
Ya yi ta magana yaji shiru, da yake mun saba zuwa nida Amrah da Nusaiba wata rana nida Amrah kawai wani lokacin kuma ni ɗaya shi yasa yasan hali na, dan haka bai damu ba, da share san da nake yi.
Yana bani naman hannun shuraim naja muka nufi gurin mai sai da cucumber carrots cabbage na soya harda green beans da dai sauran su, ya wake ya yanko mani, ya zubo mani a Leda mai zane, ya zubawa shuraim lemo da ayaba da abarba yanka ɗaya_ɗaya godiya nayi masa muka fito ka suwar muka dawo gida abinci dai aka gama komai, Umma ta fita dashi cikin ikon Allah har ana nema.
Tun daga wannan ranar ne Umma a gidan ta abincin yake ƙarewa.
Mama Luba ce, tazo gidan mu cike da masifa wai Umma ta muna fuce ta, duk ta janye mata customer, wallahi tayi alkawarin sai Umma ta zubar da hawayen ta indai har tana cikin garin nan kuma tana siyar da abinci “.
Kallon ta mukayi bamu ce dasu uffan ba dan ko Umma murmushi tayi bata ce da ita komai ba,har ta ƙarasa zazzaga masifar ta, zata fita Umma ta ce, “Luba saboda ke nazo garin nan kuma ke ce kika bani shawarar yin wannan abincin, banso yiba sai da kika roƙeni, kece kika bani gurin fara wannan aikin daga baya kuma kika zo kika hanani kika ce na baki shagon ki, na baki abun ki, shine kika zo yan zun har gidan mu kike futa mani irin wannan muya gun kalaman, to naji Luba ki bani nan da kwana biyu, kizo unguwar nan kuma ki bin cika a garin nan idan har kin tsinci takalmin da na bari a garin nan kije kiyi abunda kika ga dama dashi! “.
Fuuuuu taja iska ta fita kallon Umma mukeyi cikin mugun tashin hankali, nace, Ummmma… Kina… Nufin. Zamu.. Zamu bar.. Garin…. Garin nan ne to muje ina!?.
Amrah ta ce, “Umma kina nufin cewar tsoron ta zamuji ne, to muje ina wai, ko zamu koma garin mune inda ake farau tar rayuwar mu!? “
Kallon mu Umma tayi ta ce, “tabbas mutun abun tsoro ne, kuma zuciya mugun nama ce, hassada mummunar abuce, kada ku yau dari zuciyar ku, saboda idan kun lura da yanda take wannan maganar sam bataji bata gani huɗubar shaiɗan ce kawai keyi mata yawo a jinin jikin ta”.
Nusaiba ta ce, “to Umma ina zamu a yanzun zun nan shike nan mu kullum cikin gudun hijira muke? “.
dariya Umma wadda tafi kuka ciwo tace, “Yaro yarone tabbas duk ku yara ne, kuje ku fara shiri zan zo da dillalai su saye kayan mu saboda tafiyar nan bata yuyuwa da kayan nan namu”.
Hannun shuraim taja suka fita mukam duk jikin mu a sanyaye yake, yanda Umma ta ce, muyi hakan mukayi, koda dillalai suka zo suka siya kayan har tukunyar da muke abinci dasu da katifu, suka bita kuɗin suka kwashe kayan ya ge daga mu sai suturar mu da wasu tarkace ba masu yawa ba, gurin wanda take ansar kayan abincin taje ta biya su, cike da alhini suka rabu, ta biya kuɗin da ake biyar nu na haya, ta dawo da sauran kuɗin.
Da dare sai dai muka shimfiɗa tabarma mukayi shimfiɗa muka, kwanta duk muka kasa yin bacci sai juye_juye mukeyi, har Asubahi, muka tashi mukayi sallah, mu ka fito neman abinci, tea muka dafa muka sha muka wanke kayan muka kwashe komai muka ɗaure a buhu, muka fito da komai a tsakiyar gida duk kowa ka duba zaka fahimci yana cikin damuwa in banda shuraim dake ta haukar sa ko ince shirmen sa, daɗi Kawai yake ji yau zai hau mota.
Sallama mukayi da maƙota muka baiwa mai gidan makullin sa, muka hau mota sai tasha, garuruwa ake faɗa mudai Umma muke bi rasa motar da zamu shiga mukayi, wani mutum ne yazo ya ishe mu da surutu, “Hajiya wallahi motar Yola bata da wata matsala dan daga ganin ku, ku mutanen Yola ne, Allah Hajiya wallahi maganar gaskiya wannan drivar ya iya tuƙi yasan takan aikin sa, dafe goshi Umma tayi ta ce, “muje malam haba! “.
Dariya mukayi duk da irin halin da muke ciki, ai kuwa da gudun sa yake ɗauke buhu huwan har da akwatin mu, mu kam sai bin sa mukeyi da ido, sai da ya kwashe komai muka bisa a baya muka shiga cikin motar, kamar mune kawai ake jira, muna shiga motar na tashi, shuraim kuwa a ƙafar Nusaiba yake zaune sai surutu sukeyi, ni kuma tunda muka shiga cikin motar nan nake jin gaba na na dukan ukku_ukku, addu’a kawai nakeyi duk na zama wata irin ta daban, Amrah ce ta dubeni ta dafa ni na ɗago ido na kalle ta.
Ta ce, “Anty lafiya dai duk naga kin sauya mani kala ba kamar yanda muka fito daga gida ba yan zun kin fi shiga cikin damuwa”.
kallon ta nayi na gir_giza mata kai alamar babu komai na rufe ido na.
Tafiya mukeyi ina ƙara shiga cikin damuwa, sai na kauda kaina gefe na fashe da kuka, wanda ni kaina ban san dalilin yin sa ba, kawai naji muryar Amrah ta ce, “Anty na sani kuka kikeyi ni ba zaki iya ɓoye mani komai ba, amman kuma na fahimta sosai kukan zuwar maki yayi, dan Allah ki daure ki daina kukan nan haka, kafin Umma ta san halin da kike ciki ko Shuraim”.
Ɗaga mata kai nayi ba tare da na juyo ba, tafiya kawai muke yi, har muka isa garin yola koda muka sauka a tasha bamu san inda zamu ba, wata motar kawai muka shiga aka sauke mu a cikin garin.
Goya Shuraim nayi saboda ya gaji kuma yunwa yakeji guri muka samu ajikin wata bushiyar mangwaro muka zauna a kusa da wata hanyar manya_manyan gidaje, shimfiɗa mukayi, mukayi sallar ƙasaru, daga nan muka buɗe abinci muka fara ci amman ni sam hankali na yana gurin wata hanyar da wata motar ta fito a can gaban mu, ba wannan hanyar da muke kusa da ita ba.
Tashi nayi na ce, “Umma” zan je wan can gurin na gani.
Amrah ce ta ce, “muje na taka maki, nima nagano abunda kika tsare da ido tun ɗazun”.
Murmushi nayi, nace, “Amrah “kedai kice gudu kikeyi na ɓata kije nema na baki san inda zaki same ni ba.
Dariya mukayi zamu tafi Shuraim ya taso ya riƙe mani hannu nace wallahi rigimar ka yawa ne da ita, nida zani gurin can ba wani nesa ba.
Dariya Amrah tayi, ta riƙe hannun sa ɗaya muka tafi, hanyar nake bi da ido duk da marece ne, wata bushiyar lemon tsami na kafe da ido a take gaba na ya faɗi, da sauri hawaye suka soma zubo mani, babu tsayawa, cikin tsananin tashin hankali Amrah take gir_gizani tana tambayar miye na gani, kuka na fashe dashi matsanan cin kuka na fashe dashi, na durkusa, ƙasa ina kuka, tambayar duniyar nan Amrah tayi mani amman na kasa bata amsa shima Shuraim ganin kukan da nakeyi ne ya saka shi fashewa da kukan ya rungume ni ta baya.
Da sauri Amrah taje ta kira Umma da Nusaiba suka kwaso kayan mu suka sameni a yan da Amrah ta barni.
Nusaiba ma cikin kukan take tambayar mike faruwa amman duk na kasa basu amsa Umma kuwa juya muna baya tayi, har sai da su Amrah sukace idan ba zan dai na kukan ba, suma ba zasu daina ba, dan dole tasa na goge hawayen duk da basa barin zubar, na ce, “Amrah kuzo muje ba zamu kwana a nan gurin ba, duk da ban taɓa tsammani haka ba ko mafalkin hakan ba, kuma ina roƙon ku da ku zuba mani ido kawai”.
Sukam duk basu fahimci inda maganar tawa ta dosa ba, goya Shuraim nayi ina takawa a hankali kamar wadda ƙwai ya fashe wa a ciki tafe muke ta gefen hanyar muna ta wuce manyan gida jen dake unguwar, bayan wani ƙaton gidan wanda irin su basu wuce biyar ba, amman kam unguwar akwai gida je masu kyau kuma unguwar ta tsaru, ta jikin wata “yar ƙaramar hanya mukabi ta bayan wannan gidan, muka iso gaban gidan.
Nusaiba ta ce, “kai Anty Narjeesah uban waye zai iya bamu gurin aiki idan ya kalli shigar mu da kayan mu, kuma wannan gidan ai sai masu yanka kan yara dan Allah mu rufawa kanmu asiri! “.