HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Saida yaja numfashi sannan ya ce” ku bani guri zanyi magana da ita”

Basu su hakan ba musamman sani nani shi da yaso jin hukunci da wulaƙancin da za’a mata,amma haka nan suka fita.

Kallonta yayi cikin jin tausayi ya ce”Sabreen mai ya faru?

Sai yanzu kuka mai sauti ya kamata,kuka mai tsuma zuciya ta fara wanda tunda ta zo duniya bata taɓa yin irin shi ba.

“Kiyi magana ganin ba zata yi ba yasa ya ce mata” to ya isa hakan.

A zuciyarshi y ce” kukan ki ya tabbatar min da baki aikata komai ba,amma dole zan yi hukunci dan dukace amma tabbas zan rufa miki asiri ba zan tuzarta ki ba”

Wata ƙararrawa ya danna alamar su shigo,cikin zuguɗin abinda zai faɗa suka shigo.

Kallon su yayi ya ce “Kamar yadda duka ta tanadar za’a gayama iyayenta sannan a koreta daga makaranta,amma ba zan koreta ba,zan dai gayama iyayenta sanan bana son jin wata ƙaramar magana na,kai sani ya kalle shi

“Kai ne abin ji wallahi idan har iyayenta suka ji wanan labarin ka bani,baka san matsayin su ba ne,balle ta tabbatar mu da ƙarya kake mata,ba kai ba har makarantar gaba ɗayanta ka ja mata kalle ta ya nuna Sabreen ɗin wacce dan tsabar kuka jikinta ya mutu yayi tiɓiss.
Sanan ya ɗaura da faɗin”Hm kai kasan komai,ni bani da abinda zan ce a cikin ku waye ma gaskiya ,amma abu ɗaya tabbas idan har iyayenta suka ji kai ne mara gaskiya dan sai sun hukunta ka.

Jikin sani yayi sanyi tabbas yasan bashi da gaskiya ko kaɗan.

Kallon shi principal ɗin yayi yaga yadda jikin shi ya mutu sanan ya ce”Hmm zaka iya taimakon kanka ta hanyar ƙin gayama kuwa dan wllh idan ka yarda iyayenta suka ji wanan mgnr ka kaɗe”

Kallon sauran malaman yayi ya ce musu”Ku kuma nasan kun waye mahaifinta kuma kun san abinda zai iya to wllh ku rufama makarantar nan asiri domin idan ba haka ba,kun san abinda zai biyo baya,kuma wllh duk idan naji wani yayi kokarin gayan wata magana a bakina aikin shi”

Gaba ɗayan su jikin su yayi sanyi dan sun san mai taƙama,musamman sani.

“Kuma abinda yasa ba zan koreta ba ,dan gudun kar ayi zargin wani abu,ina fatam kunji abinda na gaya muku da kyau”

“Eh munji suka faɗa a tare sanan kowa ya gama gaban shi.

Har suka gama magana suka fita Sabreen na kuka.

“Sabreen na san ƙarya ya miki,yana da wata manufarshi na yin haka,shiyasa ba zan matsa sai ya gaya ba domin idan nayi hakan wasu zasu ji daɗi,shiyasa na rufe musu baki,sanan ke kuma kiyi hakuri tunda kin san baki aikata komai ba,plsss Sabreen kiyi hakuri kuma karki gaya ma kuwa abinda ya faru harda gidan..

Sai yanzu Sabreen ta samu bakin magana cikin shekar kuka ta ce”Ban…s..san..abin..da..suk…ke..magana…b…n rantse da girman allah bansan…

“Ya isa haka ya ƙatse ta,na sani shiyasa na ce ki kwantar da hankalin ki,idan kika nuna danuwa waɗan da suke son ganin kin tuzarta daɗi zasu ji”

Allah sarki Sabreen baiwar allah ko kaɗan bata kawo Haulat a ranta ba,bata ma yarda wani zai iya mata hakan ba dan yasa ta wulaƙanta tabar shi a matsayin an samu kuskure.

Ya daɗe yana lallashin ta,har lokacin an kusa tashi ma,sanan yasa ta shi toilet ɗin office ɗin ta wanke fuskarta,ta wuce classa
ɗin su.

Number Alhaji ya fara naimo wa cikin sa’a kuwa ya ganta ya danna kira,ringin ɗaya tayi ya ɗauka.

“Assalamu alaikum Alhajn ya faɗa.

“wa’alaikum sallam Alhaji ya gida ya kokari ya iyalai.

“Alhamdulilah komai lafiya

“Mash allah! Alhaji daman ina son yin wata magana ne akan Sabreen”

yana jin ya kira sunanta ya natsu ya tattara dukkan hankalin shi”ina jinka lafiya take dai ko”

“Lafiya qalau take daman shawarace zan baka da wasu malaman suka lura suna ganin ya kamata ayi wa Sabreen Aure”

Zaida Alhaji yayi jim kaɗan shi ma bai kawo komai a ranshi ba dan likita daman ya gaya musu suyi mata aure.

“Ba komai insha allah daman nasan da zancen auren ina wani shiri ne dan Sabreen bata kula maza ni kuma bana son yi mata dole”

Ba wani fahimtar maganar yayi ba ya ce”to haka ne kam za’a mata dole ba”

A haka suyi sallama.

Ita kuwa Haulat ta kasa kunne taji labari ya fara yawo amma shiru bata ji komai ba gashi bata ga sani ba,gashi har an tashi gida.

Duk wanda yasan Sabreen idan ya ganta yau sai ya gane chanji ƙarara dan fuskarta a ko yaushe ɗauke da annuri amma yau kuwa ba annuri ba alamar shi sai ma yanayin ƙunci da ya baiya na a fuskar.

Tana tsaye tana jiran direba,kanta a kasa idanuwanta cike da hawaye dan ba abinda ya taba ɓata mata rai a duniya irin wanan abun taji zafi kamar me.

????lallai akwai aiki kuna ganin idan Sabreen ta gane aikin haulat ne zata iya hakura?

Cikin salon yanga da iyayi da kinibibi Haulat ta fito daga office ɗinta,hango Sabreen da tayi yasa tayi murmushin mugunta musamman da ta hango yanayin da take ciki.

Sabreen bata san Haulat ta matso kusa da ita ba sai ji tayi ta ce”My illiterated student! yadai

Ƙasa ce mata komai tayi dan bata cikin yanayin.

Ganin hakan yasa Haulat murmushi tana ganin kamar tayi nasara ta ce”Tun kafin a baiyana abinda kuka aikata har kin shiga wani irin hali.

Cikin rashin fahimta Sabreen ta kalleta.

Murmushin mugunta Haulat tayi ya ce”Yess! baki kina tunanin zaki iya ja Haulat ba har kika sa aka bani suspension,to bari ki ji ni na haɗa komai na biya sani,ke ba kin sa an bani suspension ba,ni kuma zan sa a wulaƙanta ki ,ki tozarta ki kunyata kuma a koreki a makarantar sanan a gaya ma iyayenki abinda kika aikata, daman baki son karutu ke jahila ce sai a haɗa ki da jahili ɗan ƙauye irinki,dan ko mai washe bola ba zai iya auren ki ba”

Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara bin fuskar Sabreen zuciyarta na ƙona tana mata radaɗi.

Ganin halin da take ciki yasa Haulat farinciki cikin dariyar mugunta ta ce”Hmm ja da Haulat ba irin ki ba jahila ƴar kauye kuma yarinya,hmm karki wahalar da kwakwalwarki gurin yin tunanin zaki iya ɗaukar fansa akai na yarinya domin ni ba tsararki ba ce,tana gama faɗa wushe tabar Sabreen tsaye da zafin zuciya.

Hmm ikon allah yau Sabreen baki ya mutu????.

Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi,daidai lokacin direban ya iso ,tana ganin shi ta ruga da gudu ta buɗe motar ta shiga tana kuka.

A ruɗe yake tambayarta lafiya dan ko a mafarki bai taɓa tunanin akwai abinda zai sa Sabreen irin wanan kukan ba.

Suna isa gidan ta buɗe motar ta fito da gudu a falo ta hango hajia zaune gurinta tayi ta faɗa kan jikinta tana kuka,a ruɗe Hajiar ke tambayarta”Lafiya Sabreen ke da waye???????

A ranta ta ce” *NI* *DA* *MALAMA* *TA*.

Tsananin kuka ya hanata magana.
Hajiya ta ruɗe tana faɗin”Na shiga ukku ke dawa me ya faru wa ya taɓa ki,ko baki da lafiya ne????

charab ta ce”Bani da lafiya

Ai hajia sai ta ƙara ruɗewa ta ma rasa abinda zata yi,ganin hakan yasa Sabreen,faɗin “zan kwanta ki kaini ɗaki na”

A ruɗe hajiar ta tallabo ta suka hau sama,suna shiga ɗakin Sabreen ta kwanta hajiar har ta rufe ta.

Amma Sabreen bata
daina kuka ba tuno kalaman malama Haulat take yi,tana jin zafi a zuciyarta.

Ganin hankalin hajia tana ƙara tashi yasa ta daina kukan ta fara yin na zuciya,tayi lamo kamar tayi barci,tana jin hajia tana ta maganganu,A haka har barcin ya ɗauke ta.

~~~~~~~~~~~~~

A hankali ta fara jin muryar hajia da na Momy da na farrah,bata ji muryar shi ba amma ƙamshin shi ya tabbatar mata yana nan,a hankali ta fara kokarin fuɗe ido domin taga a inda ta ke.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button