HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Eh sun fita zasu je gurin su Sabreen wai zasu je gurin gyaran jiki”

Murmushi yayi ya ce”Mata ƴan kwalliya”

Gyaran murya Dadyn yayi ,ya ƙara gyara zama ya tattara dukkan hankalin shi gurin Naufa ya ce”Naufal ka natsu kaji abinda zan faɗa maka da kunnan basira”

Yadda yaji Dadyn yayi maganar yasa ya tattaro dukkan natsuwar shi yai ƙasa da kai “Ina jinka Dady”

“Naufal Naufal Naufal,Sau nawa na kira ka?

“Sau ukku!

“To ina son ka ji avubuwa ukku da zan gayamaka,ka ɗauke su ka saka su a cikin kwakwalwarka da tunaninka”

Zuciyar shi ta fara buguwa da ƙarfin gaske kamar zata fasa ƙirjin shi ta fito.

“Abu na farko Naufal ni na haifeka kuma ina sonka ina alfahari da kai,baka taɓa faɗa min rai ba ,ko na saƙon ɗaya kullum cikin bin umarni na kake,wanan dalilin yasa na son na tausasaka akan hukuncin da na yanke akan rayuwarka ba tare da naji naka ra’ayin ba,Naufal gobe zan ɗaura ma aure da Sabreen

Dumm Dumm zuciyar shi ta fara buguwa da ƙarfin gaske wanda tai nasarar sandarar da tunanin shi komai ya tsaya mishi chikkk ,sai zufa da take keto mishi ta ko ina a jikin shi,gashi ya kasa ɗaga kai ya kalle Dady.

“Ban san ra’ayinka akan ta ba,Naufal da wanan nake cewa kayi hakuri.

“Abu na biyu Naufal Inhar ka ɗauke ni uba to ina so ka ɗauke Sabreen a matsayin matarka kuma ƴar uwarka,ko kaɗan karka nuna mata ƙiyayya idan ka nuna mata ƙiyayya ban yafe maka ba..

A zabure ya ɗago kai da jajayen idanuwan shi ya kalli Dadyn na shi.

“Sabreen ina sonta fiye da yadda nake son ka,idan ka cutar da ita ko bayan ba raina ban yafe maka ba,Naufal,kuma idan har ka ɓata mata rai ta zubda hawaye Naufal ban yafe ma ba.

“Sai Abu na ukku wanda shi zan roƙe ka akai ,idanuwan shi sukai jajir muryarshi ta fara rawa abinda bai taba faruwa ba kenan tunda Naufal yazo duniya bai taɓa jin mahaifin shi a irin wanan raunanniyar muryar ba.

“Naufal dan allah dan annabin Rahma Naufal ka riƙe amanar marainiyar allah nan,ba dan hali na ba…

“Dady…dad..dady ka..

“A’a naufal wanan ba umarni ba ne,roƙan ka neke yi,Sabreen amana ce a guri na,zan danƙa mata ita,Naufal ka riƙe ta amana…..
.
[12/16, 5:36 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/16, 5:41 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????

 

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
Page 10
……………………………………………

*_السلام عليكم ورحمة
الله وبركا ته_*

*_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{IDAN ALLAAH YAYI NUFIN MUTANEN WANI GIDA DA ALKHAIRI, SAI YA MUSU JAGORAR (SAKA) ‘KOFAR SAU’KIN HALI(A GIDAN).}*_
°
“`[Silsilatus Saheeha;523]“`

_Duk gidan da suke da saukin hali to lallai Allaah Ya na nufin su da alkhairi. Arziki ne babba mutum ya siffantu da saukin hali. Allaah Ya azurta mu da shi. Allaahu a’alam._

“`Allah ta’ala yasa mudace“`

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

…………………………………………
Kasa ƙarasa maganar Dady yayi,jikin shi ya mutu ga kwalla ta cika mishi ido.

Cikin wani irin yanayi Naufal ya ce “Dady baka yarda dani ba ne, Dady komai girman abu zanyi shi idan har ka saka ni yinshi k….

“Ba haka nako son ka ce ba Naufal ina son naji ka ɗau alkawarin da zan baka ne”

Cikin raunanniyar murya Naufal ya ce”Na ɗau alƙawari zan riƙe Sabreen,zan kula da ita kamar yadda zan kula da kai na,ba zan bari wani abu ya faru da ita ba,nayi alkawari”

wata irin raguwar ajiyar zuciya Dady ya sauke”Kasan daraja da muhimmanci alƙawari ,ba sai na tunatar da kai ba.

“Naufal tun farkon rayuwarka kake min biyayya,amma ban taɓa jin daɗi abunda ka min irin na yau ,na gode Naufal”

“Dady dan allah ka daina gode min”

“Dole ne,amma Naufal karka yarda ka ƙara min alƙawarin da ka ɗauka,karka wulaƙanta Sabreen ,wllh Allah idan makamancin hakan ta faru zan iya fushi da kai ,zan iya rabu da kai,daga ranar ma karka ƙara kira na da sunan Dadyn ka”

Wasu zafaffan hawaye suka fito mishi zuciyar tana radaɗi da zafi,yau shi mahaifinshi ke gayama irin wanan maganganun masu zafi gaske “Dady ba zan ƙara alƙawari”

“Na sani Naufal kai jini na ne,ina ƙara ma ƙarfi ne yadda zaka riƙe da muhammanci,Sabreen tana sonka ita ta fara magana,na san kai ma kana son ta”

A razane ya ɗago yana kallon dadyn maganar da yayi tana mishi yawo a cikin kaI”Sabreen tana sonka ita ta ce tana sonka” kai anya ina wa…

“Naufal bamu ga ta zama ba,tashi mu fita gobe ne fah

Gaban shi ya faɗi” gobe gobe!!

“Ba’ayi biki haka ba,bakin ƴaƴan gata ka tashi mu fita,baka da wani abu da kake son ayi”

ƙasa yayi da kai,dan kanshi yayi nauyi.

“Naufal ko auran dole ne”

“uhm ina tunanin abinda za’ayi ne”

“to mu fita”

dadyn ya fara fita yabar nan,da ƙyar ya iya jan jikin shi,ba abinda yake tsorata shi irin da yaji Dady ya ce wai sabreen ta ce tana sonshi,tabbas yakan sabreen bata son shi,ko kaɗan” to meyasa zata min haka? dan tsana”

ya tambayi kanshi ya kuma bawa kanshi amsa”meyasa Why?Sabreen ke wacce iri ce kin dagula min rayuwata,da kika haɗa rayuwar mu tare,bana sonki bana ra’ayinki amma saida kika cusa kanki a rayuwata meyasa baki gane bana sonki ba, am helpines,ba zan iya komai ba Sabreen kin cuci ni kin….

“Naufal kayi sauri ina jiranka, dady ya katse mishi tunanin daya ke yi”

~~~~~~~~~~~~~

Su Sabreen manya ana chan ana gyaran jiki ita da farrah harda Momy ma, tasha lalle wanda ya fito da yar madaidaiciyar hasken jikinta,yaƙe kawai take yi amma bata jin daɗi a zuciyarta.

“Toh yanzu taya zan haɗu da malama,ko na bari bayan an ɗaura aure”

“Keeee tunanin me kike yi Aunty Amarya”

Ɓata rai Sabreen tayi”Farrah ki daina ce min aunty bana so”

“To matar yaya”

harara da gallama ta “waye matar yaya?

Dariya Farrah tayi “Kai Sabreen lamarin ki sai ke,ranar da kuka ,kina son yaya ya ɗaura muku aure amma yau wa waye matar yaya kike tambaya”

“ina son Yaya allah ya kyauta me xanyi da ɗan kilibibin nan”A zuciyarta tayi wanan maganar ,A fili kuwa harar ta tayi.

Momy bata gurin su kaɗai ne,ita ta koma gida dan tayi wasu aikin.

Sun daɗe har bayan maqrib suna nan ana abu ɗaya.

~~~~~~~~~~~~

Bayan su dadyn sun dawo ya tambayi momy ina su Sabreen ta gayamishi suna gurin gyaran jiki,Ɗadyn ya ce Naufal ya je ya ɗauko su.

***********

Wayar Farrah ya ya kira”Hello Ki fito ina waje” Ya katse wayar

Kallon Sabreen farrah tayi”Angon ya ƙaraso”

“Mitsewww!

“Ni tashi mu je yana jira idan mun je kin mishi tsakin”

Suna fitowa daga shagon motor shi,gaban Sabreen ya faɗi amma ta ɓata rai.

Daman ya lafiyar giwa balle tayi hauka,wanda ko farinciki yake ya ga damar ya ɓata rai balle kuma.

Bai ɗago kai ya kalle su ba,har suka shiga cikin motar,harar shi sabreen ke yi ta gefan ido a ranta tana faɗin”Ban kaddara da me zai haɗa ni da kai,kuma burina yana cika na son ɓatawa Haulat rai zan rabu da kai ne,dan ba zan iya rayuwa da kai ba”

kiran wayar farrah ne ya katse musu shirun da suke yi,ƙawarta ce,ita kuwa farrah ko a jikinta ta saki jiko suna fira akan bikin ma,hayaniyar ta fara damun shi

ya daka mata tsawa”Keee baki da hankali ne”

Bata san lokacin da wayar ta faɗi a hannun ta ba,jikin ta ya fara rawa,Ita kuwa Savreen ko a kafaɗar ƙafarta.

A haka suka isa Gidan su ya fara sauke ta,sanan ya zo gidan na su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button