HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Laaa…..fiii….y…yaa…me…y..yaaa….k.k..ka.wo..ka..”Ta faɗa a ruɗe.

Bai ma san tana magana ba,dan gaba ɗayan hankalin shi baya tare da ita.

Idanuwan shi ta kalla ai sai ta ƙara ruɗewa ganin yadda suka chanja kala,gashi ta ga nonowan ta ya zubawa ido,A ruɗe ta faɗa kan gadon ta ƙudundune da bargo tana ihu.

Ringin ɗin wayar shi ne yai nasarar dawo da shi haiyacin shi,lumshe idon shi yayi waɗan da suka rine.

Da ƙyar ya iya sarrafa hannun shi gurin lalubo wayar da ke ringin ɗin,ringin ɗin kiran Haulat daban ne amma saboda tsananin shiga wani irin yanayi bai iya tantance ringin ɗin ba.

ya san ko ya ɗauka ba zai iya magana ba ,yasa ya kasa ɗaukan,ga shi kafafuwan sun mishi nauyin da zai iya saukar da kan shi ƙasa.

Hawaye ne taji sun fara bin fuskarta a hankali ta ce “daman ɗan iska ne! kuma zan aure shi”

Tuno irin yadda taga ya kafe nonowanta da ido tayi haba sai hawaye shaaa kamar an kunna famfo.

Ko kaɗan su hajia basu kawo komai a ransu ba ,daman tayi hakan ne dan suyi magana ita da dadyn.

Jin sheƙar kukanta yasa shi ya ƙasa shigowa ɗakin “Keee ya daka mata tsawa,uwar me kike yiwa kuka,wani abu ne ya faru banza kawai kiran ki aka ce na zo nayi”

Yana gama faɗa ya fita a fusace ranshi a ɓace,kan me zata yi kuka wani abu yayi mata,ji ƙarfin hali irin na Naufal ko tabarmar kunya dai zai naɗe.

Ai wani sabon kukan Sabreen ta ƙara fashe wa da shi,abinda ya ɓata mata rai tsawar daya ɗaka mata,wacce saida tasa hanjin cikin ta yin kuka,dan tsoro,kuma meye nashi idan tayi kukan,ba shi ne yaja ba”

“Ko me zaka min ba zan fasa aurenka ba,kuma na baka bashin tsawar da ka dakamin amma bazan yafe ba”

Ita kaɗai tai tai maganganun ta,tana kuka.

baƙin glass yasa kafin ya sauko kasan,yana isa hajia ta ce mishi

“Tana ina?

“Gata nan zuwa”ya faɗa cikin wata irin murya,fita yayi daga falon yaji daɗi da dadyn bai hanashi ba ,yaɗai ce mishi ya jira shi a motor

A motor ya zauna ya jingina kai da sitiyarin motor zuciyar shi tana bugawa,kamar wanda bai taɓa ganin makamancin haka ba,yasha ganin mace tsirara amm bai taɓa jin irin na yau ba,ko Haulat tasha ɗaukar hoto da towel a jiknta ta turomishi,amma yau sai yaji wani irin abu wanda ya kasa ganewa.

“Mtseewww me yakai ido na jikin wanan wawiyar yarinyar yanzu zata raina ni,dan taga irin kallon da na mata mtseww”

Ya faɗa cike da jin haushin zuciyarshi da idanuwan shi.

Hajia da dadyn sun gama magana akan ranar juma’a za’a ɗaura aure,hamshaƙin aure irin na ƴaƴan gata,Sanan sunyi magana akan gidan da zasu zauna da komai da komai,sanan dady ya bata maƙudan ƙuɗi dan yin wasu abubuwan,sanan ya tashi a falo ya tarar da shi.

“Ya Aka yi ne Naufal”

“Ba komai dady ya aro murmushi ya ɗaurawa fuskar shi”

Hoto nan gidaje Dady ya nuna mishi “Wanne yafi kyau Naufal”

Gaba ɗayan gidjen sun haɗu kamar ba’a 9j ba,saida ya tsaba wani madaidaici mai ɗankaran kyau sanan ya nunawa Dady ya ce”Waw dady wanan yafi kyau”

Murmushi yayi sanan ya ce”Sabreen zata so shi ko”

“Sabreen me ya kawo maganar Sabreen a nan kuma?ya tambayi kan shi a zuciya murmushi yayi tuno komai za’ayi sai idan yayi mata sanan ake yi.

“Eh dady zai mata kyau ai yana da kyau”

hhhhh Shiyasa baka da masoya Naufal dan baka gane komai????.

Murmushi dadyn yayi “Yawwa.

********
Ganin ta daɗe bata fito ba yasa Hajia ta shiga ɗakin ganin ta a kwance yasa hajiar ta ruɗe”Ƴar aljnna lafiya? ta ƙarasa gurinta da sauri.

Tana jin hajia ta ƙara duƙunƙunewa kamar me barci.

“Ƴar aljanna buɗe mana lafiya”

Cikin irin muryar barci ta ce”Barci nake ji hajia ki barni nayi”

Cikin nuna kulawa ta ce”Kin tabbata barci kike ji”

“uhm.. ta fara kukan shagwaba ta ce”Barci hajia ki barni”

“To ya isa haka,ta faɗa ta tashi ta fita.

*******

Kallon farrah momy tayi ta ce”farrah Naufal zai aure Sabreen cikin satin nan”

“What? ta faɗa haɗe da zaro idon.

“Taya momy Ya Naufal ɗin?

“Hmm nima saida naji wani iri anya kina ganin ba za’a zamu matsala ba kuwa”

“Tabbb gaskiya momy da kamar wuya a ƙi samun matsala dan Yaya ma yana da budurwa”

Jikin momy ya mutu “Waya gaya miki yana da budurwa farra?

“Yasan da maganar auren?

“A’a me sani ba”

“Hmm to saidai kawai muyi addu’a dan yaya dai baya son Sabreen ita ma ɗin,amma zasu dace ita ce daidai ce,idan ya fara sonta zai chanja,na kam naji daɗi bari ma taje gurinta”

Tana faɗa ta tashi jiki na rawa,ita kuwa Momy jikinta ya mutu tausayin Naufal ya mamayeta,amma ya zata yi.

Cikin zumuɗi da rawa jiki Farrah ta isa Gadan a falo ta isake hajia ta washe baki ta ce “Hajiya ashe muna da babban biki”

Ita ma hajiyar washe baki tayi “Bari dai farrah zamu sha biki ,ya hajiar ta ku”

“Tana lafiya ita ta gayamin ma,hajia ina Sabreen”

“Tana ɗakinta barci take yi,amma halan ta farka”

ai tun kafin hajiyar ta gama magana ta haye sama.

Tana isa ɗakin ta faɗa kan gadon”yeeeh Amaryar Yaya,shi ne ba za’a gayamin ba na shirya faty”

Sabreen tana jin Farrah ce ta tashi yana mutsike fuska cike da ƙarfin hali ta kalle farrah tana murmushi.

Dungurinta tayi akai tana dariya ta ce “Gayamin yaushe kika fara son mutumin naki?

Bata son ta gaymata dan kar da gayawa hajia,murmushi tayi ta ce”Tun shekaran jiya na nayi mafarkin shi”

Dariya farrah tayi sosai “Ah lallai wato mafarki wani irin mafarki?

“Ke nidai karki ishe ni,da tambayoyi kamar wata ƴar jarida,yanzu dai faty nake so a haɗa.

Ƙara farrah tayi”Yeehhh ai lallai ana son yaya Wai nifa abin mamaki yake ban Wai Sabreen ɗin d na sai ƴar aljanna ƴar gatan hajia wai ita ke son Yaya Naufal ɗan iyayi da kinibibi”

“To meye”

“A’a ba komai duk love ne,amma abin da mamaki fa”

“Ni kidaina mamaki ,ki tsaya muyi magana”

“To na tsaya Aunty Sabreen”

Doka sabreen ɗin ta kai mata”Waye Aunty?

“Sabreen amaryar yaya”

“Ke fa ai”

“Ni me? yaushe ne bikin naji ance cikin satin nan ?

“Jibi!

ƙara farrah ta buka ta haye kan Sabreen ɗin tana ihuu.

“Wai hajia farrah zata kashe ni”

ɗaga ta farrah tayi tana dariya “Lallai Sabreen tun yanzu to gaba wa zaki kira ya taimake ki?

Cikin rashin fahimta ta ce”Hajiata mana”

Dariya farrah tayi sosai ta ce “Akwai wata ƙawar momy tana gyaran jiki na amarya ya kamata momy ta kai mu gobe,abubuwan ne sun matse kamar wata wacce ta ƙagara za’a sa biki kwana ukku,haba ace mai taƙama family zasu aurar da yara biyu yaran ma ƴan gata ace ba abinda za’ayi haba,gaskiya ba zai yuwu ba yadda nake da buri akan bikin wani daga cikin ku”

Ta kai hannu ta doki cinyarta,ƙara Sabreen tayi”Ann Haba farrah ke mugu ce daman”

Dariya farrah tayi ta ce”Tab akwai aiki kuwa yaya zai wahala,to nidai gasky tashi yanzun nan mu je kasuwa,muyi siyayya ya kamata ma kuyi photo fa wanda za’a sa a memo da jaka da wanda za’ayi amfani da shi gurin faty”

Kallon farrah Sabreen tayi “to yanzu ya za’ayi”

“yawwa ina da pic ɗin yaya zai muje ki ɗauka sai a haɗa kamar kunyi tare,daga nan sai muje a haɗa mana memon da jaka”

“to bari ta saka kaya” ta faɗa tashi tayi daga kan gadon ta je gurin drower towel ɗin ya zamo.

“Waiyo ni gaskiya Sabreen yaya zai ja kaya irin wanan hips haka”

Cikin rashin fahimtar abinda Farrah ke nufi ta watsa mata harara ta ce”To yanzu ina zamu samu kuɗi?

“Dady zaki tambaya”

harararta ta ƙara “baki da hankali kawai sai na tambaye shi kuɗi.

“Ke nidai yi ki saka kaya kuɗi ba matsala ba ne hajia zata ba mu,momy ma nasan zata ba mu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button