HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Na chanja taya zan chanja ina ban chanja ba niɗin ce dai ƴar aljanna shalelen Hajia”,a zuciyarta tayi wanan maganar.

“Kiyi magana Sabreen ko da gaske kin chanja ne.”

“Hmm ba zan chanja va,farrah ni ɗin ce dai..

“Na sani ba ƙaramin abu ne zai iya chanja ki ba,amma naga kina dabur-dabur ne,ko maganar ce kika rasa ta inda zaki faɗa min?

“Eh Farrah na rasa ta inda zan fara ne.”

“Sabreen ki natso ni ƴar uwarki ce karki ji komai ki gayamin kai tsaye abinda ke ranki.”

Kallon Farrah Sabreen tayi ta ce,”Kin san yayah ba ni yake so ba akwai wacce yake so,to shine nake son ya manta da ita,kuma bansan ta inda zan fara ba.”

Dariya farrah ta fara yi sosai harda kwanciya kan gadon.

Rai a ɓace sabreen ta ce,”meye haka farrah kin abinda bana so kenan ina magana ana dariya.”

Cikin dariyar farrah ta ce,”Ni mamaki ba kika bani.”

“Mamaki me kefah banza ce.”

“Ba dole ba wai ƴar aljanna ke tambayat yadda zata sa mutun ya manta da wani,bayan kin fini sani.”

Tsaki Sabreen tayi “da na sani da zan kira ki ne.”

“Kin sani savreen baki na tuna miki.”

Zaune ta tashi da tsaida dariyarta ta ce”Sabreen kin iya kiss kisisi shagwaɓa duk wani salon jan hankali kin iya,to da su zaki yi amfani ki sa yaya ya manta da budurwar shi cikin ƙanƙanin lokaci,Sabreen ba zaki sha wata wahala ba gurin mantar da shi akan ko wacce mace domin kin samu dama duk yadda kika yi da shi dole yayi ko da bai so ba,kinga wanan babbar dama ce,idan kina so ki mantar da shi akan ko wacce mace dole sai kin kusance shi kin jashi a jiki kin nuna mishi kulawa.”

“Ba abinda bazan iya yiba idan har sai sa ya manta da malama Haulat.”
A zuciyarta tayi maganar.

Hannuwanta Farrah ta riƙo cikin kulawa ta ce,”Sabreen kina son yaya ya manta da budurwarshi.”

“Sosai ma kuma cikim ƙanƙanin lokaci.”

“Yawwa to bari na gaya miki abubuwan da na sani,ya zama dole ki tausassa kalamanki nasan ba’a ɗaki daya kuke kwana ba ,to kiyi yadda zaki yi ku dunga kwana ɗaki daya shi,kuma ki hana shi zuwa gurinta,ki kusance shi sosai duk inda yaje ki bishi,kissa kisisi na yaudara shagwaɓa ki dinga mishi ba zai baki wahala,kin gane inda na nusa.”

“Kina ganin hakan zai yasa ya manta da ita kuwa?

“ki yarda da ni tabbas idan kika yi hakan zai manta da ita.”

“To bari na jaraba.”

“Sabreen karki ce haka lallai ki ɗauka hakan zai mantar da shi ita.”

Murmushi Sabreen ɗin tayi dan jin daɗi “Hmm ni fa ƴar aljanna cikin ƙanƙanin lokaci zan saka ya manta da ita.”

Dariya Farrah ta ce,”Yaya fa an shigo hannun manya,”

haka suka cigaba da firar su cikin jin daɗi da nishaɗi da kula da junan su.

~~~~~~~~~~~~~

Bayan ya fito daga bayin ya shirya tsabba ya ɗauko wayar shi pic ɗin Haulat yake kallo ya kasa gane dalilin da yasa yafi jin daɗin kallon pic ɗin Savreen akan Haulat,yana cikin kallon pic ɗin kiranta ya shigo ya daɗe yana kallon sunan da yasa mata,kafin ya ɗau waƴar ita ta fara magana.

“Hello dear!

Saida ya lumshe ido dan dalin muryarta.

“Ya kike?

“Ba lafiya ba,meyasa Naufal,”cikin raunanniyar murya tayi maganar.

Hankalin shi ya tashi jin yadda take maganar a ruɗe ya ce,”Kiyi hakuri Haulat kin san ina sonki ba zan iya miki haka ba,Dady na ne ,amma kin san ina sonki ke ce ra’ayina.”

Gaba ɗaya farinciki ya mamaye ta duk wani baƙinciki ya kau,ji take kamar bat taɓa shiga cikin ƙunci ba.

Cikin wata irin sigar da ke ɗaga mishi hankali ta ce,”Na sani Naufal ka kwantar da hankalinka bana son ka shiga damuwa.”

Yadda tayi maganar ya kashe mishi har tsigar jikin shi saida ta tashi.

Lumshe ido yayi ya ce,”Tnx dear nasan zaki fahimta,karki damu zanje gurin hajiya babba(Wacce ta haife momy) akan maganar auran mu nasan zata samu dadyna da maganar kuma nasan zai aminci.”

Ko kaɗan Haulat bata son ayi mata maganar aure dan baya ganta,shiyasa bata ji daɗin mgnr shi ba,tadai ji daɗi da ya nuna mata yana son ta.

“Yaushe zaka zo,?bani da lafiya fa!

“Subhananllah meye sa meki?

“Hm ciwon son ka da kishinka tun ranar ina nan kwance sai yanzu ta tashi.”

Saida yayi jimm shi ya yarda da son da haulat ke mishi na gaske ne,cikin sigar tausayi da ban baki ya ce mata,”Sorry zan zo yanzun nan,ba amfanin wahalar da kanki domin ni naki ne ke kaɗai ba wata maccen da nake so ,ke ce muradi na ra’ayina.”

Gaba ɗaya ya kashe mata ji da kalamanci waɗan da suke ƙara narkar da ita,cikin murjar jan hankali ta ce”Okkk sai ka zo dear.”

Ta katse wayar,daman ya gama shirin shi tsaba key motor kawai ya ɗauko sanan ya sauko ƙasa,a falo ya haɗe da su Sabreen da farrah.

Farrah tana ganin shi ta miƙe ta ce,” ina wuni yaya?

“Lafiya lau ya hajia?

“Lafiya lau tana gaida ku.”

Kallon Sabrewn farrah tayi ta ce,”To zan tafi sai anjima.”

“To ki gaida momy da Dady.”

“Zasu ji.” tana faɗa ta wushe abinta.

Shi ma kai yasa zai fita da sauri ta ce,”Yaya ina zaka je,zan biki tsoro nake ji.”

Kallon ta tayi kamar zaiyi mgn sai ya fasa ta ya juya abin shi.

“Yaya Naufal!

Banza yayi da ita ya fice abinshi.

Wani ƙululun takaici ya kama cikin faɗa da ɗacin rai ta ce,”Ni nake ma magana kayi banza da ni,wllh yaya kayi sa’a dan ina son cika kudiri na ,amma da ba zan yafe maka ba,yanzun ma ba yafewa zanyi ƙafa zan ɗaga ma,kuma ba zanyi fushi ba duk abinda zaka min har sai na mantar da kai waye Haulat a rayuwar.”

Kamar yana gaban tayi maganar tana gamawa ta hau sama cikin fushi.

~~~~~~~~~~~~~

Momyn su Haulat muguwar macce bara ilimi da imani bin bokaye ɗabi’ar gadon gidan su ne,Dadyn su haulat mutum ne kamili mai rikon addini da sanin ya kamata ɗabi’a ƴan boko bata dame shi ba,tun kafin suyi kuɗi,kullum burin shi yaga yaran shi suna riƙo da addini,yana kwaɓa musu idan suka kauce hanya,wanan dalilin yasa momyn mai suna balaraba ta asirce shi,sai yadda tayi da shi baya iya yin komai daga ita har yaran basu jin tsoran shi ko kaɗan.

Haulat ita ce babba wanda yanzu tana da shekara ashirin da shidda a duniya,tun tana candy ta fara lalewa da bin maxa lokaci har jami’a,halayen ta iri ɗaya sak da na mahaifiyara,har tafi mahaifiyar ta taƙama fariya gadara uwa uba wulaƙanci da alfahari ,Salma ita ka bi mata ita ma halin su ɗaya,sai auta sakina baiwar allah mummuni ga tausayi saboda halinta yasa basu sonta ko kaɗan dan tana faɗa musu gaskiya.

“A lallai kinji sauƙi irin wanan waahe baki haka.” cewar momyn haulat wacce ta shiga ɗakin haulata ɗin dan duba jikin ta.

Ƙara faɗaɗa fara’arta tayi ta ce,”Eh momy naji sauƙi,Naufal zai zo gani na yanzu.”

“Kunyi waya ne? ki son shi sosai,sai yaushe zamu je gurin bokan.?

“A’a tukun na dai,yana so na sosai momy.”

“Hmm haryanzu da sauran ku.”

“Ba haka ba ne,momy nafi son irin wanan soyayyar da yake min nafi jin daɗin ta,yanzu kinga indan muka je gurin bokan avin sai koma kamar bin umarni da dole za’ayi mishi akai na,”

“to ita yarinyar fah zata iya raba ki da shi.”

“No momy ba zata iya ba,ni yake so ba ita ba,ni ce ra’ayinshi ba abinda zata iya.”

“Haulat kenan ina nan zaune zaki zo ki same ni,bari naje mu fara shiri kafin ya iso”.

~~~~~~~~~~~~~

“meyesa zan mata haka? akwai haƙƙin ta mai nauyi akai na,ga alƙawarin dadyn ,yanzun idan tayi fushi ta gayawa hajia fa,ita kuma ta gayawa dady.”

Zuciyar shi ta fara bugawa tsoro ya kama shi ,”Sabreen bata da haƙuri zata iya gayawa hajia,nima ban kyauta to yanzu ya zanyi? ya zanyi ko na kirata ne?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button