NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Tana sa kaya suka sauko ƙasa farrah ta gayawa hajia zasu fita su fara shiri,hajia taji daɗi sosai ta basu kuɗi sosai,har zasu tafi ta ce su jera tare zata gurin Momy suyi magana.
Ko da suka isa gurin momy ,momyn tana ganin su cikin farinciki ita ma farincikin ya kamata,musamman da taga Sabreen ta tuno da maganar da dady yayi”Idan har jini na ke yawo a jikin Naufal to jinin Sabreen ma yana yawo ajikin shi zai so ta idan har yana so na”
Hankalinta ya kwanta sosai,ta saka a ranta zai so ta ne.
Ita ma ta ƙara musu kuɗi masu yawan gaske ta kuma kira idan zasu je ai mata makeup sanan a haɗa hotonsu tare,kuma a haɗa komai da komai wanda za’a saka photon,kuma ta ce zata kama tsadaddan holl wanda za’ayi fatyn,sanan suka fito,ita kanta hajia daɗi ya mamayeta ainun.
.
[12/16, 5:35 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/16, 5:36 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
*By*
*fatima* *Batula*
Page 9
………………………………………
*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_
_*ZIKIRAN DA AKEYI BAYAN IDAR DA SALLAH*_
:
.
_*(1)* -“Astagfirullahi” sau uku,(3)_
.
_*(2)*“Allahumma Antas Salam, Wa minkas Salam, Tabarakta Yaa Zal Jalal Wal Ikram”_ _*[Muslim ne ya rawaito shi].*_
:
_*(3)* -“Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli Shai’in Qadiir._
.
_*(4)* Allahumma La mani’a lima aadaita, Wala mu’udiya lima Aaxait, Wala Yanfa’u Zal Jaddi Minkal Jadd”_
_*[Bukhari ne ya rawaito shi].*_
.
_*(5)* -“Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli Shai’in Qadiir._
_La haula wala quwwata illa billahi, Laa ilaha illal Lahu, Wala Na’abudu Illa Iyyahu, Lahun ni’imatu Walahul Fadlu, Walahus sana’ul Hasan, Laa ilaha Ilal Lahu, Mukhlisina lahudden, Walau karihal Kafiruun”_
_*[Muslim ne ya rawaito shi].*_
:
_*(6)* -“Subhanallah, Wal Hamdu Lillahi, Wallahu Akbar” Sau talatin da uku.33_
:
_*(7)* “Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli Shai’in Qadiir”_
_*[Muslim ne ya rawaito shi].*_
:
_*(8)* La Ilaha Illallahu Wahdahu La Sharika Lahu Lahul- Mulku Wa Lahul-Hamdu, Yuhyi Wa Yumitu Wa Huwa ala Kulli Shai’in Qadir.._
_*sau goma(10)bayan sallar Asuba da magariba*_
:
_*(9)* -“Allahumma A’inni Ala Zikrika, Wa shukrika, Wa Husni Ibadatika”_
_*[Abu Dawud ne ya rawaito shi].*_
:
_*(10)* – Karanta ayatul Kursiyyi, da suratul Al-ikhlas, da Falaqi da Nasi *dai- dai…….1 -1*_
_*Sanna (Sau uku-uku)3-3* bayan sallar magariba da asuba_
_*[Nasa’i ne ya rawaito shi].*_
:
_*(11)* – Fadin “Allahumma Inni As’aluka Ilman Nafi’an, Wa zirqan Xayyiban, Wa amalan Mutaqabbalan”_ _*[Ibnu Majah ne ya rawaito shi]*_
_Bayan an yi sallah daga sallar asuba._
:
_An kar6o daga *Aisha – Allah ya yarda da ita* ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana bude sallah da kabbara, karatu kuma da “Alhamdu Lillahi Rabbil Aalamin”. Hakanan ya kasance idan ya yi ruku’u baya daga kansa sama, kuma baya sunkuyar da shi qasa, sai dai yana sanya shi tsakanin haka. Idan ya dago kansa daga ruku’u baya sujjada har sai ya daidaita a tsaye, hakanan idan ya dago daga sujjada baya komawa sujjada har sai ya daidaita a zaune. Ya kasance yana faxin tahiya a dukkan tsakanin raka’o’i biyu. Hakanan ya kasance yana shimfida kafarsa ta hagu, ya kafe ta dama (a zaman tahiya). Ya kasance ya hana zaman shaidan (zama akan dugadugai), yana hana mutum ya shimfida tsintsiyar hannunsa kamar yadda dabbobi suke yi. Yana qare sallah
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
………………………………………
kallon Momy Hajiya tayi ,tana murmushi ta ce”Hajiya kinji yadda muka yanke shawara ba mu tambayi ra’ayinki ba”
“Ah haba Hajiya ba komai kun isa ne,kuma shawarar tayi daidai naji daɗi sosai, ubangiji Allah ya haɗa kan su,ya basu zaman lafiya da zuri’a ɗaiyaba”
“Amin ya Allah”
“Bari nima na tashi ba’ayi biki haka ba,naje nayi siyayya na gaiyaci ƴan uwa da abokan arziƙi”
“To gaskiya kuwa abin ne yazo da sauri”
Bayan sun gama maganar su Momy ta kawo Hajia gidan ta,ita kuma ta wuce kasuwa daga nan ta tafi gidan su gurin iyayan ta.
~~~~~~~~~~~~~
Tun Safiyar ranar da Haulat ta tashi take jin ɓacin rai duk saboda Wayar Naufal a kashe tun jiya da ya kashe bai kunna ba, da safen ma ta kira bai shiga ba,ranta ya ɓaci haka nan ta tafi makaranta ranar student sun sha zagi da bala’i ,ganin bata ga Sabreen ba yasa ta ɗan ji daɗi,amma bata ji labarin wani abu ba,akan sharrin da ta haɗa mata ba.
Tun a makarantar ta kira shi yafi sau biyar amma yaƙi ɗauka a lokacin suna tare da dady.
Haka ta dawo gida jikinta ya mutu.
“Haulat wai ke ba zaki ragewa kanki wanan irin mugun son da kika ma wanan mutumin ba”
Saida ta ɗago tai mata wani irin kallo sanan ta ce”Ni ban san meyasa yaƙi ɗaukar wayata ba tun ɗazun nake kiran shi,ko yana fushi da ni ne”
“Fushen me?
saida taja guntun tsaki sanan ta ce”Shi wani iri ne kamar bai waye ba,ni na ɗauka ma baya sha’awa ne”
“Kamar ya kika ce a india yayi karatu”
“A nan ne ,amma karki ga yadda gudu na,idan kika ga yamin kiss to ba ƙaramar sha’awa yake ji ba,ni haushi nake ji ”
“Kai Haulat,yanzu ke da zaki yi alfahari da hakan,kana gani dai kowa burinshi ya taɓaka,amma har ki samu wanda ba jikin ki yake so ba,amma kina wata magana,kin san komai haulat a…..
tun kafin ta ƙarasa maganar ta katse ta”ke allah dan baki ganshi ba ne,amma ina tabbatar miki duk macen da ta ganshi sai taso wani abu ya haɗa su..
“Haulat sha’awarshi kike yi ko sonshi?
“Duka biyu”
“Hm Haulat kenan ni yanzu ƙawarki ce dole na baki sha’awa”
“Yawwa ƙawar Arziƙi mu je ɗaki na”
Ashe duk wanan maganar da suke yi a falo ne.to allah ya kyauta.
Zama suka yi akan gado salma ƙawar Haulat ɗin ta kalle ta tace”Irin waɗan nan mazan a hankali da dubara ake binsu,tunda ya nuna yana jin tsoran wani abu ya faru,to karki matsa mishi ,idan ba haka ba kuwa zai fara ja da baya,hankali xaki haɗa mishi tarko daya faɗa shikenan”
Dariya Haulat ɗin tayi suka taɓa” shegiya ƙawa shiyasa nake sonki,yanzu ba wanan baki na kira faisal(tsohon saurayinta) dan a matse nake,yaushe rabo na,nayi ma ƙokari”
“Ke Haulat baki da dama,ni kuwa kinga tun lokacin da na rabu musa(saurayinta)ban ƙara saduwa da wani ba,saidai ƴan abun da ba’a rasa ba,yawwa ban tambayeki amma zai aureki dai ko”
Kallonta Haulat ɗin tayi tai dariya”Aure ni da aure yanzu ina,allah ya kyauta haka kawai na haihu na tsofa,ke ma kin san bani da ra’ayin aure yanzu,shi dai tunda bai waye ba,daya min maganar auren nake katse shi”
Shiru Salma tayi tana mamaki ina da ita ta samu irin wanan damar”Haulat ni kin ban tsoro na ɗauka kin cire wa kanki wanan ra’ayin banzan,Ina jiye miki abun da zai iya biyo baya”
“mtseww na me? ba abinda zai faru”
“hm murmushi tayi kawai suka cigaba da firar su mara amfani.
~~~~~~~~~~~~~
Saida nayi da ƙyar na iya gane Sabreen ban taɓa tunanin tana kyau irin haka ba sai yau,nayi fitinan kyau,makeup ɗin ya amshi fuskarta ainun,cikin wata dugowar riga wacce ta ɗan kama ta,pink da golden colour kalan ya ƙara fito da ita ga ɗaurin ɗan kwalin ,ita kanta rigar abun kallo ce,bayan an gama yin makeup ɗin aka ɗauke ta hoto na,kala-kala,idan ba ita ta gayama ba son auran take yiba,ba zaka taɓa yadda ba,dan yadda ta saki jiki tana zabga fara’a.