NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“To bata iya amfani da waya ba kuma”
“yes village girl ce ya fada had’e da ta’be baki.
“me ya haɗa ka da wata village girl kuma? ba wanan ba yaushe zaka zo?
numshe idanuwan shi yayi ,yana son zuwa gurinta tunda yana sonta,amma yana jin tsoran abin..
“Wai meyasa kake gudu na ne,ta katse mishi tunani.
“Ba gudunki nake yi ba dear ,ina son na yiwa zuciya faɗa ne”
Ɗan guntun tsaki ta ja”Kana ɗai gudu na kamar wata maiya anya kana sona kuwa”
“ina sonki Haulat”
Saida tsigar jikinta ya tashi dan yadda yayi maganar gaba ɗaya feeling ɗinta ya tashi.
Cikin sigar da tasan zata ja hankalin shi ta ce”prove it!
katse wayar yayi dan ya tabbata idan ta cigaba da mishi magana a haka ba zai kai labari ba,kashe wayar yayi ma, dan yasan zai ta kara kira tunda maiyace anace????.
~~~~~~~~~~~~~
Gaba daya ya rasa natsuwar shi tunda sukai magana da hajia, ƙarfe da ƙyar ya tsaya yayi salar maqrib a office ɗin,cikin gaggawa da hanzari ya iso gidan su hajiyar.
Suna zaune a falo ƴar aljanna tana kan cinyar hajia kamar yadda ta saba indai suna tare da ita to a kan cinyarta take kwanciya.
“Assalamu alaikum”
Sabreen tana jin sallamar shi ta miƙe
Hajia ta amsa mishi sallamar,yana ƙarasowa yayi gurin Sabreen ɗin fuska ɗauke da Annuri ko wani irin yanayi yake ciki idan yaga Savreen zai yaji farinciki.
“Sabreen ya jikin ki”
kanta a ƙasa ta ce”yayi sauƙi Dady”
“Alhmdllh! allah ya ƙara miki lafiya Sabreen”
Hajia ta katse shi da faɗin”ƴar aljanna je ki ɗaki”
“to kawai ta faɗa ,ta tashi ta hau sama ,duk da tasan dady ba zai ƙi amincewa ba amma saida ta tsinci kanta da faɗuwar gaba wanda ta rasa dalilin yin shi.
Bayan sun ƙara gaisawa ta kalle ta ce”Alhaji kana jina koh?
“Eh ina jinki hajiya”
“Yawwa to,tun lokacin da likita ya ce ayi wa Sabreen aure na shiga tunani da wa za’a haɗa ta,tun a lokacin Naufal ya faɗomin a rai ,domin bana son mu ba wani wanda bamu sanshi ba,kar ya cutar da marainiyar allah,amma zai ban nufe ka da maganar ba,kuma kai ma nasan kayi irin nawa tunanin ,duk ba mu san muyi mata dole shiyasa ba muyi wa juna maganar ba”
“Wanan haka ne hajia kuma ɗazun malamin makarantar su ya kira ni ya shawurce ni akan muyi mata aure”
“To alhmdllh! Allah yaga zuciyar mu ya ga kuma tsoran mu,yau tana dawo wa daga makaranta da tabbatar min da tana son Naufal”
Wani irin farinciki ya mamaye alhaji”masha allah alhmdllh,hajia allah ya dube mu,daman muna tunanin ko ba zata so shi ba,amma abin allah gashi tana son shi,ba ƙaramin daɗi naji ba,cikin gaggawa kuwa za’a ɗaura auran nan”
“Yawwa ni kaina naji daɗi mara misaltuwa,yanzu zai a tsaida ranar auren.
“To kwana nawa kike ganin ya kamata a saka”
“To bari mu sai gobe idan munyi magana da ita”
Hmm tofah ana wata ga wata,ko ya naufal xaiji idan yaji maganar auren shi da Sabreen,ga kuma mutumiya haulat.
Bayan ya tafi hajia ta shiga gurin Sabreen ɗin ,a kwance ta ganta tayi lamo kamar me barci,tana jin an buɗe kofa ta tashi zaune,kusa da ita ta zo ta zauna.
“Ƴar aljanna bana son ganin ki kina damuwa Naufal ya zama naki,yaushe kika so a ɗaura muku auren?
Dumm dumm zuciyarta ta fara buguwa wani irin abu zuciyarta ke bijiro mata da shi me kama da tsoro,amma dan tsabar ƙarfin hali irin na Sabreen ta ce”Sati ɗaya,A’a kwana huɗu ranar juma’a kenan,sati ɗayan ya mata yawa.
“To baki da matsala yanzu ai a fara shiru”
“Hajita ina son a tsara bikin nan sosai irin na ƴaƴan gata”
“ke ƴa gata ce Sabreen karki ji komai ko da ɗukiyar alhaji zata ƙare akan yasa ki farinciki zai kashe,za’a haɗa biki irin wanda sai ƴaƴen manya ƴan gata”
Wani irin farinciki ya mamaye Sabreen ,amma a ƙasan zuciyarta tana jin wani iri.
~~~~~~~~~~~~~
Ko da dady ya koma gida suna zaune a falo suna fira.
duk da sun san dady da fara’a amma yau kuwa sunyi mamakin ganin irin fara’ar da ke fuskarshi kamar wanda akai wa bushara da aljanna,zama yayi suka yi fara sosai sai ƙarfe goman tare kowa ya tafi ɗakin shi.
“alhaji wai yau naga kana cikin wani irin farincike ne”
murmushi yai mata sanan ya ce” hmm wani irin abu ne kike ganin zai sani irin wanan farincikin”
“eh to abu ɗaya ne zuwa biyu na farko dai magana akan Savreen na san ko…
da sauri ya katse takYawa uwar gida,ma tso kusa na baki labari”
Ba mutsu ta matso”to ina jikin ka
Saida yai gyaran murya ya kara natsuwa sanan ya ce”Kin san lokacin da likita ya ce ayi wa Savreen aure hankali na ya tashi akan da wa zana haɗa ta wanda sai riƙe ta da amana yaji tausayin maraicinta”
“Haka ne ni kai na abin yana damu na domin Sabreen abin tausayi ce”
“To allah ya ga zuciyar mu,ita da kanta ta ce tana son Naufal kinga faɗuwa ta zu daidai da zama,yanzun mun kama magana da hajia daman ba wanda ta cancanta da ya aure sabreen sai shi,kuma cikin satin nan za’a ɗaura auren nan”
Ba ƙaramin daɗi momy taji ba,dan tana son Sabreen tana jin tausayinta,amma abin da ya ɗaure mata kai daya ce wai Sabreen ta ce tana sonshi,a iya ganinta basu shiri dan ra’ayin su bai zo ɗaya ba.
“To Naufal yana sonta kuwa?
“Tunanin me kike yi?
Murmushi tayi ta ce”Naji daɗi sosai da sosai amma shi Naufal ɗin ka ji ta baki….
Da sauri ya katse ta da faɗin”Ba buƙatar jin tashi Sabreen ƴae uwarshi ce dole ya sota yana ma sonta,idan jar jinin jiki na ke yawo a jikin shi,to na Sabreen ma yana yawo a jikin shi,kuma idan har yana so na to yana son Sabreen,kuma kar yaji wanan maganar sai ranar da za’a ɗaura aurank
Ganin rance ya fara ɓace yasa tai saurin tarar shi cikin sigar lallashi ta ce”Ba wai ina nufin wani abu ba ne,ina nufin ya kamata ace ya san da maganar ne…
“To idan bai sani ba ,wani abun zai yi?
Shiru tayi dan taga alamar ya hau sama,tashi tayi ta fita a ɗakin….
lallai Sabreen saboda ɗaukar fansa zaki aure wanda baya sonki baki son shi.
.
Sir Dboy
[12/9, 1:13 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/16, 5:46 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
………………………………………
_*YAWAITA SALATI GA ANNABI S.A.W ARANAR JUMA’A*_
➖➖➖➖➖➖➖➖
_*Annabi s.a.w* yana cewa: (Yana cikin mafificiyar Ranakunku Ranar Juma’a, dan haka ku yawaita yin Salati agareni acikinta, domin ana bujuromin da salatinku gareni)._
_*@Saheehu Abu Dauda.*_
_*Annabi s.a.w* yace: (Duk wanda yayi salati a gareni, *Allah* zaiyi masa salati Guda Goma)._
_*@Saheehul Jami’i*_
Page 7
___________
Kallon Sabreen ɗin yake yi cikin mamaki,ya ƙasa yarda da abinda aka gaya mishi dan yanayin ta ba irin na matan nan ba ne,ga kuma hawayen da yaga tana yi.
“Dan Allah kayi hakuri karka kore ni,bamu taɓa yi ba sai yau.
Kamar wata wawiya ta juyo ta kalli shi,tana hawaye.
Shi kanshi principal ɗin kan shi ya ɗaure ganin yadda sani nani yake magana,gashi ita ta kasa cewa komai.
“Daman ba tun yau ba nasha ganin ta tana zuwa toilet ɗin maza” cewar wani mai aikin makarantar.
Kallon shi cikin mamaki da tsoro Sabreen tayi, duk bakin Sabreen yau naiman shi tayi ta rasa.
“A hukunta su daidai laifin da ta aikata” cewar uncle ɗin maths ɗin su wanda shi ma yana cikin office ɗin.
Kallon su kawai Sabreen ke yi tana zubarda zafafan hawaye zuciyarta na ƙuna.