NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Kallonta yayi ,yana tuhumar kanshi akan maganar da ta gayamishi ,a fili ya ce haɗe da ɗan guntun murmushi, “Ba haka bane hajia,ya kewa?
“Ba sauƙi jiya ban iya barci ba ,da zan iya da nayi kishi da kai”
Gaba ɗayan su sukai dariya banda Sabreen wacce ta murtike fuska.
“yi hakuri Naufal munzo kawo abinci ne da farrah zata kawo to sai hajia ta ce tana son zuwa.”
Murmushi yayi ya ce”Ba komai Momy.”
“Amma ina kake ƙokarin zuwa?
“Am..amm..da. amman daman zanje gurin hajia ne na samo mata abinci bata ci komai ba.”
ya faɗa yana kallon Sabreen ɗin yana mata guntun murmushi.
Charab hajiar ta ce”Hm to na hutar da kai,amma naji daɗi da kake nuna kulawarka akan Sabreen na gode Naufal Allah ya biyaka da aljannar shi.”
“Ba komai Hajia ko kin manta Sabrewn ƴar uwata ce,zan iya yin komai a matsayinta na ƴar uwata,sanan kuma matata! daidai gurin yji zuciyar shi ta buga ƙara maimaita kalmar yayi “Matata!
Wani irin kallo Sabreen ta mishi na mamaki,shi ma ɗago kai yayi suka haɗe ido mugun kallo suka yiwa junan,amma sai suka yi murmushi.
Wani irin daɗi ya mamaye Momy wanda ta kasa ɓoyewa sai yaƙar baki take yi,kamar Ango.
Ita kanta farrah dake gefe murmushi take yi,dan jin daɗin yadda naufal ya aminta da ita cikin ƙanƙanin lokaci haka.
Wai kuma kunsan farinciki gurin hajia ba sai ance komai ba.
Sun ɗan taɓa fira kaɗan,sanan momy ta kalli hajia ta ce”Hajia to mu tafi ko,yadda zasu sake su iya cin abincin da kyau.”
Kallon momy yayi a ranshi ya ce”Hm wai mu sake kamar wasu masu cin amarshi.”
Sabreen naji abinda momy ta ce,idanowan ta sukai jajir kwalla ta shika su famm,cikin murmuyar kuka ta ce”Hajia yanzu tafiya zaki yi.”
Momy ta ce”Kinga idan kuka zaki dunga yi,xata daina zuwa,muma zamu daina zuwa,kina son gobe ta zo?
ɗaga mata kai tayi alamar eh.
“Toh idan kina so ta zo gobe,kiyi shiru.”
“Tohhh! kawai ta faɗa.
Kallonta hajia tayi ita ma hawayen ne a idonta ta ce”Kiyi shiru kinji ga mijinki nan zai tayaki zama,kuma baga waya ba,sai ki kira ni mu gaisa.”
“Ba zaki xo gobe ba.”
“zan zo.”
A tare suka fita fita har harabar gidan,suna kallo suka shiga motor,Sabreen sai hawaye shaaa kamar famfo,ko kallon inda take baiyiba ya juyo ɗakin,yana zuwa ya janyo kulolin abinci ya fara ɓuɗewa,kunon gyaɗa ne sha madara sai waina da miyar ita kanta wainar sai tashin ƙamshi take yi,miyar ma haka ga nama zaƙo-xaƙo,sai dangalin turawa soyayye da dafaffe wanda ya haɗe da hanta, sai kuma farfeson kaza,da soyayyan gwai harda lipton,kallon abincin yake yi yana yamutsa fuska kamar wanda yai arba da ɗanyan kashi.
Kunon gyaɗan da waina ya xuba ya fara ciki,yana cikin ci Sabreen ta shigo,kallon shi ta tsaya yi.
“Waya ce ka cimin abinci ai ba kai aka kawo mawa ba.”
Bai ɗago ba balle ya tanka ta,saida ya gama ci ,tana kallon shi yana hura hanci kamar warin abincin yake ji.
Yana gamawa ya tashi saida ya fara goge hannunshi da hankey sanan ya tashi har lokacin bai kalla inda take ba.
“Ina zaka?
A fusace ya juyo gabanta ya ƙaraso dabb da ita har suna jin fitar numfashin juna,kallon ta yayi ido cikin ido ya”Momy ko Dady,kuyi hakuri dan allah zani gurin wacce nake so ne.”
“Toh ban aminci ba.”
Dariya ya fashe da ita sosai yana mamaki hali irin na Sabreen,a lokaci ɗaya kuma ya murtike fuska kamar ba taɓa dariya ba,rikiɗewa yayi ya dawo ainihin Naufal mara dariya ɗan gilibibi da iyayi da yatsine isa izza mulki.
kallon ta yayi ya ce”me zan miki idan na tsaya?
“Ai.. dan…
“Hm Sabreen dan kin aure ni,da ƙarfi ba ki da ikon juyani,kin gane yana maganar yana ƙarya harshe cikin iyayi.
Kallon ƙaramin bakin shi Sabreen ke yi,yadda yake fito da maganar take kallo.
Ƙara matsuwa yayi dabb ta ita ƙokarin haɗe bakin su ya fara yi,tureshi Sabreen ta fara ƙokarin yi,amma ina ta kasa.
“Yadai ba abinda kike so ba kenan.”
“Allah ya kyauta ni ba ƴar iska ba ce.”
“Ni kuma ɗan iskane,u know what Sabreen?i cant share anything with you,”
“Ni bana jin yaren india.”
Haba me Naufal zaiyi dariya ya fashe da ita harda komawa baya ya zauna kan gujera.
Ta ƙule gurin takaici hararshi take yi ,shi baima san tana yiba,saida yayi me isarshi sanan ya tsaya ,ɗaure fuska yayi ya ce”u are very funny Sabreen.”
Ko kaɗan Sabreen bata gane abinda yake faɗa,ko hausar ma ba ko wani lokaci take ganewa ba.
Fita yayi yabarta a tsaye tana jin hauci.
“Kai Anya banyi kuskure ba,gashi gurin Haulat zaije kuma sai ya gayamata abinda ya faru ni nace zan aure shi baya so na,waiyo allah na yanzu ya zanyi? ya zanyi???
Naime naime ta fara yi,chan ta hango abinda take naiman wayarta ce.
“To yanzu wa zan kira?
“Dady nace mishi me?
“Na kira Naufal yawwa shi ,to me zanje mishi ya dawo.
Cikin rashin abinda zata faɗa mishi ta kira shi,yana tafiya a cikin motor shi da tunanin yadda zai fusanci Haulat a ranshi,jaji ringin ɗin waya,baƙowar number ya gani dan bashi da number ta,kamar kar ya ɗauka sai kuma ya ɗauka,tana jin ya ɗauka tai shiru.
“Hello! waye?
“Ya Naufal ka dawo gida yanzu Dady ya zo yana son ganinka.”
“Ohhh no! Am coming” yana faɗa ya katse wayar ya juyo da sauri a zuciyar shi yana tausayawa kanshi halin da zai shiga,ya kamata a kyaleshi ya sarara amma yaga alamar ba’a da niyyar barin nashi.
“To ni yanzu idan ya zo me zan ce mishi,ko na ƙara mishi wata ƙaryar .”
“Ah’ah ba zan kara mishi wata ƙaryar ba,gaskiya zan faɗa mishi.”
“To idan yaji hauci fah?
“to sai me ba abinda ya isa ya miki”
Murmushi tayi haɗe da juyo kanta”Hm ni ce fah ƴar aljanna ƴar gata kuma shalelen Hajia da Dady,sai abinda na ce,baka da yarda zaka iya Ya Naufal zan juyoka”
????waiyo aka ce raahin sani yafi dare duhu Sabreen kina da ƙuruciya kuma kinyi kuskure.
Tana gaba faɗa ta haye sama tana jin daɗi,wanka tayi ta saka riga da sikit na atamfa shiff-shiff suka mata kamar dan jikinta aka yi kayan,ko mai bata shafa ba,ta fito falo ta zauna akan 1seater ta kunna tivi tana kallo hankali kwance.
********************
Kwance take akan gadan ta hannuta ɗauke da drip,barci take yi,tun jiya har yanxu bata farka ba.
Momynta ta kalli ƙanwarta salma ta ce”Kai salma lamarin Haulat yana ban tsoro ,ban taɓa tunanin akwai namijin da zata shiga wani hali akan shi ba,tun yaushe nake gaya muku,daga kun ga abinda yake son ya gagareku ,kuje gurin malam gajere zai warware muku komai amma kun ƙi jira kuke yi saina kama ku na kaiku”.
“Ba haka ba ne momy,shi ma yana sonta dan ya sha matsa mata akan ta bashi izini ya turo.”
“Yana sonta shi ne zai aura wata ke baki ga hoton ba,yadda suke wa juna kallon soyayya.”
“Wllh momy yana sonta bansan yadda aka yiba,kuma ita ma tana da laifi tunda tun lokacin yake mata mita ya fito taƙi amcewa.”
“Ni na kasa gane abinda kike son faɗi,kina nufin wanan zoƙeƙen saurayin ne zai tsaya a mishi auran dole,bari kiji yanzu ko wacce mace ba’a zaune take ba ,musamman ma shi wanda kowacce mace ke buri ,to da ƙyalla ido ta ganshi bazata bari ya ƙuɓuce mata ba,amma ita dayake bata da wayau shashace ta zauna haka ai gashi nan tana ji tana gani an ƙwace mata shi,ba yadda zata yi.”
“Hm momy kenan ai ko ni kinsan ba hakura zanyi ba,balle Aunty Haulat kuma akan abinda tafi so a duniya ai wallahi zata iya yin komai akan shi,ba zata haƙura ba.”
“To da dai yafi mata,ta ɗau mataki,akwai wani sabon malami wanda ƙawata tamin hanyarshi ya iya aiki,aikin shi kamar yankan wuƙa yake,idan ta tashi sai muje a san yadda za’ayi”