NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Kyaleta nayi, na matsa a jikin get ɗin na durkusa, ƙasa na tona wani rami wanda yake da dutse a gurin na janye dutse, wani ɗan akwatin ƙarfe na ɗauko wanda yake rufe a cikin wata ‘yar jaka, na buɗe makullai ne a cikin gurin sai da na duba da kyau na ɗauki ɗaya, naje na ɗorawa Amrah akwatin wadda ta saki baki da hanci tana kallona ko ƙyaftawa babu, a hannun ta, na juya naje na saka ma kullin na buɗe ƙofar sai da na rufe ido na, a lokacin da gidan ya buɗe, tsaye nayi a gurin duk jikina a sanyaye yake, Nusaiba ce ta dafa ni na jiyo na buɗe ido na na kalleta zata magana nace, “Nusaiba” bana son tambaya a halin yan zun dan haka ki ɗauko kayan mu mu shiga daga ciki.

Sanin halina da yanda nayi mata magana ne ya sakata aikata abunda na faɗa, da tsoro_tsoro suka shiga cikin gidan harda Umma ni kuwa sai da na daɗe a gurin da addu’a na ɗaga ƙafata na shiga cikin gidan tare da zubar da hawaye, rufe ƙofar nayi da makulai na ƙara gyara get ɗin gidan, motoci ne guda biyu a harabar gidan duk a lullube suke, abun duk yayi datti bana wasa ba, shuke_shuke ma wasu duk sun bushe wasu sun fito ciyayi duk ko ina in banda cikin barandar gidan.

Wuce su Umma nayi, na dake zuciya ta, naje na buɗe ƙofar da ɗaya makulin na tura ƙofar na jiyo nace “Bismillah Amrah”.

Nice na fara shiga ina shiga na kunna wutar gidan a take gidan ya ɗauki haske ta ko ina gashi gidan babba ne kuma a cikin babban falon gidan duk kujeru ne ta ko ina ga kayan more rayuwa.

Kowa ni yake kallo tare da neman ƙarin bayani, ni kuwa na share na ce, kuzo mu gyara gurin da zamu zauna kafin zuwa safiya kowa ya kama nasa ɗakin duk da nasan Nusaiba da Amrah ɗaki ɗaya zaku ɗauka Umma ɗaki ɗaya, ni kuma ɗaki ɗaya nida Shuraim.

Amrah ta ce, “ok Anty Narjeesah Allah ya taimake mu baki ɗaya “.

Kowa ya ce, “amin”

Makuli ɗaya nasake amsa gurin Amrah naje na buɗe wata ƙofar wanda gurin yake kichin ne da gurin ajiye kayan share_share da goge_goge, ɗaukowa nayi nazo na basu muka fara gyara ko ina, A cikin falon sai da muka gyara Umma da Shuraim suka zauna, a kujera, lokacin sallah ne yayi nazo muka fita gurin fanfo mukayo alwala mukayi sallah nadade ina addu’a har sai da nayi sallar isha’i natashi gurin abinci muka ci kowa da abunda ya ke saƙawa, bayan mun gam.

Amrah ta ce, “dan Allah Anty Narjeesah yaushe ne kika taɓa zuwa garin nan kuma har kika san wannan gidan dan duk abunda kika aikata a tun daga ɗauko makullin gidan nan da buɗe sa da shigowar ki da da yanda kike komai hankali kwance da sanin ma’ajin komai haƙiƙa babu ko shakka kin san abunda mu bamu sani ba”

Nusaiba ta ce, “tabbas Anty Narjeesah akwai abunda kike ɓoyewa wanda mu bamu sani ba dan Allah ki sanar damu dan muna cikin duhu, ki fitar damu haske “.

Amrah ta ce, “Anty Narjeesah tun lokacin da muka tun karo garin nan kike ciki ƙunci da damuwa, kuka kuwa tun a cikin mota kike yin sa har zuwa lokacin da muka shigo cikin gidan nan, miye shi wannan damuwar da kukan kuma ta ya ya kika san garin nan kika san gidan nan batare da sanin muba”.

Shiru nayi jin wannan tambayoyin masu kama da saukar kibau a ƙirjina na, kuka na saka suka ishe ni da tambayar da ƙarfi na rufe ido na cike da masifa nace masu, Gi… Da… Na… NE nan halak malak!.

Duk suka tashi tsaye suka gir giza kai suna faɗar, gidan kine kuma? ta ya ya zaki faɗi hakan ..?

Comment And Share

Ummu Ihsan ce ????????????????????????????????????????????????????????????????????????

???????? NARJEESAH ????????

Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN

ELEGANT ONLINE WRITERS

Bismillahir Rahmanin Rahim

           9⃣⏮????

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Nace dasu babu ko shakka wannan gidan nawa ne, kuma Abu na biyu da zan sanar daku shine bazan ƙara amsa maku wata tambayar ba dan gane da wannan rikitaccen al’amarin, saboda dalilin masu yawa”.

Amrah ta ce, “Anty Narjeesah ki sani mune ‘yan uwan ki baki da kamar mu a nan duniyar Umma kuma itace ta haife ki baki da wata uwa a duniyar nan wadda ta dace da tasan sirrin ki bayan ita, kasan cewar babu wani bare a cikin mu, miya sa ba zaki iya sanar da mu sirrin kiba?”.

Kallon Amrah nayi cikin matsanan cin kuka na ce, “Amrah” duk ku kun yarda da cewar Umma ce ta haifeni amman ni har yan zun ina da shakka akan hakan, miyasa kuka damu da damuwa ta bayan wadda ta can_can ci da tayi mani irin wannan tambayoyin ko fiye da hakan sam batayi ba! “

Umma bata sona, da Umma tana sona da tun kafin na san kaina ita na fara sani, saboda miye zan sanar da sirri na ga wanda bai son jin hakan!? “Amrah Nusaiba “ku jini da kyau wallahi kamar yanda tun farkon lamarin ban sanar da kowa ba, to yan zun ma, baya ga sanar daku cewar wannan gidan nawa ne ba zan ƙara cewa komai ba, akai har sai ranar da Umma ta buɗe bakin ta, ta tambaye ni da kanta, tana son sanin gaskiyar lamarin ni kuma nayi alkawarin a ranar ko ɗigon gaskiya bazan ɓoye mata ba! “

Duk sai suka maida idon su akan Umma wadda tayi kamar bata gurin kamar bata san mike faruwa ba, gyarawa Shuraim kwanciyar sa ma takeyi.

Gir _giza kaina nakeyi kawai na wuce su naje na kwanta akan kuje ɗaya na rufe ido na.

Nusaiba ta ce, ” Umma dan Allah ki.. Kallon da Umma tayi mata ne ya sakata yin shiru, Amrah ma ganin yanda Umma tayi wa Nusaiba itama sai taje ta kwanta, haka muka kwana kowa babu daɗin zuciya.

Tun da mukayi sallar asuba bamu koma ba, da garin ya soma haske muka tashi muka soma gyara gidan, Amrah da Nusaiba ganin irin dukiyar da aka zube a gidan sai da suka tsorata kasan cewar mu a gidan talakawa muka tashi kuma ƙauye, Umma dai har yan zun bata ce damu komai ba, ko cikin dorowa da zamu saka kayan mu cike muke da mamaki har dani saboda kayan da muka gani, zanen gado ya kai bakwai, kuma shaddodi atamfofi les matiriyas iri daban_daban.

Rufewa mukayi mukaje muka ajiye kayan namu a inda suke sai dai muka gyara komai, bayi da muka shiga duk sai da na koyar dasu komai muka fito.

Nusaiba ce taje ta koyar da Umma komai akwai ɗakin da ban buɗe ba wanda bani da niyar buɗe sa, ko kaɗan bana son kallon ƙofar ɗakin.

Sai da muka gama, muka shiga cikin kicin ɗin muka gyara ko ina, store ne na buɗe gurin yayi uban datti sai yanar gizo_gizo, attishawa kawai mukeyi, windo muka buɗe gurin ya ɗauki haske ta ko ina kuma na kunna glub, buhu huwan shinkafa muka gani da kwalayen taliya da indomi da kus_kus da semo cike muke da mamaki wanda su kansu su Amrah sun tabbar da nima ina cike da mamaki.

Amrah ce ta ɗauki taliya ta ɗebi indomi ta fita, mu kuma muka gyara muka goge muka rufe, girki Amrah ta ɗora a rishon da muka zo dashi, ɗaki muka nufa kowa yayo wanka sai da muka fito Amrah taje tayo Nusaiba ce ta zubo muna taliyar mu ukku, Umma ita ɗaya, shuraim shi ɗaya ai kuwa yaƙi ci ya dawo jikin Nusaiba ya zauna yana ci, sai muka gama ne muka wanke kayan da muka ɓata muka fita yawon duba gari amman bada Umma ba.

Haka mukeyi kullum har muka saba da gidan da unguwar muka daina jin tsoron komai.

Watan mu ukku yau a garin nan duk mun ciko mun murje sam bamu da wata damuwar hankalin mu a kwance, shuraim ya cika shekara ukku cif sai shegen surutu kamar Aku.

Zaune muke a kujera muna labari mu ukku Shuraim yana jikin Umma yana yi mata kukan shagwaba, ita kuwa ta biye masa tana lallashin sa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button