NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 37-38
🅿️ 37&38
…wani irin bak’on yanayi dr sadeeq yatsintsi kansa aciki”bemasan time d’in da yafara shafa bayan taba”kasancewar Aysha ce mace ta farko dayatab’a haka da ita” in aka cire hindatu da ammi”cikin cool voice yace”. I’m sorry my sholy”kiyi shiru kinjiko?”
Aysha kuwa gaba d’aya batasan time d’in datayi abinda tayiba”gabanta yafad’i sbd gudun kar agansu amusu wata fassara daban”
Da sauri tabar jikinsa”shikuma still yana rik’e da hannun ta”kallon parlourn Aysha tayi da sauri”tasaki ajiyar zuciya sbd ganin bbu kowa.
yaya sadeeq kacikamun hannuna”kaida kace naje nabaka waje”kuma ka tsaneni…..haba my sholy komai ya wuce”naji ban kyautaba”nad’auki laifina”Ayi hak’uri adena fushin dani haka”
nika cikani”tafad’a tana turo baki”sai kin kalleni kince kin hak’ura bazaki guduba”sannan saina cikaki”
ni wlh saika cikani konayi ihu”tafad’a cikin shagwab’a da turo baki”jiyayi ta burgesa”yanata kallonta yana rik’e da hannun nata yace”.kinga Inda kin hak’ura sai muje ki had’amun ruwan wanka na shirya mutafi office dake ko ?”
nifa bazanjeba”tafad’a aranta tana jin dad’i yau tana wanashi”bayan ada bata isa tayi hakan ba”
yaya sadeeq dan Allah kacikani”basaina maimaita miki ba”shikenan na hak’ura”cikata yyi….tayi sauri zata gudu tana masa gwalo”biyota yyi da sauri”hakan yyi daidai da shigowar hindatu acikin aparlourn ta turo ammi asaman keke….
Basarwa dr sadeeq yayi yatsaya yadena binta"dama yau baka zuwa office?"ammi ta tambaya"
d’ago kanta Aysha tayi da sauri tace”.ammi kina mgn dama?”jiya nafara ta kwarata”jiya kikak’i zuwa dubani ko?”
Ba haka bane ammi”tafad’a cikin jin kuya ta k’araso cikin parlourn ta tsugunna ta gaishe da ammin”kafin tace”. Alhmdllh! sauk’i nata zuwa ammi”
Dr sadeeq kuwa tsaye yyi yana kallonsu da sauraren su”
mamaki yayi yadda ammi ta manta dashi tana jan Aysha dafira”yyinda hindatu kesaka musu baki”
ni ammi menayi dabaza’ayi firan daniba”
??za’a nuna mun wariyar launin fata”
Ammi na murmushi tace”.bakaso Ayi dakai ba sadeeq”yana k’ok’arin mgn wayarsa tayi ringing”d’agawa yyi ,can yace”.lafiya qlau anjima kad’an zan iso insha Allah”yana fad’in hakan yakashe wayar”
yaya baka zuwa office yau?”cewar hindatu”zanje mana tambai”to kazo kayi break fast d’in mana”tafad’a tana dariya”
Okay yafad’a yana satar kallon Aysha suka had’a ido ta murgud’a masa baki”ammi dake lura dasu tace”.Aysha tashi kije kiyi kalaci kinjiko?”
na k’o..wlh ammi gulmace kawai batayi break fast ba”cewar dr sadeeq yana tafiyarsa dining area”
Hindatu kuwa wani shegen murmushi tasaki”tana mamakin yadda yayan nata ke shirin hawa net work d’in wannan jaririyar yarinyar”
Aysha kuwa batace komaiba ta tashi ta wuce dining area d’in”kujera taja ta zauna”
my sholy yau bbu gaisuwa?ko baki hak’ura bane??”bbu komai na hak’ura fa yaya sadeeq”ansan musulmin k’warai da hak’uri da kauda kai”amma banji dad’i ba abinda kamun jiya”dan Allah karka koma”ayanzun matsayin yayana na d’auke ka”tunda bana b’oye maka sirrina ko?”
Tunda take mgn yakafe d’an bakinta,me pink lips da kallo har tayi shiru”
nima my sholy irin wannan tunanin danayi yasaka najira zuwanki na rarrasheki”amma idan bakyaso mudena fad’a dake to karki mun musu kinjiko?”shikenan”tafad’a kanta ak’asa”
zaki bini muje asibitin?”zanzo asaman adaidaita”meyasa bakya son bina ne?”bbu komai”naga banjima agun ammin ba”
Dama sholy ke malama ce?”yafad’a yana bud’e warmers d’in”d’aliba ce daini yaya sadeeq”
uhmmm tashi ki had’amun tea”batayi musuba ta had’a masa”itama ta had’a kad’an”
Ta zuba masa farfesun kaji”ta zuba masa doya da k’wai”dukta tura masa agabansa”i ta kuma bread me yanka yanka ta d’auka guda 2″tafaraci da tea d’in”
Kallonta yakeyi”yalura batada kwad’ayi da had’ama”irin na wasu mararsa hali”kuma batada son abin duniya”dukda ada baya mata wannan kallon.
my sholy badai wannan shine break fast d’in kikeyiba?”shine mana yaya sadeeq”ina key d’in d’akin naje nahad’a maka ruwan wankan”kafin kagama”
ban yarda wannan abin zai miki wani abuba”bayan period kikeyi”ko jinin yad’auke ne?
kasa mgn Aysha tayi sbd kunya da nauyi”ta lura shifa ko ajikinsa”yanayin abinsa iya gaskyarsa”dama ance ai likitoci basuda kunya ai…. answer me idan kingama tunanin”
turo baki tayi tace”.nidai kabani key naje”kinsan Allah ni bbu ruwana zan azaki asaman cinyata namiki d’ura koki zuba abincin kirki”
tasan tsab zai iya”tunda jiyama a restourent datak’i fitowa “d’aukarta yasoyayi”ita kuma batason hakan nafaruwa tsakaninsu.
1’2’3… Dr sadeeq ke counting”da sauri ta bud’e warmer ta zuba doya da k’wai guda 2 acikin plate”cikin marairaice murya tace”.dan Allah wannan idan nacinye ta isheni yaya sadeeq”
kansa kawai yagyad’a bece komaiba”yanadai kallonta ta gefen ido”ita kuma tanaci atakure harta idar”
hannunta ta goge da bakinta da tissue”irin yadda taga hindatu nayi”
Hindatu kuwa gulmar Aysha da dr sadeeq takeyiwa ammi”ammi dai nata sauraron ta tana murmushi.
Aysha kuwa key nasa dake saman table d’in ta d’auka batace komaiba”
tama rasa meyasa takejin kunyar ta wuce su ammi dake zaune”
Kin idar Aysha?”Eh zanje na d’akko masa sak’o ne”murmushi kawai ammi tayi batace komaiba”Aysha ta wuce.
Dr sadeeq kuwa yana idarwa yabi ta k’ofar baya”kai tsaye sashensa ya wuce”
Aysha nafitowa dg toilet nasa ,shikuma yana shigowa bed d’in”gabanta taji yafad’i”duk taji wani tsoro”tayi k’asa da kanta, tak’i yarda ta kallesa”d’an tab’e baki yayi sbd yalura da yadda ta wani firgita”
zanje idan ka gama saina fito”kisamun number naki namiki flash mana”yafad’a yana mik’a mata wayarsa”
Amsa tayi da sauri ta nufi bakin k’ofar fita dg bed room d’in”wai my sholy dafaki zanyi ad’akin ne kome kike wannan kirman?”da sinne sinne kin k’i kallona”
K’asa tayi da kanta batace komaiba”kifito mun da kayan dazan saka?”yana fad’in hakan yajuya yashige toilet d’in”
Ajiyar zuciya tasaki”itadai harga Allah atsorace take”batason zama ta kadaice ita da wani namiji”sbd bata manta abinda taheer yaso yamata ba.gashi yanzun tarasa meyasa idan taga yaya sadeeq dakejin fad’uwar gaba”
gun ward rope nasa ta nufa ta bud’e”bayan ta saka number d’in ta ajiye wayar”wani fitinan nan k’amshi yadaki hancin ta”aranta tace”.masha Allah!sbd ganin tulin uban suturar sawarsa”komai layinsu daban”shadda,yadi, k’ananun kaya,vest,boxers,dadai sauransu ko wane layinsa daban.
farar shadda”giznah me tsadar gske”riga da wondo ta fiddo masa”ta ciro masa hula bak’a kalar zaren”ta ajiye da sauri tabar d’akin”
sashensu ammin ta koma”tasami hindatu na waya da mijinta”
Ammi kuma na zaune” Aysha kin dawone?”Eh”dama ammi akwai zam zam d’in?”Eh akwai komai”jiya banyiba wlh banajin dad’ine shiyasa”amma na warke”
Subahanallahi Allah yasawaka” meke damunki?”ciwon kaine”tafad’a tana nufar bed room d’in ammin”
Komai ta had’a tadawo parlorn”bayan tabata nashan ,hindatu ta amsa tana shafa mata a sassan jikinta.
Aysha kuwa tayi k’asa da kanta tana latsa baby nokia d’inta”kira akayi” bak’uwar number ta shigo”ranta yabata dr sadeeq ne”
D’ago kanta tayi tace”.ammi natafi Allah yak’ara lafiya”Ameen Aysha nagode kinji?”murmushi tayi tace”.anty hindatu na wuce”to sholyn yaya”tafad’a tana dariya k’asa k’asa”ita dai Aysha batace komaiba ta tashi ta fita.
Hindatu na murmushi tace”.wlh yayane yakirata”tabbas ammi son yarinyar nan yakeyi”bayan yagama cika bakin….kinga wlh nidai bbu ruwana idan yajiki”cewar ammin”shiru hindatu tayi bata koma mgn ba”