HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

kaff da ita ya matsu ya miƙe hannun shi zai ɗauko towel ɗin jikin su ya haɗu da na juna,yarr dukkan su suka ji ,ruwan girjin shi ya zuba a fuskarta,wani irin sanyi taji har zuciyarta,tsintar kan shi yayi da son rungumeta, faɗawa yayi kan jikinta ya rungume ta,wani irin baƙon yanayi ya fara ziyartar zuciyar shi,mutsu-mutsu ta fara tana kokarin janye jikinta,”Ka gyale ni bana so.” ta faɗa.

Zuciyar shi ta fara buguwa da ƙarfin gaske,wanan maganar tuno mishi da mafarkin shi tayi,kafin ya ƙarasa tunanin shi,ta ƙwace jikin ta,barin ɗakin tayi da sauri ta barshi da bugun zuciya….

.
Sir Anas!
[12/23, 1:52 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/23, 2:16 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

Page 14
………………………………………

*Addu’a Ga Wanda Yayi sabon Aure*

بارَكَ اللَّهُ لَكَ، وَبَارَكَ عَلَيْكَ، وَجَمَعَ بَيْنَكُمَا فِي خَيْرٍ.
Barakal-lahu lak, wabaraka ‘alayk, wajama’a baynakuma fee khayr.

Allah Ya sanya albarka a gareka, yayi maka albarka kum aya hada tsakaninku da alheri.

Wanga page na ku ne iyalan bintu Ahmad ,da tana jamcy ina yinki sosai na gode da kulawar ku,ku sha zaman ku ,ku huta batula tana yinku fiye da tunanin ku.

_____________

Ya daɗe kwance a inda ta barshi,”Ka gyale ni bana so”,maganar ke mishi yawa cikin kai ,ba yau kaɗai aka taɓa gaya mishi ita ba,abinda ya kasa gane meye halaƙar maganar Sabreen da mafarkin shi,ganin kan shi ya fara ɗaukar zafi yasa watsar da tunanin,ya tashi ya saka kaya mara su nauyi wayar shi ya ɗauko yana sun kiran Haulat,”Mtseww na rasa gane meye matsalar haulat a cikin ɗakin take koƙarin taga mun aikata alfasha”,ƙara jan tsakii yayi ya jefar da wayar bai ma kula da wayar a kashe take ba.

Hango kwanan abincin da Sabreen ta kawo mishi yayi,murmushi yayi ya ƙarasa gurin ya buɗe ci ya fara yi yana murmushi.

Cikin salon magana irin nashi ya ce,”Wai zata iya kwana a ɗaki ɗaya da ni,sai bakin tsiya yadda take magana kamar wata mai faɗa a gani.”

Saida ya gama cin abincin sanan ɗauko system ɗin shi yana chat,murmushi yayi mai ɗauke da farinciki pics ɗin sabreen ne farrah ta saka a status da kayan makaranta tayi su,nayi kyau sosai fuskar ta ɗauke da murmushi.

“Mijina!

Tsintar maganar yayi a kunnuwan shi,wani murmushin ya ƙara yi,bai ɗago ba ya ce,”Kin ƙara dawowa ne?

Saida ta ƙaraso ta zauna a gefen gadon kusa da shi sanan ta ce,”Eh ya bazan dawo ba,ni da zan kwana a nan.”

Sai yanzu ya ɗago ya kalle ta,”Zaki kwana a nan?,ki kwana a ɗakin ki.”

“A’a ni tsoron ɗaki na nake ji,to meye idan na kwana a ɗakin miji na.”

Kallon ta yayi sosai dan tunda ta fara maganar ya zuba mata ido,har zai yi magana ya fasa,ya maida hankali gurin abinda yake yi.

Bata damu da hakan ba ta ce,”Me zan dafa ma?

“Kin san haƙƙin miji akan matar shi ? a maimakon ya bata amsar tambayarta sai tambayarta yayi.

Kai tsaye ta ce,”Na sa ni.”

“To gaya min.”

Saida tayi jimm sanan ta ce,”Eh ta kula da shi ta mishi biyayya da kula da kayan shi,ta dafa mishi abinci sai me ma? yawwa sai tarbiyar yaran shi sai…

“Taya ake samun yaran?

“Ciki!

“Taya ake cikin!

“Me?!

“Eh taya ake cikin?

Duk da kasancewar bata san abubuwa sosai ba waɗan da suka shafi ma’arata,amma saida taji kunya rufe ido tayi da hannuwan ta.

Kallon ta yayi yana murmushi Sabreen tana burge shi komai tayi abin kallo ne,”Hm meye na rufe ido ko kin san yadda ake yi ne?

kai ta girgiza mishi alamar a’a

“To ba zaki kwana a ɗaki na ba,tunda baki san haƙƙin aure ba.” ya faɗa idanuwan shi suna kan ta yaga yadda zata yi.

“A’a ni anan zan kwana.”

Yadda tayi maganar cikin shagwaɓa yasa ta kashe mishi jiki lumshe idanuwa yake yi yana kallon ta.

“A’a ba zaki kwana ba,wacce tasan haƙƙin mijinta ita ke kwana a ɗakin shi,kinga ke baki sani ba.”

“To ka gayamin sai in sani.”

“Saidai na koya miki.”

“Ka koyamin.”

“Idan baki so shikenan sai ki kwana a ɗakin ki kawai.”

“Ina so toh.”

Dariya yayi sosai har saida haƙoran shi suka baiyana sautin muryar shi ya baiyana.

“Sabreen kenan idan gaji yadda ta iya kiran mijina sai ka ɗauka tasan meye mijin,kamar wata wayayya idan ka ganta amma a zahiri bata san komai ba,bata iya komai ba”, shi da zuciyar shi suke wanan maganar har lokacin kallon ta yake yi yana dariya.

Ganin dariyar tayi yawa sa ya ita ma ta fara dariyar,yana jin ta fara dariyar ,ya ƙara fashe wa da dariya.

dan dariyarta tana bashi dariya,kamar wasu sababbin kamo haka suka dinga dariya ,dan tsabar dariyar da suke yi bata san lokacin da ta faɗa akan jikin shi ba,kwanciyar da yayi yasa ta kwanta kan ƙirjin shi.

“Sabreen!

“Na’am mijina.”

Dariya ta ƙara bashi amma baiyi dariyar ba yadai murmusa.

Kallon ta yake yi ,a ran shi yana faɗin ,”Ina ma kina so na ina sonki,da munji daɗin rayuwa.”

“To mai zai hana ka so ni ɗin.”

Zaro ido yayi jin amsar da ta bashi ,badai taji abinda ya faɗa ba.

Dariya tayi,”Naji ai.”

Lokaci ɗaya girman kai ya shige shi,”Kinji ai ba da ke nake ba,ni bazan so ki ba,dan ba ra’ayina ba ce ke.”

Ko kaɗan bata ji zafin maganar shi ma,dan ita ma ba son nashi take yi ba,kuma ba ra’ayin shi ba ce ita,duk abinda take yi dan Malama haulat ne.

A ranta ta ce,”Ban damu da ka so ni ba ni kawai ka manta da waccen banzar wacce bata san darajar muta ne ba,ni ban ma san abinda ka gani a tattare da ita da kike son ta ba.”

Shiru suka yi ba abinda kunnuwan su ke ji banda bugun zuciyoyin su,musamman ita da ke saman ƙirjin shi,hannun ta takai saitin gurin zuciyar shi,bata ke komai ba tana dai jin yadda take bugawa ne.

Yana jin ta taɓa ya rufe ido dan ƙaruwa bugun zuciyar ta ƙara yi.

Lumfashin ta kan fuskar shi yake sauka,ɗaga ta yayi yaga tayi barci murmushi yayi,”Savreen kenan mai abin mamaki.” zame jikin shi yayi sanan ya ƙara gyara mata kwanciya.

~~~~~~~~~~~~~

“Aunty Haulat dan allah karki biye momy abinda ta ke so kuyi bashi da kyau,kuma ba daidai ba ne,ga tarin zunubai ga ɗaukar haƙƙi gashi kuma baku san abinda zai biyo baya ba,dan allh….

Cikin daka tsawa ta ce,”Keee Sakina zaki gaya mana allah ,ke idan baki fita daga ido na ba,wllh zan ɓata miki rai,ni tsarar ki ce ma,ke a dole malamar addini ko,zaki dinga wani wa’azi an gaya miki ban san allah ba ne,ko ke kaɗai kika taɓa zuwa islamiya da za…..

“Sakina ko.” faɗar momy wacce ta shigo ɗakin,kallon Sakinar tayi wacce ke tsugunne a ƙasa.

“Sakina anya kuwa ni na haife ki?da a asibiti na haife ki wllh sai na ce canja min aka yi.”

Hawaye ya wanke fuskarta gaba ɗaya ,kuka mai tsuma zuciya take yi,halin uwarta yana ɓata mata rai ga tsanar da take nuna mata da banbanci,cikin muryar kuka ta ce,”Kiyi hakuri.”

“Dalla ɓace ki bani guri bazan shasha wawayi wacce ta ɗibo ɗabiyar dangin mahaifinta na.”

Jan jiki tayi tabar ɗakin tana kuka mai tsuma zuciya tausayin kanta ya kamata.

Kallon Haulat Momyn tayi ta ce,”Gobe da sassafe zamu tafi ki shirya da wuri dan a katsina ne.”

“Momy ban yi tunanin zan yi barci ba,ko tsakiyar dare ne a shirye na ke.”

“Yawwa Ƴar albarka.”

~~~~~~~
“Sabreen ki tashi an kira sallar maqrib.”

Sautin muryar shi ya doki dodon kunnan ta,a hankali ta fara buɗe ido,kan fuskar shi idanuwan ta suka sauka,kallon juna suka fara yi,ganin baya da niyyar barin kallon na ta yasa tai ƙasa da kai haɗe da tashi zaune.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button