Ni da Dr. SadeeqNOVELS

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 41-42

🅿️ 41&42

bayan wasu watanni

Alhmdllh rayuwa ta lula”wata ran da dad’i wata ran akasin hakan”Aysha ta kammala SSCE d’inta alast week daya wuce”bisa tallafawar dr sadeeq”yyinda shak’uwa” ko nace soyayya mai zafi tashiga tsaninsu sosai da sosai.dukda dg shi har ita sun kasa gane son juna sukeyi”ammi da hindatu sun saka musu ido suna jiran jin dr sadeeq zai furta yanason Aysha ko kuwa….yyinda dr sadeeq yaso yasi mata waya amma tak’i yarda har yanzun”har fad’a sukayi akan haka”har suka shirya kansu.

Duk week end Aysha na gidan ammi suna tare da dr sadeeq"idan kuwa Alhamis ne da friday"idan taje office nashi 2 sai 6 tadawo gida.gaba d'aya gulmarsu akeyi a asibitin" ana k'us k'us"saidai bbu damar furtawa sbd sanin halin dr sadeeq d'in"
    gefe guda kuma jikin ammi saidai muce Alhmdllh"domin ciwo farar d'aya yakeshiga"amma sauk'i sai Ahankali"to hakan yakasance"hindatu mijinta yadawo tana gidanta dake G R A"anty binta "tazo dg yola k'anwar ammi"itace ke kulawa da ita"kasancewar bazawarace tana zaman gida.ayanzun tashine kawai ammi yarage mata"addu'a yi akeyi bbu fashi"samun sauk'in ta yasaka hankalin dr sadeeq ya kwanta"mlm muhammad yayan dr habib shine yaci gaba da bawa ammi taimako har yanzun"yyinda honorable lawal na nan daram agidan"bbu zancen ranar girkin ammi"duk time d'in daya gadama zuwa yakeyi"yakuma hanata amsar magungunan tsari"bata fasa amsaba tasharesa.khaleefa kuwa yana nan da soyayyar Aysha aransa"saidai ammi tabashi hak'uri"tunda hindatu ta fad'i Aysha bata sonsa ai....Aysha ta k'ara zama budurwa sosai"tak'ara haske da wayewa"sbd canjin abinci da suttura.

Aysha kuwa baffa idi yasaka mata ido sbd shidai ba kwana agida yakeyi ba"sadda zai dawo Aysha na skul ko gun aiki"sadda zata dawo benan"saidai goggo sa'a tamata bak'ak'en maganganu"

Alh nura kuwa yana kan bakasansa game da Aysha”dg shi har baffa idi”ko yanzun baffa idi wani hukunci ya yanke game da Aysha “saura kiris kuma yacika burunsa”ammafa aganinsa…

 "mahaifiyar Aysha BINTU !tazo ganin Aysha  itada danginta"sai akayi sa'a ranar Aysha ta dawo gida da wuri"bayan tasamesu tayita murna"ga uban siyayya ummanta ta mata"Aysha naso tasanar mata halin datake ciki"amma tana tsoron umma tace".zata tafi da ita batsari"sbd ita yanzun batason rabuwa da dr sadeeq"dukda ta sanar mata tana aikine na goge goge a asibiti"ta kuma sanar mata yadda dr sadeeq kebata kulawa"sosai ummanta taji dad'i"takuma yimata fad'an ta rik'e mutuncinta da talaucinta aduk Inda tashiga....sunjima suka tafi"bayan Aysha ta amshi number d'in umman.

Ayau yakama friday!kasancewar Aysha yanzun ta Ida skul”tunda wuri tabar gidan kamar kullum”gidan ammi ta wuce”tasamu dr sadeeq baya nan”tun asuba yana asibiti emergency room aka kirashi.

Ai Aysha k’in tsayawa tayi “tayi break fast d’in da ammi kecewa ta zauna tayi”

Aysha tace ita ta k’oshi ta fita”gaba d’aya fa jiyane da marece rabonta dashi”amma yau tanajin kewarsa sosai”

Adaidaita ta hau”suna isowa asibitin ta sauka ta wuce ciki”

Office nashi arufe yake”kasancewar yahanata shiga Inda tasan yana tare da maza”yasaka ta kalli murtala”

pls kaje emergency room ka amsomin key agun yaya sadeeq”

Hmmm!Inda shine yakirani sainaje na amso miki amma bazanje aikenkiba”ba aike bane taimako zakamun pls”gsky bazan iya ba”

batace komaiba ta matsa nesa dashi ta fiddo wayarta ta kira dr sadeeq”

k’a’idarsace idan yana duba patient d’in dasuka shafi Emergency baya d’aga kira”amma dayaga my sholy
da sauri yad’auka”yaya sadeeq!na’am my sholy”kinzone?”Eh mana”kuma naga bakanan “wannan murtalan nace yazo gunka ya amsomin key”wai bazaijeba”gashi ka hanani zuwa gunka inkuna tare da doctors”okay abinda yace kenan bazai zoba?? Eh”nidai kabada akamun konatafi gida”sorry kinji ko?”zan aiko miki yanzun kijirani “dato ta amsa tana kashe wayar”

babu jumawa saiga wani dr lukman da keys d'in office d'in yakamata"

Ta amsa ta bud’e”bayan tashiga tashare ta goge office d’in k’al”ta wanke toilet ta zauna tana hamma”sbd batayi break fast ba”

gaba d’aya ta gaji da zama”tana zaune kan kujerar dayake zama tana latsa wayar ta”kusan awa guda amma shiru”cake da lemo ta d’auka a fridge nasa taci ta k’oshi”bacci yyi awon gaba da ita.

Dr sadeeq kuwa yana aiki amma hankalinsa nagun sholy”har kiranta yyi sau biyu tana bacci ba tayi picking ba”

yana idarda da abinda yakeyi yawuto nan”kallon da murtala yaga dr sadeeq na jifarsa dashi yasaka yasha jinin jikinsa”

sannu da aiki both"banza yamasa yana tsayawa gun table nasa"dg yanzun idan sholy ta buk'aci kamata wata alfarma"banaso ka duba k'arantarta"inaso kamata alfarmar sbd ni"insha Allah zan kiyaye"

Beyi mgn ba ya wuce office d’in”yana tura k’ofar”idanuwansa suka sauka kan Aysha dake baccinta hankalinta kwance”

gashin gaban goshinta duk yafito”sbd bbu d’an kwali akanta tasaka hijab d’in jikinta”

Eyelashes nata yabi da kallo kamar anzana”ta tsuke pink lips d’inta,ta d’an turo baki”

Lumshe idanuwansa yyi azuciyarsa yace”.sarkin tsiwa”har baccinma anayi ana turo baki”

Kan kujera 2 seeter yafad’a yana sakin ajiyar zuciya sbd gajiya”dg shi sai jallabiya brown colour”kansa bbu hula da silifas ak’afarsa me cike da gargasan gashi”

mik’ewa yyi kan 2 seeter d’in”wanda rabin kafufuwansa ak’asa suke”ga yunwa yanaji”

amma gaba d’aya duk wani motsin Aysha akan idonsa ne”wayarsa yazaro yyi kiran wani mukhatar yamasa order na break fast”tashi zaune yyi bayan yagama wayar “

Toilet yashiga”bayan yafito yatsaya agaban Aysha ya yarfo mata ruwan hannunsa”

saurin bud’e idanuwanta tayi tana addu’ar tashi dg bacci”had’a ido sukayi”ta shagwab’a fuska”yaya sadeeq shine katasheni ko?”

my sholy duniyar tamiki dad’i ko?”ni ganinan agajiye ,amma ke bacci kikeyi ko?”

Ayya sannu yaya sadeeq”dama nagaji da jiranka shine nad’an kwanta”

Kujera yaja ya zauna yace”.kinga dakin yarda kinyi wayar saikiyi game ko?”nidai zansiya da kud’i na ai”yana murmushi yace”.china phone zaki siya ko?”Hmmm bbu komai idan nasiya”kasan ance iya kud’in ka iya shagalinka”

hakane my sholy”yafad’a yana tunani aransa duk karancin shekarunta tanada sanin yakamata”

wai dama ko wanka bakayiba?”Eh mana yanzun break fast namana orde sai muje ki rakani nashirya ko?”nidai yaya sadeeq ina nan zan jiraka”

meyasa bazaki rakaniba?”kunya”tawa kuma?”ammi mana”kuma nina yi break fast”cikina acike yake”me k’arya?”

Hmmm idan zakaje gidan zaka ajiyeni gun saloon pls”to shikenan my sholy”

yafad’a yana kallon yatsun hannunta”2days kindena yin lalle”meyasa?”wacce kemun anmata aure”

saura kema kiyi auren ko?”gabanta yafad’i cikin jin kunya tace”.taf y’ar yarinya dani za’a mun aure”

Kwanaki wanima yazo gun baffa da gske zai aureni”cikin bugawar zuciya dr sadeeq yace”.sai kikace me?”

ni dama bana sonsa”kuma baffan yakoresa”hmmm mazan yanzun wasu suma sai addua”duk wanda yace yana sonki karki amince my sholy”kuma ki sanar mun kinjiko?”tana k’okarin mgn aka turo k’ofar”dr Abbas yashigo da sallama”

Atake dr sadeeq yahad’e rai”Aysha kuwa shiru tayi ta kauda kanta”sbd ta lura da yanayin both nata”

Abokina idan bbu yak’i meyakawo gaba?”aika amsa sallama tawa ko?”

Idan abu me mahinmanci yakawoka pls sanarmun “I’m very tire!

Dan Allah inaso kamun wata alfarma abokina”abaya na buk’aci kabani yarinyar nan aro ta gyaramun office”kak’i har muka kusa samun sab’ani dakai”

Cikin k’osawa da kalamansa dr sadeeq yace”.bancika son yawan dawo da abinda ya wuce abaya ba”sbd haka idan maganarka bbu mahinmanci ka juya pls”

Tab’e baki dr Abbas yayi yace”.Inda bacin alfarma nazo nema dana koma kawai”

yarinyar nan Aysha ko sholy naji kana kiranta?”dan Allah
inason ta tsakanina da Allah
inaso kabani dama nayi mgn da ita”tunda yanzun amatsayin karkashinka take”may be dg baya naje nasameta agida kawai…..✍️

🤭😳🤫

Team d’in sholy dana dr sadeeq kufito akafta guys🤣 idan Banga zafafan comments ba bbu update da safe😎😎

mom fareesa🖊️

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button