HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Murmushi tayi sannan ta rungumeta “Kina lafiya hajiyata yau bamu fito da wuri ba ne,wanan ƴar iskar malamar ce ta tsayar da mu”

“Cikin nuna damuwa ta janye jikin ta tace”Wai ko sai na tura anje gurinta ne aja mata kunne,ko na fitar da ke daga makarantar gaba ɗaya ma”

“A’a Hajiya ki barta kinji ”

“to ni bansan duk wani mahalukin da zai ɓata miki rai,zan iya yin komai akan farincikin ki”

Daidai da isar su cikin katon falon wanda shi ma ya ƙyyatu har tsoro yaban dan tsabar kyaun shi,ga wani asirtaccen kamshi wanda ya haɗe da AC ɗakin.

Murmushi tayi cikin shagwaba ta ce “Nima na sani hajiyata,amma tunda na ce ki barta kawai ki barta zanyi maganin ta ,zan gwada mata ni ɗin ƴar gata ce”

“Hajiya bari na hau zama nayi wanka sai nayi sallah na huta”

“Yawwa ƴar aljjanna na manta ban gaya miki ba,ɗan india ya dawo an jima sai ki je ku gaisa”

Yamutsa fuska tayi yin sunan wanda ya dawo din”Wanan dan iyayin wanda aka je ɗauko mu tare”

“Eh shi fa”

“Tabbb gaskiya ni ba zani ba saida shi ya zo “ta faɗa tana hada rai

“to shikenan ba zai kin ɓata rai ba,zan sa ya zo da kanshi,kinji hankalinki ya kwanta”

ta washe baki “eh hajiyata,ta haye sama ,a ranta tana faɗin yadda zata ganshi dan tun sanin farkon da ta mishi kafin yaje india dan iyayi da kinibibi ne,to bari yanzu da yaje india….

Kasa kwanciyar tayi, tunanin abinda zata yi ma malama Haulat ta shiga yi, wani guntun murmushi tayi dan ta gano abinda zata mata , gajiya da zama ita kaɗai tayi ta sauƙo falo.

Ba Kowa a falon ,har zata ɗakin Hajiya sai kuma ta fasa ta dawo ta zauna.

“Banza dabba daƙiƙiya mara hankali”
Runtse idanuwanta tayi tuno zafafan maganganun da malama haulat ke gaya mata.

Bata san lokacin da hawaye suka ƙankaro mata ba,sai jin su tayi ,ƙasa share su tayi dan takaici a fili ta ce “Wallahi sai kin biya,baki san waye ƴar aljanna ba,bana yafiya kuma ba zan yafe miki.

Wani irin hamshakin ƙamshi hancin ta ya ji,wanda saida ta lumshe ido tai wata irin ajiyar zuciya ,ɗago da manyan idanuwanta tayi dan ganin wanda ƙamshin ke tashi a jikin shi.

Waw masha allah ,allah yayi halitta wanda duk wanda yai arba da ita saiya ɗan tsorata dan tsabar kyau,kyakykyawa ne first class ga kwarji ni irin na jaruman maza ga izza,abin kamar a novel,fari ne sul mai yalwar gashin kai da na ido da na gira,ga dugon hanci kamar na indiyawa,duk da fuskarshi a murtuke take amma saida kyawun shi ya fito

Tsaye yake a kofar falon hannuwan shi gaba ɗayan su ya rungume su a ƙirjin shi,fuskar nan a murtike sai yatsinata yake yi ,kamar wanda ya shigo bola.

Tun kallon farko da Sabreen ta mishi ta gane shi,ganin yadda yake yatsina fuska yasa ta kau da kai ,ta ƙara gyara zaman ta rimot ta ɗauka ta chanja tasha ta kuma ƙara bulum,ta gafen ido take kallon shi yakai saƙonni a tsaye a gurin kafin ya fara tawo wa,wani ƙululon takaici ya kamata,Sabreen ta tsana mutum mai iyayi da kilibibi.

Dan guntun tsaki ta ja,ta cigaba da kallon tivi abinta.
Har tsakiyar falon ya iso,kallon ta yayi yana mamaki hali irin ta,wanda zai kira da rashin tarbiyya,bai ce mata komai ba ya samu guri ya zauna yana wani yatsina fuska haɗe da hura ɗan karamin hancin ta,yana kuma taɓe ƙaramin bakin shi,ni dai kuwa kallon shi kawai nake yi ina murmushi dan abin ya mishi kyau.

Ganin bata da niyyar mishi magana gashi yana sauri yasa ya kalle ta a hankali cikin wata irin murya wacce zamu kira da ƴan kilibibi ya ce “Sabreen plss go call hajiya for me”

Da sauri ya juyo tana kallon shi bata san lokacin da wata irin muguwar dariya ta kubuce mata ba,”Bala’i yau ga wanda yafi malam haulat bala’i to ikon allah ”
A zuciyarta tayi maganar ta kuma ƙasa daina dariyar.

Wani irin kallo ya bita da shi yana yamutsa fuska haɗe da taɓe baki,cikin wani irin ƙaƙale ya ƙara ce mata “What Rong with you”

Haba ai sai ta ƙara fashewa da wata muguwar dariya harda hawaye dariya dariya kamar ba zata daina ba,idan zata daina sai ta ƙara tunowa ta ƙara kwacewa da dariya.

“Ƴar aljanna dariyar me kike yi haka ,lafiya?

Hajiya ta faɗa lokacin da ta shigo falon gurinta ta ƙarasa,ɗagowan da tayi ta ganshi ,ta washe baki ta ce “Ƴan india ne a gidan yaushe ka shigo”

Saida ya yamutsa fuska kamar wanda ke jin wari ko wanda yake kallon kashi ya ce “Ɗazun ne”

Haba ai wata irin dariya ta ƙara fashewa da ita har saida ta faɗo daga kan kujerar dan tsabar dariya.

“Waiyo ni Sabreen hausar ma ba za’a barta ba”

A zuciyar ta faɗa,ita kuwa Hajia ruɗewa tayi dan ganin irin dariyar da Sabreen ke yi.

“Waiyo Allah na bani ƴar aljnna”

*Naufal* hajia ta kira shi, ka taimaka ka kira likita”

“u mean doctor”

Ba Sabreen ba ni kaina saida na dara dan yadda ya ƙira doctor ɗin,mugun ɗan ƙaƙale ne,dan abin dashi ya wuce iyawa ya koma kaƙale,kamar yadda ake fitar da harafin larabci haka yake fitar da kowanne harafi harda ƙari ma.

Kuka hajia ta fara “Waiyo na shiga ukku ni yau”

Ganin hajia na ƙara ruɗewa yasa ta fara kukarin tsaida dariyar amma ta kasa,saida ƙyar da sassauta dariyar ta kalli hajia ta ce “Waiyo hajia ta ba komai lafiya ta lau dariya ne Kawai”

Shi kuwa Naufal yana gefe yana kallon su dan bai gane shi take yiwa dariya ba,dan shi a nashi ganin baiyi abin dariya ba,kallon mahaukaciya yake mata.

“Jajia bari na tafi ana jira na”

yadda ya ke kiran sunan hajiyar ma abin a dara ne,dan mugun ɗan ƙakale ne na ƙarshe.

Kasa ɗaurewa Sabreen tayi haba ai sai ta cigaba da dariyar.

“To mutun india ka gaida hajiyar ku ,zamu shigo da daddare mu amshi tsarabar mu”

“Okkk hajia sai kun zo”

Kamar wanda ba bahaushe ba haka yake hausar.

Yana gama faɗa yabar falon yana tafiya cikin ƙasaita da izza tafiyar ma abin kallo ce,da ana karatun iya tafiya da sai na ce ,yayi digiri gurin iyawa.

Da ƙyar sabreen ta iya tsaida dariyar ta”Hajia ta wai ke ba ki ji abinda da nake yiwa dariya ba”

“Yo ina zan ji ni tsoro ma kika ban”

“Wancam ɗan indian ne yaban dariya ji yadda yake magana kamar shi ya kawo magana duniya u mean doctor”

ta maimaita abinda ya faɗa ta irin yadda yayi maganar.

Dariya ita ma hajiyar tayi ta ce “kin san daga india yake shiyasa”

“Su ƴan indian haka su ke,ƙilibibi ne na bala’i,kai bari n Je nayi wanka dan jikina duk ya mutu .

“Ba dole ba irin wanan mahaukaciyar dariya ai dole jiki ya mutu”

hajiar na gama maganar ta haye sama tana dariya da mamaki dan bata taɓa tunanin za’a samu wanda yafi malama haulat iyayi da ƙilibibi ba…

~~~~~~~~~~~~~

Zaune take a tankameman falon wanda yasha fentin pink da fari haka zalika komai na cikin falon kujeru da flowers da sauran kayan alatun rayuwa.

Fuskar nan tata dauke take da annuri wanda nake ganin kamar haka halitta yake wato smile face akan 2 sitter take zaune,ita ma karya kyakykyawace ga murmushi, babba mace ce mai halin girma.

A gafe guda kuwa Wata kyakykyawar yarinyace ko na ce budurwa wacce shekarun ta ba sufi goma sha takwas ba, tun kallo na farko na gane suna da alaka da matar nan dan irin Yadda suke gama.

Cikin siririyar murya ta kalli matar ta ce “Momy nifa na ƙagara naga tsarabar da yaya Naufal ya kawo min,wai ina ma yaje ne daga zuwan shi”

Murmushi tayi wanda ya ƙara baiyana zatin fuskarta ta ce “ke kuwa *farrah* kina da gajin hakuri kuma kin san halin Naufal baya son damuwa idan kika nuna mishi kin zaƙu ya hanaki,ya je gurin Hajia ya gaida ta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button