HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Akan hajia idonta ya saura dakin da mutanan da ke ciki ta fara ƙarewa kallo,ɗakinta ne,chan daga bayan su akan kujerarta ta hango shi fuskar nan kamar kullum a yatsine.

Sannu suka mata ɗaga musu kawai kawai take yi.

Momy ta kalle shi ta ce”Naufal baka ga ta farka ba”

Bai ce mata komai ba ya ƙaraso gurin tana ganin shi da juya kanta.

Taɓe baki yayi ya ce”Ya jikin?

Ɗaga mishi kai kawai tayi,bai damu ba,ya koma ya zauna ta gefan ido yake satar kallon ɗakin ,ɗakin ya mishi kyau ga wani irin ƙamshi irin wanda yake ji a jikinta,ya shagala gurin satar kallon ɗakin.

Momy kalleta ta ce”Ƴar aljanna bari mu barki ki samu ki watsa ruwa”

Bata ce bata komai ba suka tashi suka fita yana jin hakan ya riga su tashi,kash saidai ya manta da wayarshi a hannun kujerar da ya tashi a kai.

Hajia ta kalleta ta ce”Zaki iya wankan”

Murmushi tayi ta ce a hankali “zan iya”

“To ki kula kinji”

Kai kawai ta ɗaga mata,hajiar ta fita.

Tana ganin sun fita ta sauko daga kan gadon ,ta cire kayan makarantar ta ɗaura towel,har zata shiga bayi ringin ɗin waya taji kalle-kalle ta farayi charab idanta ya sauka akan wayar Naufal ɗin wacce ya manta da ita a ɗakin.

Ƙarasa gurin tayi tana faɗin”Garin ya ya manta da wayarshi a ɗaki na?

Tana kai hannu ta ɗau wayar ,tsaro idanu tayi tana ƙara tabbatar a abinda idanuwanta suka ga ni.

“Malama Haulat! ta faɗa ita ɗince pic ɗinta ne ya baiyana a gaban wayar har kiran ya katse Sabreen bata sani ba ,dan mamaki ƙara shigowar ringin ɗin ne ya dawo da ita daga duniyar mamakin abinda ba abin mamaki ba ne.

Katse wayarta”Malam haulat ita ce kenan”

Wani kiran ya ƙara shigowa a fusace ta ƙara katse kiran.

“Ya Naufal ne wanda keke mugun so daman”

Jin tafiyar mutum yasa tai sauri ta ajiya wayar ta faɗa toilet ɗin da sauri.

Farrah ce ta shigo ɗakin ta ɗauki wayar daya aikota ta ɗauko mishi.

“Sabreen zamu tafi amma anjima zamu dawo momy tayi baki”farrah ta gaya tana kallon toilet ɗin,bata tsaya jiran amsar Sabreen ɗin ba ta fita daga ɗakin dauke da wayar a hannunta.

“Malma Haulat”

Ta faɗa tana tuno kalaman da ta gaya mata.

kamar wace abu ya tsikara tayi zumbur ta mike ta ɗaura towel ɗin ta fito,tana fitowa hajia na shigowa,tana ganin hajiar ta fashe da kuka mai tsanani ta faɗa kan gadon.

A kiɗime hajia ke tambayarta”Lafiya Sabreen ki gayamin abinda ke damunki ko meye shi zan miki magananin shi”

Cikin kukan ta ɗago kai ta kalle hajia ta ce”Ya Naufal na ke so,kuma ya Aure ni”

Ba hajia ba ni kaina saida taji wani yarr

“Naufal kike son aura

“Eh kuma a wanan satin” Tana faɗa ta ƙara fashewa da kuka.

Cikin sigar lallashi hajiar ta ce”Kiyi hakuri indai Naufal ne ya zama naki ke kaɗai kuma ko gobe kike so za’a ɗaura muku aure!

tirƙashi!!!

???????? waiyo me kike shirin aikatawa Sabreen duk ɗaukar fansar ne!!
.
Dboy
[12/16, 5:46 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????[12/16, 5:35 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

بسم الله الرحمن الرحيم

_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{KAYI ALKHAIRI, KUMA KA BAR LAIFUKA. ALLAAH ZAI MAYAR DA LAIFUKAN KA(NA BAYA) BAKI ‘DAYA SU ZAMA ALKHAIRI.}*_

“`[Sahihut Targib;3164]“`
~~
_Duk mutumin da Allaah Ya azurta da halin kirki ya rin’ka aika alkhairi, kuma ya guji aikata sabon Allaah, toh sai Allaah Ya mayar da laifukansa na baya ma su zama masa alkhairi. Allaahu a’alam._

“`Allah ta’ala yasa mudace“`

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

Page 8
…………………………………

Kamar yadda ya saba yin mafarkin yau ma hakan ne,
Ya kai tsawon minti ashirin yana nazari akan mafarkin wanda yanzu abun ya fara tsorata shi, dan saidai idan har bai kwanta ba, amma sai yayi mafarkin ta.

Tashi yayi ya shiga toilet ya daɗe yana watsa ma kan shi ruwa kafin ya samu yayi wankan ya fito.

Cikin jallabiya baƙa ya shirya ,ta mishi kyau ainun,ga ƙamshi da ke tashi a jikin shi saboda yawan saka turare yasa ko mai shafa ba,jikin shi yake ƙamshi.

Kallon agogon bangon dake ɗakin yayi ƙarfe tara na ranar laraba,ya mutsa fuska yayi haɗe da hura ɗan ƙaramin hancin shi,wayar shi ya ɗauko ya kunna,yana kunnawa saƙonnin Haulat suka fara shigowa,shefar da wayar yayi haɗe da jan tsaki.

Gaban shi yai mummunan faɗuwa jin ringin ɗin kiran Dady da sauri ya ɗauka murya a harɗe ya ce”Assalamu alaikum”

Cikin jin daɗi da annashuwa Dadyn ya ce”Wa’alaikum salaman”

“ina kwana dady

“Lafiya lau Naufal baka tashi ba ne?

“Na tashi dady

“To ka fito ina jiranka a falo”

“to ganin nan zuwa ,tun kafin ya rufe baki ya tashi ya fito,a ranshi yana tunanin me yasa dadyn nashi cikin farin ciki tsakanin jiya da yau,sanin ba zai iya bawa kan shi amsar ba yasa shi ya bar maganar.

A Falo ya same su,da dukkan alama suna cikin jin daɗi,shi ma aro annuri yayi yasa wa fuskar shi,xai da ya zauna sanan ya kalli momy cikin kulawa ya ce “Good morning

“Morning Naufal

Farrah ma ta ce”Ka tashi lafiya Yaya Naufal”

“Lafiya lau”

Allah sarki momy tana son Sabreen amma bata son ya aure wacce baya so,dan ƙiyayyar namiji bala’ai ne.

A tare suka yi breakfast cikin son da ƙaunar juna,bayan sun gama Dady ya kalle shi cikin kulawa ya ce mishi”Naufal tashi muje yau akwai abubuwa masu muhimmanci da xamu yi”

Cikin rashin fahimtar abinda dadyn ke nufi ya ce”To Dady A office ne?

“A’a wanan yafi aikin offfice tashi dai mu tafi”

A ranshi ya fara tunanin wani irin avu ne wanda yafi aikin su mahimmanci.

“Gidan hajia zamu fara zuwa”

“to Dady ya faɗa ba komai a ranshi.

~~~~~~~~~~~~~

Zaune take akan tanƙameman gadonta ,gaba ɗaya jiknta ya mutu sakamaƙon mafarkin da tayi Naufal ya tsare da ido yana mata wani irin kallo wanda ƙaramar kwakwalwarta ta ƙasa gane ina kallon ya dosa.

“Ina haba Sabreen tun yanzun zaki karaya,dan ɗaukar fansa zaki yi fa,bai kamata ki karaya ba” Zuciyarta ke mata wanan maganar a fili ta ce haɗe da yin murmushi “Sabreen ƴar aljanna ƴar gatan hajia,duk abinda nasa gaba sai nayi shi”

Zuciyarta ta ƙara yin ƙarfi duk wani tsoro da fargaba ya fito,Cike da izza ta tashi tai toilet fuskar nan ɗauke da annuri.

A Falo suka iske hajia ,hajia tana ganin Naufal ta sake wani irin murmushi,ta ce “Mutan India manya Har ka fara ƙamshin dogon buri”

Cikin rashin fahimtar zancen ta ya ce”Ina kwana hajia”

“Lafiya lau,yanzu fah ka ɗau hanya”

Banza yayi da ita tunda shi bawai ya iya hausa sosai ba ne,baya gane magana cikin magana,dan ma su momy suna mishi hausa da ba zai iyata sosai ba,a ranshi ya ce”To yau kuma ita ma naga tana cikin farinciki Sabreen fa?

“Sabreen meye nawa da ita,duk a zuciyar shi yake wanan maganar,ya kas….

“Naufal hau sama ka kira Sabreen”

Hajia ta katse mishi tunanin da yake yi,kallon ta yayi ta sakar mishi wani irin murmushi,kallon dadyn yayi shi ma murmushin yake yi.

Tsaye ya miƙe ya hau saman a ranshi ya faɗin”Meyasa hajia zata aike ni ɗakin ta?

Tura ƙafar yayi,lokacin ta fito daga toilet daga ita sai towel dan ƙarami iya karshi gwiwa.

Jin an buɗe kofa yasa ta juyo”Waiyo!! ta faɗa a tsora ce.

Ƙamewa yayi a tsaye zuciyar shi tana bugawa da karfin gaske kuma ya kasa sauke idanuwan shi da suka kafe akan brest ɗinta,lokaci ɗaya jikin shi ya mutu wani irin bakon yanayi ya fara ziyarta zuciyar shi,wanda ya ke tunanin yafi ƙarfin ya kira shi da sha’awa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button