NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Ohhho dai kuma sai na kwana a ɗakin nan kamin hakan ne dan karna kwana ko ,to sai na kwana.” tana maganar tana murguɗa baki kamar yana kallon ta,tashi tayi tai kicin copee da haɗa mishi ta dawo har lokacin bai fito daga bayin ba.
~~~~~~~~~~~~~
Bayan farrah ta dawo gida Momy ta tambayeta mai ya faru,ƙarya tai mata, akan cewa ta tambaye ta ne ta koya mata yadda muke yin kunun gyaɗa ranar da muka kai musu taji daɗin shi kuma shi ma yaya irin shi yake so.
Momyn tajo daɗi sosai ta fara tunanin ya fara son ta.
Zaune suke a ɗakin su Dady yana kan gado ita kuma momy tana gaban mirrow tana cire ɗan kunnayen ta.
“Hajiata uwar gida.” Dady ya faɗa yana murmushi.
Bata kalle shi ba ta ce,”Na’am abban Naufal.”
“Ya kamata su tafi honeymoon ko?
“Eh gaskiya daman ina son nayi maka maganar gashi sun shaƙu da junan su.”
Washe baki dady yayi daman yasan auran Sabreen da Naufal alkairi ne,yasan hakan zata kasance kuma ya saka a ranshi ko ba daɗe sai Naufal ya musu godiyar haɗa sun da aka yi.
“To amma wacce ƙasa kike ganin ya kama ta su je?
“wacce suke so.”
“A’a bana son su san da maganar sai ranar.”
“To zanyu taya zaka gane wacce ƙasa suke son zuwa.”
“Karki damu nasan yadda zanyi.”
~~~~~~~~~~~~~
Ganin ya daɗe bai fito ba yasa ta fara gyara ɗakin duk da kasancewar Sabreen bata aikin komai a gurin hajia hakan bai hana ta iya abubuwa ba girki,gyran ɗaki hatta wanki tana yi,bata da ƙyuya ko kaɗan.
Yana fitowa hanci shi yaji wani irin kamshi mai kwantar da hankali lumshe ido yayi ya buɗe,ƙarewa ɗakin kallo yayi kamar ba nashi ba komai tsaf-tsaf
“Wai mijina ashe haka kake daɗewa idan kana wanka.”
Zuciyar shi ta fara amsan saƙon muryata sanan kunnuwan shi.
Kallon shi ta fara tsabb da sauri tai ƙasa da kai.
ba komai a jikin shi zai towel shi ma ɗan ƙarami ne.
ganin irin kallon da ta mishi yasa shi yin murmushi,lokaci ɗaya farinciki ya mamaye shi wanda bai san dalilin faruwan hakan ba.
Bai ce mata komai ba ya wuce gurin durowar ya buɗe zai naime kayan da zai saka.
“Ah nima daga yau zan ɗinga daɗewa a bayi gurin wanka,ai sai yanzu na gane ace daɗewan da kake yi ne yasa ka zama fari.”
Dariya ta kuɓuce mishi mai ɗauke da jin daɗi juyowa yayi ya kalle ta ,ita ma murmushin dariyan take yi.
“To bari naje waje ka gama saka kayan”,tana faɗa ta fita a ɗakin.
Murmushi ya ƙara yi,Sabreen tana burge shi,bai san lokacin da ta fara burge shi akan komai tana ba,ƙanana kaya ya saka mara su nauyi, sanan ya sha mai da turare,kan gadon ya koma ya zauna barici yake ji.
Ɗakin ta shigo fuskan nan ɗauke da annuri,”Ka gama shiryawan gaskiya kayi kyau sosai.”
jin shi kawai yayi ya ce,”Tnx ke ma kinyi kyau.”
Washe baki tayi,”Thanks my miji!
Murmushi yayi,yana jin daɗin sunan mijin da take kiran shi da shi.
copee ɗin ta miƙo mishi,”gashi ka sha zaka ji daɗin shi,kuma zai saka ka kayi barci ka huta.”
Hannu ya miƙa ya amsa yana ɗan murmusawa.
“Yawwa miji na!
Sha yayi yana lumshe ido yana jin zuciyar shi wasai,zama tayi a gurin har ya shanye,ta sama kofin.
“Yaawwa sai ka kwanta ka huta.”
Amsar umarnin ta kawai yake yi,yadda ta ce hakan yake yi.
Lamo yayi har barci ya ɗauke shi,tana zaune a gurin tana kallon shi.
Ƙarar wayar shi taji da sauri ta ɗako wayar zumbur ta miƙe ganin hoton haulat saida taji ani abu a ranta,kallon shi tayi sanan ta fita da sauri.
“Hello malama ta! har nayi fushi da ke,akan ƙin zuwan ki ɗaurin aure na alhalin an gaiyaci dukkan mutanan da ke garin abuja da ma kewayan ta.”
Haulat wacce ke zaune akan kujera jin muryar Sabreen yasa ta miƙe zumbur.
“Naufal!
“No malama ta,miji na,mijin ɗalibata zaki ce.”
“Sabreen!
“Na’am malama ta,zan zo ni da mijina na miki godiya dan da bandan ke ba da ban aure naufal ba,ko kin manta kike ce ina son aure aka gayawa iyaye na.”
Saida ta sauƙe gajerar ajiyar zuciya sanan ta ɗaura da faɗin,”Malam ta,jahili daƙiƙi ɗan kauye iri na da aura,ko ɗan gaye mai aji mai ilimi da kyau na aura wanda ko wacce macce take son rayuwa da.?
“Gaya min dan na kasa ganewa,laah ko shi ne wanda malamata ta ke mafarki akan shi?
“Malama ta! ya kike yi shiru ,ki zauna kinji ki natsu,ni Sabreen ba tsararki ba ce,yawwa kuma ki fita harkar miji na,baki da ikon juyamin shi tunda ba ɗalibin ki ba ne,ina fatan kin gane.”
“Ƴar aljanna ke dawa kuma?
Ɗagowa tayi ganin hajia ce yasa ta katse wayar a ranta ta ce,” *Ni* *DA* *MALAMA* *TA*.
A fii kuwa dariya tayi ta faɗa kan hajiar tana ihuu tana faɗin,”Oyoo ooyoo hajiata.
“Ba wani bayan kin manta da hajiar aure daɗi ko?
Cikin shagwaɓa ta ce,”Kai hajia ba wani daɗi.”
“To ya kike? ina ta kewar ki shiyasa na ce bari na zo na ganki.”
“Nima hajia ai nayi kewarki sosai.”
Fira suka shiga yi sosai da sosai cikin so da ƙaunar juna.
******
Ɓangaran Haulat kuwa tunda sabreen ta katse wayar ta fasa ihuu,mai rikitar wa.
“Lafiya kike haulat mai ya faru?
A ruɗe momyn ki tambayarta wanda ihunn na ta ne ya fito da ita daga ɗakin ta.
“Waiyo allah na momy na shiga ukku dan allah mu tafi gurin bokan nan.”
“Duk da basan abinda ya faru ba,nasan sai irin hakan ta faru,ke ce banza bara wayau ai.”
“Sabreen sai na yi ajalinki walahi sai na kashe ki!!
“Mu tafi yanzun nan.”
“Matsalar yau baya sauraran mutane sai gobe.”
“Ɓakin ciki sai iya kashe ni kafin goben ba zan iya hakuri zuwa gobe ba.”
“Tun ranar da nake miki magana kika ƙi saurarata, amma harda shi zamu haɗa.”
“No momy bana son a mishi asiri.”
“Giyar so ko!,to shi ne wanda ya kamata ayi wa asirin ma ba ita ba.”
“Momy baya da matsala ina son shi,soyayyar da yake min ita nake so,bana son a saka shi dole da bin umrnin.”
“Hmm haulat kenan ina fatan zaki gane ki dawo hanya.”
~~~~~~~~~~
Bangaran Naufal kuwa tunda ya kwanta ya faɗa duniyar mafarkin da ya saba yi,wanda ya kasa bin jikin shi,dan kullum abin sabo yake zuwar mishi.
Kamar yadda ya saba tashi a irin lokacin da tare barin shi yau ma hakan ne,farkawa yayi zuciyar shi na zafi da ƙuna ga zufa ta mamaye shi kanshi a ƙasa.
Sintar muryar ta yayi tana faɗin,
“Miji na ka tashi?
ɗagowa yayi suka haɗa ido,wani iri yaji ,ita kanta kasa tai da kai,”Hajia ta zo tana na jiranka,har ta wuce baka tashi ba,daman yanzu zan tashe ka dan lokacin sallah yayi.”
Lumshe rinannun idanuwan shi yake yi,ya kasa daina barin kallon ta.
Ganin kamar ita yake kallo yasa ta fara kame-kame,”Lokaci yana tafiya fah!
“Ko barcin bai ishe ka ba ne?
Dariya yayi dan sanan ya tashi ya shiga bayin,yana shiga ta ƙara gyran ɗakin tayi tsaba sanan ta fashe shi da turare.,ɗaukar wayar shi tayi ta kashe sanan ta fita indomi ta haɗa mishi da kyau sai jus ta kawo har lokacin bai fito ba,zama tayi a bakin gadon.
Yana fitowa yaji ƙamshi me kwantar da zuciyar,idon shi suka sauka akan sabreen wacce ke zaune akan gadon tana wasa zuben da yake hannunta,ya daɗe yana kallon ta,wani iri yake ji a ranshi a duk lokacin da yake kallon ta,yadai kasa gane wani irin abu ne.
Ɗago kai tayi suka haɗa ido kai tai da kai da sauri,”Ka ƙara haske yanzu kawai.”
Murmushi yayi,”Waya gaya miki wanke ke saka mutum yayi haske?
“Gani nayi.”
“Gurin wa?
“Gurin mijina kuma yaya nah!
Dariya yayi mai ɗauke da murmushi ,yana jin daɗin sunan da take kiran shi da shi”mijina”
ƙarasowa yayi har kusa da ita wani towel ɗin zai ɗauka ya goge jiki da shi,kuma yana bayan ta.