wai ma ke da nasani uwar masifa da surutu ya ya akayi kika dawo haka? “.
Dukan mu ta bamu dariya, sai da muka dara nace, “Mama ni wallahi sai yanzun ne na gane ki ashe wai gidan ki muka sauka”.
Dariya tayi tace, “ja’irar yarinya, idan mai gidan nawa ya ƙoshi bani shi”.
Shuraim ɗin na bata, Umma kuwa tun lokacin da Amrah take, sheƙa ƙarya ta fito riƙe baki tayi tana mamakin a ina Amrah ta iyo ƙarya haka, shigowa cikin ɗakin tayi, nima naje nayo wankan su Amrah ma duk sunyi wankan muka ranka sallolin da bamuyi ba, mamar ce tayiwa shuraim ɗin wanka, mukam bacci muka ranka har shuraim ɗin, Umma kam babin firar yaushe rabo suka dasa.
A gaskiya zaman gidan Mama Luba akwai farin ciki dan ɗaki biyu ta bamu Umma ɗaya mu ɗaya, satin mu biyu a gidan ta baiwa Umma shawarar mufara kasuwan ci, to wace sa’na arce zamu fara?.
Tace da Umma “ko abinci ne ki fara sai dawa inada shago a kusa da shagon da nake ɗinki, mai sai da abincin tayi Abuja ne dan haka ke zaki iya, dan Allah Aysha kada kice ba zaki iya ba, saboda yaran ki matane, da suje su siyar da abinci ko wani abun daban gwara ke kiyi hakuri kiyi wannan sana’ar”.
Shiru Umma tayi tana, tunani zuwa can tace, “babu komai na yarda zanyi nasan duk abunda kika sani wanda zai sa naci gaba shi kike bani shawara akai baki taɓa bani mummunar shawara ba, dan haka na yarda ɗari bisa ɗari”.
Mukam duk jikin mu yayi sanyi bare ma lokacin da muka gano wurin ranar da Umma ta fara yin abinci a gurin, gidan muka dawo muka saka kuka, kamar wanda akayi wa mutuwa, a ranar koda suka dawo gida sam basu gane kan mu ba.
Babu wanda yabi takan mu dan sun fahimci komai, Umma ce naji tana faɗar Alhamdulillah kasuwa tayi kyau , sai farin ciki sukeyi.
Da haka dai har muka saba itama Umma ta saba, cikin ikon Allah Umma da tayi abinci nan da nan ya ƙare, sai Mama Larai ta baiwa Umma shawarar itama ta kama gidan haya dan itama haya takeyi Umma bata kawo komai ba, takuwa yarda, a haka har Umma ta samar muna gidan haya, amman nesa da unguwar da Mama Luba take.
Umma kam, sai sam barka a da kuɗin abincin ta mukeci muke sha, kuma muke biyan haya hankali kwance.
Cikin ikon Allah har muka shekara biyu a garin shuraim na daɗe da yaye sa, shegen wayau ne dashi shekarun sa, biyu da wata shidda a yanzun amman idan ka ganshi zaka ɗauka ya shekara ukku a duniya sai uban surutu.
Umma ce mu kaga kwana biyu bata dafa abinci ba, shine muka kasa hakuri tunda munga lafiya lau take, amman da alama tanada damuwa gashi ni ban isa in san damuwar ta ba, zaune muke da Amrah da Nusaiba na ce, “Amrah miye yasaka ba zaki tun kari Umma ba kiji damuwar ta, tunda kin san nice babba amman bani da wannan ikon dan Allah kije ki tambayar muna ita “.
Tashi Amrah tayi ta sami Umma zaune ta doka uban tagumi shi kuwa shuraim yana zaune a ƙafar ta na wasa da motar da ta siya mashi, da remote a hannun sa.
Amrah tace, “Umma dan Allah mike damun kine? Kuma kwana biyu bakiyi abinci ba lafiya dai? “.
Ajiye zuciya Umma ta sauke tace, “Luba ta hana ni ɗan makulli tace, itama abincin ta dawo wa saboda ɗikin da takeyi babu kasuwa amman taga siyar da abinci akwai kasuwa harda riba, kuma tace kada mu sake zuwa inda take gashi na kashe kuɗi na, nayo cefane, yan zun ya ya zamuyi ne, gashi wannan lokacin ne zan nemi kuɗin hayar gidan nan! “
Zaro ido waje mukayi nida Nusaiba uwa uba Amrah da take zaune ta kafe Umma da ido.
Fitowa nayi inda muke ɓoye nida Nusaiba na ce, “Umma ni zan……
Comment and share
Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????
???????? NARJEESAH ????????
Rubutawa daga alkhalamin????
NANA KHADEEJATU UMMU IHSAN SADAUKAR GA DUK KANNIN MASOYANA NA
ELEGANT ONLINE WRITERS
*7&8*
➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Umma ni zan iya fitar maki dashi a bakin titi ko ƙofar gida, tunda kema kina iya bakin ƙoƙarin ki na ganin kin ciyar damu da halak, dan haka ki bani wannan damar dan Allah Umma”.
Shiru tayi duk muka zuba mata ido Amrah ta ce, “Umma ki yarda damu zamu iya wannan aikin dan Allah, mudai kawai ki bamu dama yan zun mu soma aiki kawai”.
Nusaiba ta ce, “Umma ya kamata ki fahimci cewar baki da masoya na gaskiya idan ba muba, baki da wani ɗan uwan da zai so ganin ci gaban ki sai mu, kuma baki da wani abokin shawara wanda ya kai mu, mune kawai yafi chan chanta ki baiwa yarda da amana ɗari bisa ɗari”.
Umma kuwa ta ce, “kuje ku ɗaura girkin ni zan iya fitar da abuna kawai ni dai fatana ku koma makaranta dan ku sami ilimi domin ilimi shine farkon abunda ya kamata na koyar daku nema ba kuɗi ba”.
Sanin halin Umma magana ɗaya takeyi ne yasaka muka fita muka fara haramar ɗaura girkin kowa da abunda ya keyi, nike wanke kayan miya, Amrah ta ɗaura dafuwar shinkafa, Nusaiba ke dafuwar wake da taliya, ina gama wanke kayan miyan Nusaiba taja hannun Shuraim suka nufi gurin markaɗen kayan miyan ni kuma naci gaba da aikin da takeyi, koda ta dawo na komawa aiki na itama taci gaba da yin nata, kudi Umma ta fito dasu tace, “waye zai je sayen nama dan na kira mai naman nace ya ajiye muna na dubu ukku, sai aje a anso daga nan asiyo kayan lambu a yanka shi daga can ayi sauri a dawo”.
Kallon Umma mukeyi, Amrah ta ce, “Umma nikam yau duk a har gitse nake ba zan iya fita ƙofar gida haka ba, sai dai ko Nusaiba “
Nusaiba ta ce,”Umma kin san bana shiri da mai naman nan saboda ce mani yake nice matar sa, har mutane yake nunawa cewar Umma ta bashi ni, kuɗin Aure na kawai zai kai dan haka ni kam ba zan iya zuwa ba”.
Dariya muka saka wa Nusaiba muna zolayar ta, “aa Nusaiba kice zamuci nama sosai a gidan ki, tunda kin zama matar mai nama”
Ture baki tayi, na tashi ina dariya na wanko hannu na, na ashi kuɗin na ɗauko mayafi na, zan fita, shuraim yafasa uban ihu da sauri kowa yake kallon sa ana faɗar lafiya? Umma ta ce, “wannan yaron anyi ja irin yaro, nan mu da kake gani halan ba mutane bane ko cin yeka zamuyi ne? Da sha shancin banza”.
Sai a lokacin ne muka fahimci son yakeyi ya biyo ni.
Dariya su Amrah keyi, Nusaiba ta ce, “jirgin yawo abun nema ya samu, to tashi ku tafi kasan halin Anty zata iya tafiyar ta, tunda kana yi mata kukan banza”.
Dariya ya saki da gudu ya ƙaraso inda nake wai kuma sai na ɗauke sa, dariya nayi na ce, “ashe dai baka shirya tafiya ba, yaro nikam da kake gani na a nan ba zan iya ɗaukar ka ba, yaro sai dai kayi zaman ka”
Tunda yaga na juya zan tafiya ta, da sauri yazo ya kama hannu na ya riƙe muka fita yana yi masu bye_bye, aikuwa duk inda muka wuce, sai an bimu da ido, har na fara tsar guwa, a kusuwar kuwa Mai naman ne yaƙi shanye raɗa yake tambaya ta, ina matar sa, ni kuwa na share sa saboda ni kwata_kwata yanzun maza na ajiye su guri ɗaya azzalumai ne kawai.