HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Kallon ta farrah tayi tana washe baki”Da yaya ya ganki na tabbata bazai gane ki ba,ko yanzu sai yayi da ƙyar zai iya gane ki balle an haɗa pic ɗin ku”

Murmushi Sabreen tayi bata ce komai ba,ita yanzu yarda zata haɗu da malama Haulat take yi gashi bata da number ta.

Sunyi yawo sosai da n farrah saida ta je gurin ƙawayanta,ta gaya musu,Da aka haɗa hoton abun ba magana kamar a tare suka yi hoton sun dace sosai ita kanta Sabreen da taga pic ɗin saida taji gabanta ya faɗa da ƙarfi wanda bata san dalilin faɗuwar shi ba.

Gidan su momy suka sauka bayan sun dawo ita ma lokacin bata daɗe da dawowa ba,taji daɗi sosai musamman da taga an haɗa hoton sai ta ƙara tabbatar da sun dace da juna,ita ma nayi siyayya sosai da kayan da zasu saka da komai da komai.

Ana idar da Sallar maqrib Su dady suka dawo,a lokacin suna zaune a falo suna fira akan bikin,Da sallama suka shigo,Sabreen tana jin muryarshi gabanta yai mummunan faɗuwa.

Ko kaɗan bai kula da Sabreen tana nan ba,dan shi ba mutum ba ne mai kalle-kalle ba,har suka iso falon suka zauna bai kula da ita ba.

Dady ya kula da ita tun isowar shi ɗakin yana zama ya kirata”Ƴar aljanna zo nan”

Jin dady ya kira sunanta yasa ya ɗago kai da sauri haɗa ido sukai wani abu ji ya soki ƙirjin shi,da sauri da kau da idonta,a harɗe ta ƙaraso gurin dadyn kanta a ƙasa ,hannu ta Dady ya riƙo yana murmushi ya ce”Ƴar aljanna ya kike”

Kamar me tsoron magana ta ce” lafiya qalau”

“Momyn ku ta gayamin kun fita ke da farrah ,kunyi siyayya,kuɗin sun isa ko kuna buƙatar wasu?

“Am..dam..sun is..

Charab farrah ta ce”Eh dady ba mu gama ba,kuma sai maganar holl ɗin da za’ayi…

“Eh baku da matsala da wanan zanyi komai ni da yayan duk mun shirya komai”

Ko kaɗan Naufal bai gane ba,mamaki yake yi,wani abu xa’ayi..

Bai ƙarasa yin tunanin shi ba Wayar Momy ta fara ringin duk hankalin su ya koma gurin ta.

Ganin mai kiran yasa momy tayi murmushi ta kalli Dady shi ma murmushin yayi,ɗaukar wayar tayi.

“Assalamu alaikum,Haba hajia tun kafin Ayi Auran zaku rike min ita ,yanzu idan aka yi auran shikenan”

“A’a hajia ba haka bane,kin san basu dawo da wuri ba ne,kuma…

“To naji yanzu dai ku turomin ita”

Tana gama faɗa ta kashe wayar.

Dady ya kalle ta yana murmushi ya ce”hajia ku”

ya juyo ya kalli Naufal ya ce”Naufal kai Sabreen gida”

“Toh”
Kawai ya faɗa Amma ranshi a ɓace baya son raini Sabreen kuwa ƴar raini ce,bai tsaya jiran wani abu ba ya fito daga falon yana hura hanci.

Momy ta ce “zo nan Sabreen”

A kunya ce ta isa gurinta,zaunar da ita momyn tayi kusa da ita “Sabreen ki kwantar da hankalin ki kinji,gobe da sassafe zan zo ni da Farrah mu fita,ki tashi da wuri dan da safe zamu zo”

“To momy”

“A’a ya zaki ce ta tashi da wuri”

Murmushi momy tayi ta kalle shi ta ce” hmm tafi abinki Sabreen yana jira ki gaida hajia”

“To saida safen ku”

“Yawwa ki tashi lafiya suka faɗa a tare.

A hankali take tafiyar har ta isa gurin motar shi,gaban motar ta buɗe ta shiga,bata ce mishi komai ba.

“Mtseww! ya ja tsaki Sabreen ta tsani tsaki a rayuwarta,bata san lokacin da ita mata ta ja tsakin ba.

A fusace ya ɗago kai,hannun shi yakai kan lips ɗinta masu taushin gaske ya tsungule su da kunbar shi,ƙara tayi da ƙarfi ta ce “Waiyo hajia”

“Wa kike wa tsaki ni tsaranki ne,hajia ko kirata ta zo”

Jin xafi yasa ta cije shi a hannu ,yaji zafi ya cire hannun shi da sauri.

Kallonta yayi ya kalli hannun shi inda ta cije shi ɗin,bai ce mata komai ba yaja motar suka fita daga cikin gidan su,sai da ya raba tafiyar tsakanin gidan su da gidan su hajiar sanan ya tsaida motar,ganin ya tsaida motor yasa ta ce”Me muka tsaya yi a nan ,ni ka kaini gida”

“Ke ba kin raina ni ba,ni kike so ki maida direba ko,janyo ta yayi jikin shi,ya rungumeta wani irin abu yaji yarr tsigar jikin shi ta tashe wani irin shuƙi ya kama shi ,bai taɓa tunanin zaiji wani iri ba,da ko kaɗan baiyi karanbanin haɗa jikin shi da nata ba,ya raina Sabreen ne,kallon kwaila yake mata.

lokaci ɗaya ya tsinci kanshi cikin wani yanayi gashi ta ƙasa natsuwa sai goga mishi dukiyar fulaninta take yi a ƙirjin “Waiyo Allah na hajia ,ka sake ni ,ka sake ni,bana so ni ba ƴar iska ba ce”

Da sauri ya sake ta,yana maida numfashi sama-sama shi kaɗai yasan abinda yake ji,”Meye yasa nake jan abinda xai sa yarinyar nan ta ƙara rainani? wanan tambayar yake wa zuciyarshi yana me jin haushin zuciyar shi

Jan motor yayi da gudu nan da nan ya isa gidn,yana tsaida motor ta fito da ƙarfe ta tura motar”Allah ya isa”

Tana faɗa ta wuce tana tafiyarta hankali kwance.

Dokan kujerar yayi inda ta tashi haɗe da jan wani dogun tsaki yana jin tsanarta a ranshi.

**********

” Alhaji gobe ya kamata ka gayamishi tunda zai ga mutane sun fara zuwa”

Cikin tausasawa ya kalleta ya ce”Xan gayami shi,ki kwantar da hankalinki nasan Naufal ba zai ja da ni ba,ban taɓa saka shi abu yaƙi yi ba komai girman abun,nasan zaiji wani iri amma na ɗan ƙankanin lokaci ne”

A haka ya kwantar ma hajia hankalin.

~~~~~~~~~

“ohhh ni Allah ƴar aljanna tun yanzu zaki fara min haka”

Idanuwanta tabb ta kwalla ta ce”Hajia ba zan iya nisa da ke ba,ko yaushe zan kasance tare da ke,wa gare ni banda ke,hawayen da suka maƙale suka gangaro.

Ita ma hajiar kuka ta fara yi haka suka kwana suna kuka.

~~~~~~~~~~
Haka ya koma gida jikin shi a mace yana ƙara jin tsanar Sabreen, amma wata zuciyar tajin shauƙin yadda take abubuwanta kai tsaye ba tare da jin shakkar komai wai ta kalli shi ta ce mishi allah ya isa, shi mamaki ma abin ya bashi, kashe wayar shi yayi gaba ɗaya.

Yau ma irin mafarkin nan yayi,tashi yayi yana keta zufa,haɗe da sauke nannauyan numfashi “Idan har haka zaki dunga min ki daina zuwar min mafarki” ya faɗa kamar wanda yake jin tsoron maganar,wankan tsarki yayi ,sanan ya fita zuwa masallaci salar asuba,yana dawo wa ya shige ɗakin shi,wayar ya kunna,sakonin Haulat ne suka fara sintirin shigowa,number ta ya kira,tayi ringin tayi har ta katse bai iya kira sau ukku ba iyaka biyu shi ma idan ya matsu yake yin shi.

~~~~~~~~~~~~~

“Yanzu taya xan haɗu da Malama Haulat gashi bani da numberta kuma ban san gidan su,dole na haɗu da ita,numberta ya kamata na samu”

Hajia ta shigo ta ganta ita kaɗai a zaune kan gado tana magana ita kaɗai “Sabreen ke dawa?

Juyowa tayi ta kalli hajiar a ranta ta ce” *NI* *DA* *MALAMA* *TA*

“eyyah ki dawa kike magana ki kaɗai?

Murmushi tayi ta ce”Hajia ba kowa ina tuno wani abu ne”

“Meye shi?

“Hmm Hajia ta ba komai ”

” to na yarda tashi ki je kiyi wanka ,yanzu xaki ga su Momyn ku”

“Toh tana faɗa ta tashi ta faɗa toilet”

~~~~~~~~~~~~

Tana farkawa ta duba wayarta ganin kiran Naufal yasa ta ruɗe ta shiga kiran shi da sauri,a lokacin yana ɗakin shi yana duba laptop din shi kiran ta ya shigo yana jin ringin ɗin ya ɗau wayar
ita ta fara magana”Hello dear lokacin ban tashi ba,kuma wayar bata kusa da ni sai yanzu na tashi”

“ok ba komai,kin tashi lafiya?

“Lafiya lau,meyasa kake min haka dear,dan ina sonka shine na cancanta irin wanan wulaƙancin”

cikin sigar lallashi ya fara bata hakuri”ba haka ba ne,duk lokacin ina tare da Dadyne mun fita.

“to shikenan bana
iya fushi da kai ko kaɗan”

A haka suka cigaba da fira cikin so da ƙaunar juna.

Suna gama wayar Dady ya kira shi yace mishi ya fito falo,yayi mamaki bai ga su hajia ba ya kalli dadyn ya ce”Dady ina zu hajia naga ban gansu ba?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button