HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Hankali kwance tayi wa Farrah Sallama harda faɗin “Sai goben kenan,ki fito da wuri”

A tsora ce farrah ta ce” toh”

Ba wanda ya kalli juna a cikin su.

~~~~~~~~~~
Ta isa falon ta hango hajia zaune akan kujera.

“Hajiyata ya baki tasu kin min oyoyo ba”

Ganin hajia wani iri yasa ta ce”Hajia lafiya?

Saida ta ƙaraso gurinta ta rungumeta”yanzu shikenan xaki barni ni kaɗai”

“Waya gayamiki ba inda zani ina nan”

“Zaki barni mana,zaki koma gidan Naufal”

Gabanta yai mummanan faɗuwa”zan koma gidan Naufal”

“Eh tare zaku dunga yin komai”

Ai sai hawaye ta ƙara rungume hajia,tana kuka ita ma hajiar kuka take yi,basu iya lallashin junan su ba,saidai gajiya suka yi da kukan,a ɗakin Hajia ta kwana.

~~~~~~~~~~~~~

Naufal ƙasa barci yayi abin duniya ya dame shi.

“Meyasa Sabreen zata min haka?
“Yanzu ya zanyi da Haulat na mata alkawarin aure?
Ba zanyi iya rayuwa da Savreen a matsayin matar aure na ba?

“Haulat nake so, ita ce zaɓina ita ce ra’ayina”

Tsanar Sabreen tana ƙara yawa a ranshi,amma na banza tunda ba abinda zai iya”Ban taɓa ganin irin wanan rayuwar ba”

“Sabreen sai kin gayamin dalilinki na ɓata rayuwa”

Ƙasa barci yayi duk tsawon daran ganin abu yana son mishi yawa yasa ya tashi ya ɗauro alwala ya fara sallar ko ya samu sassauci,ya kowa samu raka’a shidda yayi barci yai awan gaba da shi.

~~~~~~~~~

Tun a masallaci suka fita shi da Dady.

Yau Juma’a
Yau ne ya kama bikin Sabreen muh’ad mai taƙama tare da Angonta Naufal mai taƙama.

Gaba ɗaya Abuja da kewayan ta sunyi labarin wanan bikin kuma suɓ hallara,ƴaƴan government tana manyan yan kasuwa da na ma’aikata duk sun hallara,dubbanin mutane ne suka hallara gurin ɗauren Auran.

Chan na hango Naufal cikin Shadda purple harda malum-malum kayan sun mishi kyau matuƙa,amma kallo ɗaya zaka ma fuskarshi ya gane yana cikin wani yanayi wanda ba wanda zai iya tantance wa,amma yanayin yafi kama da damuwa,kusa da shi Dady kalar kayan su iri daya komai da komai,kai ka ce Dady ne Angon dan yadda yake washe baki yana farinciki.
Ƙarfe biyu za’a ɗaura Auren wanda yanzu saura minti ashirin da takwas a ɗaura auren.

~~~~~~~~~~~~

Da gudu ta faɗo ɗakin a ruɗe tana haki tana nishi “Haulat Haulat!!

Haulat wacce ke kwance tana mulka barcin ba abinda ke damunta.

Ganin ba zata tashi ba yasa ta ɗaka mata doka a baya “Haulat ke tashi banza kina nan kina barci baki san abinda ke faruwa ba”

“Ke dallah kinsan bana son ina barci a tashe”

“Au haka zaki ce ko”

“To me ya fara?

“ina ce Naufal ɗan Alhaji mai taƙama ne saurayinki?

Yamutsa fuska tayi”Eh shi ne lafiya dai

“Hmm ina lafiya to wllh yau za’a ɗaura mishi aure yanzu haka an hallara gurin ɗauren Auran..

Tsaki Haulat taja”Ke ni bana son irin wanan abun kawai zaki so ki ɗaga min hankali”

“Haulat kenan kina ganin wasa ne to shikenan ba zan matsa miki akan sai kin yarda da ni ba,amma nasan gaskiya zata baiyana,tana faɗa ta fita daga ɗakin.

Ita kuwa Haulat ƙara komawa barcin ta tayi,ko a jikinta.

Ƙarfe biyu daidai aka ɗaura auran Naufal da sabreen fiye da mutane dari sun shaida ɗaurin auren.

Tunda aka ɗaura auran jikin Naufal yayi sanyi zuciyar shi sai faman bugawa take yi,kamar wanda ya tashi daga dogon jinya haka ya ke ji.

~~~~~~~~~~~
Zaune take akan gadonta tasha kyau har ta gaji,ita kanta jikinta yayi sanyi”hmm ko bakomai yanzu na ɗauka fansa akan ki Malama Haulat tunda na aure wanda kika fi so a duniya kina ji kina gani ba abinda kika iya akai,Naufal ni ba tsarar auranka ba ce kamar yadda nasan kai ni ba ra’ayinka ba ce,dan haka bazan zauna da kai ba,nan da ƴan wasu lukuta kaɗan zan rabu da kai”

“Aunty Sabreen tunanin me kike yi”Farrah ta faɗa ta ƙarfi haɗe da jijjiga Sabreen ɗin.

“To meye na tunani bayan an ɗaura auran Naufal ya zama naki ke kaɗai,ko tunanin rabuwa da hajia ne”

Harara ta mata”Ke baki jin magana ko nace karki kira ni da Aunty ki”

Dariya farrah tayi sosai ta ce”Maida wuƙar ƴan mata”

~~~~~~~~~~~~~
Ba su suka samu damar zuwa gida ba sai ƙarfe biyar da wani abu,suka shigo gidan lokacin ba mutane sosai a gidan,kowannen su ya nufi ɗakin shi.

Yana zuwa ya faɗa kan gado,haɗe da sauke nannauyar ajiyar zuciya,ya daɗe a haka yana tunani Tunanin Haulat kawai yake yi ita yake so ita ce ra’ayin shi ita yake da burin ya aura”bazan karaya ba Haulat ina sonki zan kuma aureki dan ke ce muradin raina” ya fili ya faɗa.

Ringin ɗin wayar Dady ne ya shigo wayar,yana ji ya ɗauka

“Naufal karka Zauna fa akwai dinner da za’ayi karfe shidda kayi sauri ka shirya sun gama shiri kai kawai suke jira gidan hajia zaka ku tafi tare da Sabreen ɗin” yana gama faɗa ya kashe wayar shi.

“Why Sabreen? i cant i cant,ba zan iya rayuwa da ke ba Sabreen” idanowan shi sukai jajir.

Da gyar ya iya sarrafa jikin shi yayi wanka ya fito,kallon kayan drower ya tsaya yi ,ya rasa wanda zai saka,wata baƙar suit ya ɗago mai haɗe da ash colour ya saka sun mishi kyau ainun,kallon kanshi a madubi yayi.

“Wai ni aka ɗaura wa aure da Sabreen yanzu ni mijinta ne?

ya nuna kanshi”Ni Naifal nine mijin Sabreen”

Ƙasa yayi da kanshi yana sauraran bugun zuciyarshi wanda take buguwa da ƙarfin gaske.

Turaran da ya shafa sunfi kala goma ta ko wacce gaɓa ya shafa mata turaran da ake shafawa.

Bayan ya gama shiryawa ya fito cikin ƙasaita da izza yana tafiya kanshi aƙasa,baiyi mamaki ba ganin ba kowa a falon,yana fita yaga motoc irin na alfarma gudu shidda kalar su ɗaya ash colour irin kayan shi,sun ganin fitowar shi daga gidan suka fito,suka buɗe mishi kofa ya shiga cikin isa da mulki.

~~~~~~~~~~~~~

“Sabreen ki saka wanan kalar tafi kyau”

“Ke ni bana son shi,wan xan saka,ta nuna wata dugowar riga baƙi da ash kala,rigar ta haɗu iya haɗu

“To bana matsa miki ba Amarya”

Tana saka kayan aka fara mata makeup waw masha allah ashe haka Sabreen ke da kyau ,tayi kyau har ta gai.

Ba’afi minti goma da gama makeup ɗin ba aka aiko Naufal ya iso su fito,taɓe baki Sabreen tayi.

Rigar dugowace sosai tana tafiya tana binta Farrah da hajia su suka riƙo ta har wajen gurin motorcin,motor da yake aka buɗe mata ta shiga,tana shiga wani irin sinadarin ƙamshi ya doki hancinta har saida ta lumshe ido.

Kusa da juna sosai suka zauna hakan ya ƙara haifar musu da matsanaicin bugun zuciya,kowanne yana jin fitar numfashin kowa

“Bata sonka ko kaɗan”

“Na sani kuma kema kin san bana sonki”
“But why Sabreen?

Bata kalle shi ba,daman ko ɗazun bata kalle shi ba”Saboda ɗaukar fansa”

wanan karon saida ya kalleta ,zuciyarshi ta buga dan ta bashi tsoro ganin irin kyaun da tayi gashi kalar kayanshi ta saka,cikin wata siga wacce shi kanshi bai san lokacin da ya tsinci kanshi da shiga yanayin tausasawar ba ya ce”Sabreen!

Lumshe idanowa tayi tana jin daɗin yadda yake kiran sunanta a tata cewar da indiyanci yake kiran sunanta.

Shi kanshi saida yai jimm,bai san abinda ya yasa shi yin hakan ba,ganin bashi da niyyar magana ya ce tace mishi”Nima ba zan zauna da kai ba,zamu rabu ne,dan wata manufa na aureka,karka ji wani avu nasan baka so na ka kwantar da hankalinka zamu rabu”

Da mamaki yake kallonta kanshi ya ɗaure hali irin na Sabreen yana bashi mamaki yadda take mishi magana ma abin mmk ne har ya buɗe baki zai mata magana motor ta tsaya tana tsayawa aka buɗe musu kofa.

Yana sauko da kai idanowan shi sukai arba da ƙaton hutun su wanda suka yi matuƙar kyau mamaki ya ƙara kamashi ganin yadda Sabreen tayi murmushi a hoton kamar wacce take son shi,ga hoton yayi kyau kamar ba haɗa shi aka yiba,a tare aka yi shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button