HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Yawwa momyn mu shiyasa muke sonki kuma muke alfahari da ke allah yabar mana ke.”

Murmushi tayi ya ce”Hm dole na so ku,ban yarda da rashin nasara ba,shiyasa zanyi komai akan nasararku…..

.
[12/22, 5:26 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/22, 5:28 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
Page 12

…………………………………………………………………………………

???? *FALALAR* *KWANCIYA* *DA* *AL* *-* *WALA* .

_Hadisi ya inganta daka *Annabi Sallallahu Alaihi wasallam* yace:_
*→(من بات طاهرا بات في شعاره ملك فلم يستيقظ إلا قال الملك :اللهم اغفر لعبدك فلان فإنه بات طهرا)*
…•
_( Wanda ya kwanta da alwala, mala’ika zai kwana acikin mayafinsa bazai gushe ba yana masa Addu’a yana cewa “Ya Allah ka gafartawa bawanka wane domin ya kwanta yana da tsarki (alwala)”_
…•
_*Abdullahi bin Mubarak yaruwaitoshi acikin littafinsa “azzuhudu” (64) ta hanyar hasan bin Zakwaan, Ibnu hibbaan ya fitar dashi acikin saheeh dinsa (1052).*_
…•
_Saidai isnadine mai rauni, domin Alhasan bin Zakwann imamu Ahmad ya raunatashi da ibnu ma’een da sauransu.._
…•
_*Duba Mizanul I’itidali (1/489),*_
…•
_Amma yanada wani hadisin dake mara masa baya wanda imamul dabarany yaruwaito acikin *Mu’ujamul kabeer (13620) da waninsa.*_
…•
_Hadisin dake goyawa wannan baya wanda imamu dabarani ya ruwaito daga Abdullahi bn Umar Allah ya kara masa yarda shine wanda manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:_
*→”( طَهِّرُوا هَذِهِ الْأَجْسَادَ طَهَّرَكُمُ اللهُ، فَإِنَّهُ لَيْسَ عَبْدٌ يَبِيتُ طَاهِرًا إِلَّا بَاتَ مَعَهُ مَلَكٌ فِي شِعَارِهِ لَا يَنْقَلِبُ سَاعَةً مِنَ اللَّيْلِ إِلَّا قَالَ: اللهُمَّ اغْفِرْ لِعَبْدِكَ فَإِنَّهُ بَاتَ طَاهِرًا )*
…•
_Ma’ana”ku tsarkake jikinku Allah zai tsarkake ku, domin babu wani bawa da zai kwanta da alwala face mala’ika ya kwana tare dashi acikin mayafinsa babu wani lokaci a cikin dare da zai shude face wannan mala’ika yanai masa addu’a yana cewa: ” ya Allah ka gafarta wa bawanka domin ya kwanta da alwala”._
…•
_Wasu malamai Suntafi akan hadisine kyakkyawa saboda wasu hadisan da suke mara masa baya._
…•
_Duba *”Attargeebu wattarheeb, na munziry (1/231) da muj’ma’ul zawa’id na haisami (1/226) da Sil-sila saheeha na Albany (2539), dabarani yaruwaitoshi acikin Ausaad (5087) daka ibn Abbas*_
…•
_isnadan hadisin dukkansu babu wacce ta kubuta daka wata tawaya saidai idan ka hadasu wani yana karfafa wani saboda haka Albani ya hukunta hadisin da cewa kyakkyawane idan ka hadashi da waninsa. *Saheehul Targeebu wattarheeb (599).*_
…•
_*Falalar karanta Suratul Mulk*_
_Falalar karanta Suratul Mulk (Tabarakallathi biyadihil Mulk) tazo adunqule sannan kuma Falalarta tazo kafin kwanciya bacci a kebance, *Imam *Tirmidhiy yaruwaito hadisi (2891) da Imam Ahmad a cikin musnad nasa hadisi na (7915) daga Abu huraira Allah ya kara yarda dashi* daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Akwai wata Sura mai aya talatin a cikin Alqur’ani, ta ceci wani mutum har aka gafarta masa, itace Suratu Tabarakallathi biyadihil Mulk), Sheikh Albani ya ingantashi a cikin sahihul Tirmidhiy “_
…•
_*Tirmidhiy ya ruwaito hadisi (2892) da Imam Ahmad (14249) daga Jabir Allah ya kara masa yarda”* Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya kasance baya barci har sai ya karanta Alif laam miim Tanzeel da kuma Tabarakallathi biyadihil “Sheikh Albani ya ingantashi a cikin sahih sunanul Tirmidhiy._
…•
_Abinda yafi shine mutum ya karanta Suratul Mulk kafin ya kwanta barci a kowane dare, saboda irin yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya yi, da zai karanta ta a sallarsa ta isha’i to da hakan ya isar masa, saboda gamewar zancen Hadisin farko da ya zo game da ceton Suratul Mulk ga wanda ya karanta ta, domin lokacin karanta ta ba a iyakance shi ba._
…•
_Saidai ba’a shar’anta dawwama akan karanta ta cikin sallar isha’i ba, domin dawwama akan karanta ta nau’i ne na iyakancewa, ita kuma iyakancewa a cikin Ibada bata kasancewa face da dalili, amma don anyi haka lokaci bayan lokaci to babu laifi._

……………………………………………………………
” Ni Naufal yanzu shikenan rayuwata a haka zata tabbata cikin rashin ƴanci,sai abinda Sabreen ta ke so zanyi,ba’amin adalci ba,an aura min ita bata son ta amma ba za’a gyale ni ba,yanzu ya kenan idan naje ma Dady da maganar auran Haulat..

Da ƙarfin gaske zuciyar shi ta fara bugawa,zufa na ƙeto mishi ta ko’ina a sassan jikin shi,kamar motor ba AC a cikin ta.

Da gudun gaske yake jan motor kamar wanda zai bar ƙasa,cikin ƙanƙanin lokaci ya iso unguwarta su,yana zuwa gurin get ɗin gidan mai gadi ya buɗe mishi gidan da sauri ya kunna kai,bai kai ga gurin da ake yin parkin ba ya tsaida motor ya fito.

Har yana harɗewa dan saurin gurin isa cikin falon,yana isa ya fara kalle-kalle yaga Dady bai ganshi ba,a kwance ya hango ta akan 3 seater ko ɗan kwali babu akan ta,hankali kwance take kallonta tana murmushi tana jin daɗin kallon ga juice a gaban ta.

ƙarasawa yayi kusa da ita bata san ya shigo ba sai ji tayi ya ce,”Sabreen ina Dady har ya koma ne?

Hankali kwance ta juyo ta kalle shi tana murmushi ta ce,Wani Dady?

“Wani Dady? tambayata kike yi wani Dady.”

Ɗan yaƙuna fuska tayi ta ce,”Eh!

“Haba Sabreen me kika maida ni,ki kira ni ki ce min Dady ya so yana jira na,kuma shi ne kike tambayata wani Dady.”

Ta sigar da yayi maganar ya ɗan bata tausayi abinda tayi niyyar ce mishi ta fasa.

“Ba Dady ba ne,Dady bai zo ba,bana jin daɗi ne kuma ina jin tsoro shiyasa na kira ka dan ka dawo nasan idan ba hakan na ce maka ba,ba zuwan zaka yi ba.”

Zama yayi kan kujera ya dafa kanshi, “Sabreen wai dan allah meye matsalarki da ni ?

kai tsaye ta ce mishi “Haulat karka je gurinta ka daina sonta”

“Na so wa? naje gurin kuwa? tashi tsaye yayi kusa da ita ya matsu ,yasa hannuwan shi ya ɗago ta daga kan kujerar da take zaune ,suka fuskanci juna sosai har numfashin su yana cuɗanya da na juna,mayun idanuwan shi ya zuba mata,yakan rasa dalilin da yasa idan ya fara kallonta baya so ya tsaya,kawata-kawata.

duk fitsara irin ta Sabreen saida ta sauke kanta kasa yau kawai yai mata ƙwarjini idanuwan shi suka tsorata ta,mutsu-mutsu ta fara yi alamar ta gaji da tsayuwar.

cikin wata irin murya ya ce”Na so ki! na zo gurinki ɗan iska fa kike ce min”

“am.. ni…nifa..”

“ke fah me?

“Ni bance ka so ni ba,amma karka so Haulat”

“Meyasa?

“Malama ta ce!

Tura ta yayi ta faɗa kan kujerar” Whay? Sabreen meyasa kike son taƙura rayuwar mutane ne,kin san irin son da haulat ke min kuwa? ko kina ganin zaki iya hanani son Haulat,kinyi kaɗan Sabreen,ina son Haulat ita ce muradin Raina da ita zan rayu zan aure ta,idan kuma kina ganin zaki iya hanani to mu zuba mu gani.”

Yana faɗa ya juya zai hau zama har ya taka matakalar ta ce ,”Ya Naufal!

Chikk ya tsaya,ƙarasawa tayi idan yake jin ta a bayan shi yasa shi juyowa.

“Hm ni Sabreen muhammad sai na sa ka mata da waye Haulat ,ko sunanta sai ka manta da shi .” cikin izza da ƙwarin gwuwa tayi maganar.

Dariya ta bashi sosai,ya kalleta yana dariya maimata abinda ta faɗa yayi,”Ke Sabreen muhammad mai taƙama sai kin saka na manta da Haulat.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button