Ni da Dr. SadeeqNOVELS

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 49-50

🅿️49&50

……..wani irin mugun bugawa k’irjin baffa idi yayi” sakamakon tozali da yayi da Abban Aysha tsaye”yana jifarsa da wani irin kallo”

yayi bak'i yayi rama ,kamar bashiba sbd azabar daya kesha tazama gurin"

tab’e baki baffa idi yayi yace”.ka kalleni da hujja”saina kassara rayuwar y’ar ka”natsaneka tun fil’azam sbd kafini komai na rayuwa”

Wasu hawaye masu zafi suka zubowa Abba yashare beyi mgn ba”wasu yaran su suka jashi suka d’aure”

Idan kun hanani nayi sallah ai bakina bazaku hanashi kiran sunan ubangiji naba”kobana raye idi sai asirinka yatono insha Allah”tun anan duniya har k’iyama”kaci amanar zumunci Allah sbd abin duniya”tunda na tsintsi kaina anan gurin raina yabani kaine ka kawoni”ashe bayan ni har Aysha y’ata kanason ganin bayan rayuwarta”kuma bayan haka ku k’ullawa bawan Allah sharrin kisanta….wanda bejiba beganiba s….

Abba be Ida mgn ba suka jashi zuwa wani d’aki”baffa idi duk jikinsa yyi sanyi”gashi bbu damar yabar k’ungiyyar su.

su Alh nura da suka lura da haka sai sukayita jansa da zancen kud’i zaiyi”karya damu miye miye…dg nan suka shige wani d’aki suka cigaba da aikin shirkarsu”
(Allah yatsaremu yashiryamu)

   *************

Ab’angaren Aysha kuwa bayan tagama addu’o inta batayi bacciba”sbd damuwa da b’acin rai”

Akan kunnanta aka kira asuba”saidai kuma dataje kama ruwa taga bak’on ta”

gyara jikinta tayi ta d’auki abinda take da buk’ata tasaka a hand bag nata”ta d’akko wata leda babba tayin shopping ta cika da kayanta tayi zaune ad’akin”

Ahankali ta d’auki kayan da takalminta takai soro”tadawo ta rufe k’ofar d’akin datake kwana Ahankali ta ajiye takalminta k’ofar d’akin”kafin tajuya ta nufi soro.

Ahankali ta zare sararaf d’in k’ofar soron”sannan ta fita tajawo k’ofar Ahankali”

anata sallar asuba garin yad’an fara haske”yaya abdul ta hango yafito dg gidansu zai tafi masjeed”

Da sauri ta lab’e,yana wucewa ta shige soron gidansu ta tura k’ofar ciki ta shiga”

Kai tsaye d’akin fatima(k’awarta)acan ta nufa”tasamu fatima na sallah”

atsorace ta katse sallar”sai kuma taga Aysha ce”lafiya Aysha naganki da asuba kuma?”

Kinga bacci nakeji”zan kwanta anan zuwa ko 11 nasafe sannan baffa yadawo yagama zamansa gida yafita”banaso kowa yasan nazo gidan nan”idan natashi bacci zanmiki bayani”

dato fatima ta amsa ,sbd tasan halin da Aysha d’in take ciki”
kayan Aysha d’in tasaka cikin akwatinta”sannan ta ajiye mata takalminta k’asan katifa”tasakawa k’ofar net d’in sararaf”

Aysha taja ajiyar zuciya ta kwanta kan katifar fatima”yyinda fatima tacigaba da sallarta.

Dr sadeeq kuwa ransa yab’aci akan k’in amsar wayarsa da Aysha tayi”

Duk zuciyarsa nasanar masa yarinyar batada kwad’ayi”kuma tanada gudun duniya”

da fushin ta yakwana”washe gari azatonsa zai sameta a asibiti”amma shiru bbu ita bbu alamarta”

yayi zaton toko itama fushin takeyi dashi”duk yadda yaso yashare zancenta azuciyarsa yakasa” jiyayi baya iyawa”

wayarsa yajawo yakirata amma bata shiga”yah salam my sholy ya kikeso nayi da raina?wane irin fushine kikeyi dani harda kashe mun waya”yafad’a cikin damuwa.

gaba d’aya sai yaji bayason zama asibitin idan bbu sholy”

gabansa yafad’i daya tuna halin baffanta”atake zuciyarsa tabashi kodai yahad’a sholynsa da wani yatafi da ita?”

Da hanzari yakira driver d’in gidansu yace”. yabashi 10 minit yazo yakaishi gidansu sholy”

Abakin get d’in asibitin suka had’u da dr sadeeq bayan cikar minti 10 d’in”

Da kansa dr sadeeq ya amshi driving d’in sukayiwa anguwarsu Aysha tsinke…..

Aysha kuwa k’arfe 10:15 ta farka dg bacci”bbu kowa d’akin”

madubin fatima ta d’auka ta kalli yadda fuskarta ta kumbura da idanuwanta”

wasu hawayen masu zafi suka sake wanke mata fuska”

Hakan yyi daidai da shigowar fatima d’akin”kintashi Aysha ?”
Eh bara nayo fitsari”dg haka ta fice tsakar gidan”anan suka gaisa da umman su yaya Abdul”sannan ta wuce bayi”

sosai umman taji tausayinta”sbd kallo d’aya zaka mata kasan tana cikin damuwa”ga idanuwanta da fuskarta sun nuna hakan.

bayan ta fito take sanarwa fatima da komai tana kuka”

gsky bemiki adalciba”insha Allah Aysha zaki dara wataran”Allah yasaka miki kawai zamuce.kibari kiyi kalaci saiki tafi batsarin ko?”

gun yaya sadeeq zanje yasaka akaini”ina tsoron zuwa nikad’ai kinga da akwai nisa”dg nan zuwa can tafiyar awa 6 nefa”

batun kalaci bazan iyaba fatima”yanzun kinga sha 11 saura baffa nasan yana bacci”gara nabar anguwar nan tun kafin yagane kawai….

Tafad’a tana tashi tsaye ta d’auki kayanta ta saka takalminta”fatima ta rakota waje”

Anan suka sami mlm Hamza da yaya abdul saman dankali ak’ofar gidan”

Aysha meke faruwa naganki da kaya,idanuwanki ahaka?”mlm Hamza yatambaya yana mata kallon tausayi”

hawaye na zubo mata ta sanar masa batsari zataje sbd baffa zai mata auren dole”

salati mlm Hamza yyi yace”. lallai idi yaji tsoron Allah wlh”amma hakk’i bazai barshiba”kuma ina goyon bayanki kije kisanarwa sauran danginku”amma ina zuwa”yafad’a yana tashi ya shiga cikin gidan”sbd yakamata kud’in mota.

yaya abdul daketa kallonta yana k’ok’arin mgn yaji horn d’in mota”da sauri sukabi motar da kallo shida Aysha”

Dr sadeeq tunda suka shigo layin idanuwansa suka hango masa Aysha”

Atake wani bak’in kishi yataso masa,sbd ganinta da yayi da yaya abdul”tana tsaye gefensa”

yana gama parking yafito”Aysha ta zaro ido tana hangosa”

nufota yyi fuska agimtse”saidai gabansa yafad’i sbd ganin idanuwanta alamar taci kuka ta k’oshi”

Ita kuwa tsaye tayi hawaye na zuba afuskarta tace”.yaya sadeeq!

meke faruwa my sholy?”waye yasamunke kukane?”yafad’a cikin cool voice yana k’arasowa gefenta”k’amshin turarensa yadaki hancin yaya abdul dake kallonsu kamar TV”

Aysha kuka me cin rai tasaki tana fad’a wa jikinsa…. jiyayi tamkar zai yi baya su fad’i”

Cikin rarrashi yajanyeta dg jikinsa yakama hannunta” yabud’e back sit yasakata, shima yashiga ya rufe.

Hannunta guda yarik’e menene kike wannan kukan my sholy??”fad’amun kinji?”

ba fushi kakeyi daniba yaya sadeeq”bana iya juran fushi dake my sholy”dama abinda naguda karnazo nasameki adamuwa”fad’amun menene?”

Baffane zaimun auren dole nan da sati 2……innalillahi wa inna ilaihir raju’un! yafad’a azuciyarsa yana jin wani zafi da k’una”had’e d’akin tsanar baffa idi”wanda betaba ganinsa bama afuska”cikin damuwa yace”.Jikina yabani bbu lfy shiyasa danajiki shiru nazo nagani.

wannan karon bai isa yashiga hakk’inki ba wlh”ayanzun zamuje har gun dangin Abbanki Ayi mgn”zakije ko?”

Uhmm! tafad’a kanta ak’asa”tafin hannunsa yasaka yad’ago hab’arta”lumshe idanuwanta tayi”yaja dogon hancinta yace”.banace kiyi shiru ba?”

handcheef yazaro yagoge mata hawayenta”yajanye hannunsa dg fuskarta yana kallon ta cike da tausayawa kafin yace”.muje yanzun gun ammi kiyi wanka da break fast saimu tafi batsarin ko?”

nidai yaya sadeeq zanji kunya muje can kawai”Hmmm!ammin taki kike kunya my sholy?”nasan jinin yazo ko?”rufe fuskarta tayi datafikan hannunta tak’i mgn”

murmushi yyi ya matsa nesa da ita yabud’e murfin motar”

Hakan kuma yayi daidai da hango mlm Hamza na nufosu”Aysha tayi saurin cewa yaya sadeeq ga mahaifin yaya abdul nan dake taimakamun”dato kawai ya amsa yafito dg cikin motar”itama ta fito”

yaya abdul kuwa cikin gidan yakoma bayan shigarsu Aysha mota.”

yagama yarda Aysha da wannan mutumin d’an gayu soyayya sukeyi”saidai fatanta Allah yasa mutumin dan Allah yakeson Aysha” bada niyar b’ata mata rayuwa yazo ba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button