NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Naufal ma ji yake yi ina ma zai iya yin kukan da yayi ,dan shi ne abin kuka ba su ba.
Ganin basu da niyyar daina kukan Dady ya ce”Ya isa haka kuyi hakuri dole daman sai wanan ranar ta zo.”
Kallon Naufal yayi ya ce”Naufal tashi ku tafi”
Gaban shi ya faɗi”Na tashi mu tafi”ya maimaita abinda Dadyn ya faɗa a hankali,shi kanshi zaida yaji wani iri wai yau zai bar gidan su ya kwana a wani gida daban.
Sabreen tana jin abinda Dady ya faɗa ta ƙara ƙanƙame hajia tana kuka mai tsuma zuciya.
Tashi momy tayi taje da riƙo Sabreen tana san ta rabata da jikin hajia.
“Waiyo hajia Momy dan Allah ,Hajia bazan tafi na barki ba,waiyo hajia ki riƙe ni,momy momy kiyi hakuri na fasa auran bana so Allah na fasa bana son ya naufal,hajiyata bazan tafi ba…
Duk da yanayin da suke ciki saida suka yi ƴar dariya,musamman Naufal da farrah A ran shi ya ce”Banza daman haka kike amma kika ce kina son aure n..
“Naufal zo ka jata”
Dady ya katse mishi tunani.
Hajiya ya fara ja dan baya son ya taɓa Sabreen.
“kai ita zaka ja”, Dadyn ya taɗa.
Hannun shi yakai kan kafaɗar ta,ya fara janta ,ita kuma momy taja hajia.
“Yawwa kamata ku fita”,cewar dadyn
Kuka Sabreen take yi tana ihu “Waiiyoo! wllh Dady na fasa bana so,dan allah ku barni,na zauna da hajia bana son auren,Yaya Naufal dan allah ka barni bana so waiyooo”
Dariya ta bashi sosai har ya kasa ɗaurewa zaida yayi,ita ma farrah dariya tai tayi.
“Karka sake ta Naufal.”
“To Dady.”
Har suka fito daga fallon tana kuka,gurin shiga motor ma,saida momy ta turata da ƙarfi tana shiga aka kulle kofar,hajia bata fito ba tana chan tana rusa kuka an rabata da ƴar aljanna.
shiga motor yayi direba yaja suka fita daga gidan,Su momy suna nan tsaye har motor ta fita,sanan suka dawo suyi ma hajia sallama su koma gidan su.
Dariya Naufal ya fara yi sosai da sosai wanda bai taɓa yin irinta ba.
Ƙara fashewa da kuka tayi mai sautin gaske.
“ke dare ne ki mana shiru baki son rabuwa da ita kika ce kina son aure.”
ys ƙara fashewa da dariyar shi.
Kuka Sabreen ke yi sosai bata kuma kula shi ba har suka isa unguwarsu,wani katafaran gida ne,wanan kallo ɗaya zaka mishi kasan ankace dala,dan ya fituno da kyau abin zai wanda ya gani.
Suna isa harabar gidan direban ya tsaida motor,shi ya fara fitowa”Idan kin ga dama ki sauko idan baki ga dama ba ya maida ke gidan hajia.”
Yana faɗa ya shige abinshi yana tafiyar kasaita da izza.
Kamar ta ce direban ya maida ta gurin hajia sai kuma ta fasa ,ta sauko ta bi bayan shi a falon ta isko shi,tana kuka ta karasa gurin shi ta ce”Idan na koma zance kaika kuro ni,ka ce na dawo.”
A fusace ya miƙe har zaiyi wata magana ya fasa tuno halin Sabreen ba abinda ba zata iya ba,wani mugun kallo ya mata sanan ya juya ya haye sama.
Har lokacin bata daina kuka ba,kallon falon tayi ya mata kyau sosai,kan gujera ta hau,tana ta kuka har barci ya ɗauke ta.
Daman yasan gidan ya kuma zaɓa ɗakin shi,yana zuwa ya shige saida yayi wanka yayi sallah sanan ya kwanta,ya daɗe yana tunanin irin zaman da zasu yi da sabreen sanan shi ma barci ya ɗauke shi.
~~~~~~~~~~~~~
“mtseww!
“Wai ke wa kike ma wanan tsakin tun ɗazun.”
Wani mugun kallo tayi mata sanan ta ce”Ban sani ba”.
taɓe baki tayi ta cigaba da yin abinda take yi.
Kallon wayarta tayi ta ce”Naufal meke faruwa ne?
ƙanwarta wacce suke zaune a ɗakin ta kalleta a ƙaro na biyu ta ƙara cewa”Ai daman na sani”
“Kin san me,banson iskancin banza.”
Tana rufe baki saƙo ta whatssap ya shigo wayarta,kamar ba zata duba ba,dan baƙowar number ce.
Sai ta duba, a tsorace ta miƙe tsaye haɗe da zaro idanowa,xuciyarta ta fara bugawa da ƙarfin gaske”Wa.i..y..”
Numfashin ta ya fara sarƙewa dushu-dushe ta fara gani.
“Aunty haulat lafiya mai ke faruwa? a ruɗe take tambayarta,ko kafin ta ƙarasa gurinta ta faɗi kasa zummama.
“Innalilahi! momy momy Aunty haulat mun shiga ukku.
~~~~~~~~~~~~~
kiran sallar farko a kunnan Sabreen a ruɗe ta fara tambayar kanta “Nayi Sallah jiya?
“Innalilahi ta faɗa da sauri ta miƙe tuno bata yiba,saman ta hau a ruɗe ,kasancewar bata san wani ɗaki ba ne tashi ta faɗa dakin shi,bata ma lura da yana kwance akan gadon ba tayi toilet da Sauri.
Jin ƙarar ruwa ya farkar da shi,kunna guluf mai hasken yayi,”waye a baya” ya faɗa a hankali saukowa yayi,sautin tafiya taji a tsorace ta ce”Waiyo Allah na waye”
“Ke meye ya kawoko ɗaki na?
“Bansan ɗakin ka ba ne”
“Bakin san ɗaki na ba ne”.
“eh!
“To fito nima zan shiga ne”.
“Waiyo karka shiga ya hakuri dan allah dan allah”.
Dariya ta bashi a ranshi ya ce “Kamar wata wacce zan ga wani abu ƙwaila da ita”
Murmushi ya fara yi tuno hali irin na ta,mawuyacin abu ne ta ba mutum hakuri,amma yanzu harda wani haɗa shi da allah.
“To na baki minti biyar kafin na dawo ki fito”
Yana faɗa ya juya yana murmushi.
Tana jin ya fita ta fito da sauri,ta faɗa ɗayan dakin wanda ba tazara a tsakanin su da juna,tana shiga ɗakin ta kulle,kallon ɗakin ta tsaya yi,ganin zai shagaltar da ita yasa ta maida hankalinta akan abinda zata yi.
Yana dawowa yaga bata nan daman yasan ba ganinta zaiyi ba,shiga toilet ɗin yayi ,saida yayi wankar tsarki sanan ya fito ya gabatar da ibada.
Zaune yake kan sallayar yana hailala da tasbihi wa ubangijinki,tunanin Haulat ya shigo ranshi zumbur ya miƙe ya fara naiman layinta…
Ringin wayar tayi har ta katse ba’a ɗauka ba,tsoro ya kama shi,tunda yake da Haulat bata taɓa ƙin ɗaukar wayar shi,cikin hanzari da zaƙuwa ya ƙara kira,nan ma shiru ba’a ɗauka ba,saida yai kira biyar abinda bai taɓa yiba ,amma shiru ba’a ɗau wayar ba,jefar da wayar yayi akan gado ransh a ɓace,haɗe da hura hanci.
“Haulat Allah yasa kina lafiya?
“Taya zata kasance cikin lafiya bayan abinda ka mata.”
Da kanshi yayi tambayar kuma ya ya ba kanshi amsar da ta ƙara ruɗa shi,yasan bai kyauta ma Haulat ba,ya kamata ya sanar da ita koma meye,yanzu idan taji a bakin wani fah.
Tashi yayi ya fara safa da marwa a tsakiyar ɗakin,lissafin shi duk ya dagule,kanshi yayi zafi tunanin halin da masoyiyar shi take ciki yake yi,wanda ya ɗaura laifin akan Sabreen ko kaɗan baya jin zai iya raga mata kan abinda da mishi,zumbur! kamar wanda aka tsungula ya fito da sauri,bibbiyu yake taka matalakar dan sauri,har ya iso cikin falon bai kula da mutanan dake ciki ba,ya fara ƙokarin fita.
“Ango Naufal ina kuma zaka je ka bar amarya ita kaɗai.”
Tsayawa chikk yayi sakamakon jin muryar ko ta wacece,a hankali ya juyo dan ƙara tabbatarwa zaro ido yayi ganin ba ita kaɗai ba..
“Naufal saurin me kake yi,baka kula da mu ba.”
Momyn shi ta katse mishi tunanin shi,kallon su yayi,Hajiaya ce ita da Momy da farrah sai Sabreen ɗin wacce ke manne a jikin Hajia, “Meye kuma ya kawo su da safe haka? taya zasu zo mana gida a irin wanan lokacin jiya ne fah muka tare”, a ranshi yake wanan tambayar,”To meye wani abun zamu yi waɗan da ba son juna muke yiba”,duk a zuciyar shi yake wanan tunanin,bai san lokacin da ya ƙaraso tsakiyar falon ba,sai jin shi yayi zaune a ƙasa,cikin harɗaɗiyar murya haɗe ta aro murmushi ya yafawa fuskar shi ya ce”Ina Kwana momy.”
Bai tsaya jiran amsarta ba ya juyo da kallon shi ga hajia ya ce”Ina kwana Hajia ya gajiya.”
yana kai aya hajia ta ɗauka”Lafiya lau Naufal ka barni da kewa shi ne ko tambayata baka yiba,au naga kamar ba baka so ganin mu yanzu ba.”