NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Yana fitowa kiran Haulat ya shigo wayarshi har ta kusa katse sannan ya ɗauka shiru dukkan su suka yi,daga bisani ta ce mishi a hankali cikin wata irin murya wacce tasan tana kashe mishi jiki”Naufal dear!
Saida ya runtse ido sanan ya ce mata shi ma a hankali “Yess dear!
Kina son mu faɗa halaka koh?
Taɓe baki tayi kamar tana kallon shi”Ba halaka ba ne ,kawai dai muna ɗan rage zafi ne,kuma ai aure zamu yi to meye”
Hura hanci yayi a ranshi ya ce”Ban san da wani yare zan fahimtar da ke ba Haulat”
A fili ya ce”Haulat mu manya ne kuma muna da addini ya hana mu zina,wanan abun da kike kokarin ki ga munyi zina ce”
Taɓe baki take yi ,ta tsana wanan wa’azin da yake mata,dan ma karya ishe ta ce “Eh gani nan,dear momy tana kira na later” tana faɗa ta kashe wayar haɗe da jan tsaki a fili ta ce “Ni ban taɓa ganin handsome guy kamar ka ba,gashi a india kayi karatu amma duk a banza tunda baka waye ba”
To idan baka mutu ba zaka ga abubuwa wai yanzu fa idan mutum mai aikata zina bai waye ba tirrr allah ya tsare ya tsare zuciyar mu amin ya rahimm.
~~~~~~~~~~~~~
Duk da kasancewar ta tashi jikinta ba ƙwari amma haka nan ta fara shirin makaranta,bayan ta shirya tsabb na kafa mata ido wata ba ƙaramin kyau kayan suke mata be.
Ƙasa ta sauko tana saukowa taga hajia ɗauke da plate a hannun ta murmushi Sabreen tayi,saida ta ƙaraso sanan ta ce “Ni da kaina zan ci ”
Murmushi hajiar tayi “inah ni zan baki”
Zama tayi a hannun kujera dan ta san halin hajiar.
“Yauwo ko kefa ƴar aljanna” hajiyar ta faɗa sanan ta fara bata abincin ta shi kaɗan sanan hajiyar tai mata rakiya har gurin motar.
Tun kafin su isa makarantar gaban Sabreen ya fara faɗuwa bata kawo komai a ranta kuma bata ba abin wani muhimmanci ba balle tayi zargin wani abu.
Kasancewar ta je da wuri ba mutane sosai yasa ta zama ita kaɗai a class,rubutun malam Haulat da ta gani a jikin allon ne yasa ta tuno da ita,dan Sabreen bata da riƙo ko kaɗan shi yasa ɗuk abinda aka mata sai ta rama dan karta riƙe mutum.
Murmushi tayi a filli ta ce”Su malama Haulat ƴan kilibibi manya,ina fah kika iya kilibibi ai kilibibi sai Ya Naufal”
Dariya tayi tuno yadda yake gudanar da al-amuranshi.
Tana cikin tunani ƴan ajin suka fara isowa kowa tambayarta ya ke yi lafiya ,suna son Sabreen dan ta iya abin dariya gashi bata gani ta ƙyalle sai ta tanka.
Cikin ƴanga da iyayi da kilibibi Haulat ta shigo ajin,gaba ɗayan su suka miƙe tsaye suka gaida ita harda Sabreen dan yanzu bata riƙeta ba.
Kamar yadda suka saba gani sai ta gaya abinda ta ga dama sannan ta amsa musu gaisuwa yanzu ma hakan ne,har Sabreen zata zauna dan ta gaji da tsayuwar Haulat ta ce su zauna.
Haulat na miƙewa ta hango Sabreen wani daɗi taji murmushi tayi ta taka har gurin Sabreen ɗin ta ce”Sabreen ya ƙafar ko ita ce ta hanaki zuwa makaranta kwana biyu”
Ita ma murmushi tayi ta ce”No kike cewa ko?
“to No ba ita ba ce”
Murmushi Haulat tayi a ranta ta ce”Yarinya kenan wai da ni zaki ja”
A fili ta ce”Okkk
Tana faɗa ta juyo gurin allon kamar yadda ta saba karantar da su haka yau ma tayi,bayan ta gama ta fita tana murmushin mugunta.
“Hello kana ji na yau ta zo,ka shirya lokacin break ni kuma zan san yarda zanyi ta fito.
“Okk baki da matsala Haulat”
Ana kaɗa musu ball masu fita suka fara fita dan Sabreen ita bata zuwa break.
Tana Zaune tana fira da ƙawayanta wata yarinya ta shigo ta ce “Ina Sabreen muha’d mai taƙama?
kallon yarinyar tayi ta ce ” gani wake naima na,wani uncle ɗin ku ne yana waje” yarinyar tana gama faɗa ta fita daga ajin.
“Toh gani nan zuwa”ta faɗa bin bayan yarinyar tayi ,tana fita bata ga yarinyar ba,tafiya ta fara yi tana waige-waige.
Yana ganinta ya nufu ta,ga gurin ba mutane sosai,bata lura da zuwan shi ba,kawai sai taji ya bangaje ta,wani abu ja me irin jan jini ya watsa mata.
“Innalilahi wa’inna ilairaji’um Sabreen ta faɗa tana kallon jikin ta.
“Subhnanllah! yi hakuri ban kula ba,mu je dan allah ki wanke kar ya kama uniform ɗinki.
Ba musu kuwa ta bishi har wani ɗaki me kama da office,suna shiga ta tsaya mamaki ya kamata ganin yana cire rigar jikin shi,wani irin nishi ya fara yi.
Gaba ɗaya Kan Sabreen ya ɗaure bata gane abinda yake yi ko nufi ba,shi kaɗai yake wani irin abu,dan akwai tazara a tsakanin su da shi ma.
ƙwanƙwasa ƙoka aka fara yi,kallon kofar take yi tana kallon shi,da ƙarfi aka buɗe kofar aka shigo wani uncle ne mara mutunci wani irin kallon mamaki yake mata”Me zan gani daman haka kike”
Cikin rashin fahimtar inda zancen shi ya nufa ta ce”Haka nake kamar ya”
“Rufe min baki ƴar iska kawai daman haka kike”ya daka mata tsawa.
“Iskanci!” ta faɗa cikin rashin sanin inda zance ya nufa.
“Dallah karki wani nuna baki san komai ba yau asirin ku ya tuno”
“Waiyo allah na shiga ukku wllh yau ne kawai kuma yau ɗin ma ba muyi koma….
Tsalla rufe min baki yau sai kun bar makarantar nan.
Gaba ɗaya kan Sabreen ya ɗaure ta kasa gane abinda suke nufi kalmar iskanci ya duki zuciyarta.
jiki ba ƙwari kamar wacce aka yiwa dukan tsiya ta ce “Ƴau ne kawai ku….
Tun kafin ta ƙarasa maganar taji zaukan Wani wawan mari wanda ƙarar saukar shi ya tsayar mata da jin magana,ga hawaye ya ƙasa xubuwa.
Hannunta ya ja har office ɗin principal ɗin,har suka isa bata jin abinda suke cewa.
Suna shiga daman su huɗe ne malama suka gaya wanan mara mutunci ne ya ce mishi “A ɗakin sani naani su ka kama su suna iskanci”
Wanan kalmar ita ta duki kunnan Sabreen zuciyarta ta buga ta karfin haske sai yanzu hawaye suka samu damar zubuwa.
A ruɗe principal ya ce “What! yana kallon ta no it c…
“Ya isa haka ki kwantar da hankalin ki Naufal ya zama naki”
A zuciyarta ta ce” Hmm Malama Haulat kenan ba kin ce naje na aure jahili ɗan ƙauye iri na ba,to zaki ga jahili ɗan ƙauyen,zan iya yin komai dan ɗaukar fansa akan ki,dole na aure miki shi kuma ya zauna da ni”
“Ƴar Aljanna ya isa haka bana son jin kukan ki,kiyi shiru kinji”
“To Hajiyata zanyi shiru”
“Yawwa ko kefa”
“Hm Malama Haulat sai kinga ramuwar gaiya,wacce zata tsorata ki ,ta ɗaga miki hankali” a zuciyarta take wanan maganar.
Sun daɗe a ɗakin kafin suka fito falo suka zauna,hajiyar ta kalleta ta ce”Bari naje na kira Alhaji”
“Toh kawai ta ce mata.
can ƙasan zuciyarta tana jin tsoro ya Naufal zai ɗauke maganar tasan baya sonta ita ma bata son shi ko kaɗan hali da ra’ayin su ba ɗaya ba,amma guguwar ɗaukar fansa ta hana ta yarda da jin tsoran yadda abuvuwa zasu kasance,ta ɗaukar wa kanta komai rintsi komai wuya sai ta ɗau fansa.
~~~~~~~~~~~~~
Xaune yake a cikin office ɗin shi yana duba wasu muhimman takardu,kiran hajia ya shigo wayar shi,da sauri ya ɗauka haɗe da tattara dukkan hankalin shi,cikin girmamawa da biyayya yai mata sallama.
“Wa’alaikum salam”
“Hajia ya gidan ya Sabreen?
“Muna lafiya
“Ya jikin na ta?
“Jiki yayi sauki,ina son muyi wata muhimmiyar magana da kai idan ka tashi ka biyo”
“To shikenan zan biyo insha allah!
“Yawwa allah ya kawo ka lafiya
“Amin.
ita ta fara katse wayar.
~~~~~~~~~~~~~
Cikin sigar jan hankali take mishi magana”Dear meyasa kake min haka ne,kasan irin son da kishin da nake maka kuwa,kasan yadda naji da ka katsi min waya kuwa”
Kamar wanda ke koyan magana ya ce”Haba haulat meyasa kike da zargi ne,na kaya miki wata ƙan wata ce ta ɗau wayar ,kuma bata iya amfani da wayar ba shiyasa ta katse”