NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Jikin shi na rawa ya ɗago wayar,tsakii ya ji tuno bashi da numberta gashi ya goge list ɗin kiran wayar gaba ɗaya,lokaci ɗaya yaji ranshi ya fara ɓace sai jan zaki yake yi,a hankali ya raba ambaton allah,har ya samu zuciyar shi ta fara sanyi.
Saida ya biya yai mata siyayya kala-kala kayan ci harda kayan sawa ya siya ba ita kaɗai ba harda na ƙannanta,sanan ya nufi unguwar ta su,kamar yadda ya saba shiga da motor shi cikin gidan yanzu ma ciki ya shigar da ita.
Yana isowa harabar gidan ya hango salma sa sauri ya kauda kai daga barin kallonta,gajeran wando ne iya cinya a jikin ta sai ƙaramar riga mai hannun bireziya,ba ɗan kwali a kanta.
Tunda ta hango shi ta fara faɗin,”A dole dole aunty haulat ta ruɗe irin wanan kyau ga izza ga kwarjini,cikin rangwaɗa ta iso gaban shi tana ƙare ma halitta shi kallo,cikin muryarta mai kama da na Haulat ta ce,”Hi sannu da zuwa.”
tun kafin ta ƙaraso gurin shi ya saƙa bakin glass,ɗagowa yayi amma bai yarda ya ƙara kallon ta ba ya ce,cikin iyayi da kilibibi da ƙarya harshe da ba kowani harafin haƙƙin,”Hi!
“Waw ka haɗu over Naufal.” ta faɗa a ranta haɗe da kafe shi da ido.
“Akwai kaya a bayan motor.”
ya ƙara faɗa ita kuwa yana ƙara birgeta,yadda yake hausar kai idan ba haifaffan ɗan ƙasar hausa ba ne,sai ka ce wani yare yake yi.
ɗan aikin gidan ta kwalla ma kira ,da sauri ya zo jiki na rawa,tana ganin kayan ta ƙara ruɗewa.
Duk da kasancewar ita ce a gaba shi yana baya,amma bai ko kalle ta kanshi a ƙasa har suka isa cikin,falon bai taɓa shiga ba yai yau,wani irin ƙamshi me kama da wari ne ke tashi a falon,daman ya lafiyar giwa balle tayi hauka????sai ƙamahin nan yana dokan hancin shi ta,fara tsotsoke hancin yana taɓe baki yana yamutsa fuska kamar wanda ya shiga cikin masai????
Momy haulat na shigowa falon ya ɗago kai ya kalle ta,ai da sauri yai ƙasa da kanshi zuciyar shi na bugawa,ita ma gajeran wandon ne a jikin ta da ƙaramar riga gata ba ƙarama ba.
Har ƙasa ya ɗuka yai gaida ita kamar yadda ya saba kaida manyanshi.
Ya birgeta sosai ga tarbiyya,to ashe dai ƴan isaka suna son mutum mai tarbiyya,a ranta ta ce,”Ah dole Haulat ta ruɗe,gaskiya zan matsawa haulat mu tashi tsaye dan irin so mugun riƙo ake mu su.
A fili ta ce,”Salma kai shi ɗakin Auntyn ku.”
Wani irin banbara ƙwai yaji ,wai namiji da suna hajira????,mamaki ya bala’in kama shi”wai akai shi ɗakin haulat.” ,tunani ya fara yi wacce irin al-adace wanan.
Da ƙyar ya iya tashi yabi bayan salma dan tsavar kunya,tafiya kaɗan takai su ɗaki.
“Ka shiga nan ne.” salmar ta faɗa ta juya,ya daɗe tsaye a bakin kofar,sanan ya tura ,yana turawa ta buɗe ,yana shiga yaji an rungume shi.
“Sannu da zuwa.” ta faɗa cikin wata irin siga.
Yarrr gashin jikin shi ya tashi,kallon ta yayi ai tuni zuciyar shi ta fara bugawa wanda hakan ya haufar mishi da mutuwar jiki.
Janyo shi tayi zuwa kan gadon shi ,kamar raƙomi da akala,kuma wa tayi ta rufe kofar sanna ta dawo kan cinyar shi ta zauna,cikin salo ta fara shafa fuskarshi akan lips ɗinshi ta tsaya wasa ta fara yi da su,sanan ta haɗe su hot kiss ta fara mishi,daman an daɗe va’a gamo ba ,ai tuni naufal ya ruɗe ya fara maida raddi,kan ku ce me sun fita haiyacin su,tura shi kan gado n tayi ta kwantar shi koƙarin cire mishi wando ta fara yi…….
Waiii yau ga rubutun wani iri hakan ya faru ne saboda nayi cikin gaggawa,saboda wanda nayi cikin natsuwa har read more biyar ya goge,ban yi niyar kara yi ba amma kuma nayi.
To fah fans me zai faru a ɗakin Haulat,dan naufal yayi nisa?
shin Sabreen zata cin ma burinta kuwa na son raba shi da haulat ɗin shi.?
To idan burin sabreen ya ciki Wani irin mataki haulat zata ɗauka akan ta?
Maganar zuwa gurin bokan da momyn haulat ɗin zata ƙara ma haulat ɗin zata yarda?
Idan ta yarda wa za’a ma asirin tsakanin Naufal da sabreen kuma wni irin Asiri za’a yi ma???
.
Sir Anas!
[12/22, 5:28 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/23, 1:52 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
Page 13
……………………………………………………………
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{BA ZAKU WADATAR DA MUTANE TA DUKIYARKU BA, AMMA HALAYENKU SUNA WADATAR DA SU.}*_
°
“`[Sahihut Targib;2661]“`
~~
_Wannan hadisin yana nuna mana cewa duk yanda zaka ba ma mutane dukiyarka to ba zaka iya wadatar da su ba, amma in kana da kyawun hali, kana mu’amalantar su da ita to zasu wadata da wannan kyawun halin. Allaahu a’alam._
“`Allah ta’ala yasa mudace“`
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
__________________
Cikin zafin nama Naufal ya janye jikin shi ya miƙe tsaye,yana wani irin numfashi,koƙarin buɗe baki yayi magana yayi,amma ya kasa bakin ma bai iya buɗe shi ba,cikin kasala da rawar da jikin shi ke yi ya gyara jikin shi ya nufi kofa zai buɗe har yakai hannu Haulat ta riƙo shi,juyowa yayi ya kalle ta da rinannan idanuwan shi,ita kanta kasa mishi magana tayi kuma ga bakinta yana son cewa wani abu amma ta kasa,girgiza mata kan shi yayi alamar bazai tsaya ba,sakancewar jikin ta ba ƙwari yasa ya janye hannuwan shi ya fita.
Yana isa falon ba kuwa yaji daɗin hakan sosai dan ko wani baya son ya ganahi a irin wanan yanayin da yake ciki balle su iyayen ta.
Ta gyar ya iya jan motor ya fita daga cikin gidan,yana fitowa daga gidan ya fara gudu kamar wanda za shi bangon duniya,cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gidan su,yana zuwa mai gadi ya buɗe mishi ya shiga,a tsakiyar gidan yayi farkin ɗin motor ya fito.
Ba kowa a falon ko da ma akwai ba zai gane ba tunda halin da yake ciki,kai tsaye ɗakin shi ya nufa,bai kula da Sabreen ba wacce ke kwance akan gadon shi,ya faɗa danne tan da yayi ne yasa tayi ƙara.
“Waiyo Yaya baka ganni ba ne zaka danne ni?
Tashi yayi yana kallon ta da rinnanun idanuwan shi,”Mai ya kawo ki?
“Meya kawo ni ɗakin miji na kuma yaya.”
Jin amsar da ta bashi ya tabbatar mishi da taji abinda ya faɗa,dan bai yi tunanin zata ji ba.
“Mijin ki! ya faɗa cikin dakushashar muryar shi.
“Eh ko kai ba miji na ba ne.”
Lumshe ido kawai yake yi yana kallon ƙaramin bakin ta,da fararan idanuwan ta masu hasken gaske kamar auduga.
Ya shagala da kallon ta,kamar ya janyo ta jikin shi yake ji,”Naufal kana da halal ɗin ka fah,to meye kake kai kan ga haram.” shi da zuciyar shi suke wanan maganar.
“Kuma daga yau kullum ɗakin miji na zan dunga kwana.”
Cikin kiss da kisisi na da shagwaɓa ta ke maganar,sai zazzaƙar muryarta ta ƙara zaƙi.”
“Sabreen!
Ya faɗa cikin wata irin siga wacce ta wuce ya kira hakan da sha’awa saidai shauƙin so.
“Zaki iya kwana da ni?
“Eh zan iy….
Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya janyota rungumeta yayi,dumm dumm zuciyar shi ta fara bugawa da mugun ƙarfi wanda hakan ya haddasar mishi da kasala.
ƙoƙarin janye jikinta ta fara yi,amma ta kasa dan ba ƙaramin runguma yayi mata ba,ƙoƙarin haɗa bakin shi da tana ya fara yi amma ya kasa dan taƙi natsuwa gashi baya da ƙarfi
“Ahnn waiyo allah hajiata ka sake ni.”
Tura ta yayi kan gadon ya tashi a fusace ya faɗa bayi ,ranshi ya ƙuna,ya daɗe yana zuwa kanshi ruwan sanyi ko yaji sanyi a ranahi,amma ya kasa ji,yana mamaki irin rayuwar da yake ciki haram na binshi halak na ƙin shi.