HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Kai ya aka yi nayi barci?

“Hm ko dan kin kwanta akan ƙirjin mijin ki ne?

Dariya yayi,yana kallon fuskarta.

“Eh haka ne.”

Murmushi yayi a ranshi yana faɗin,”Hmm komai aka faɗa miki yarda zaki yi da shi wawiya kawai.”

Tashi tayi ta shiga bayin shi,tai alwala tana fitowa taga baya ɗakin,ita ma ta fita ɗakinta ta nufa saida tayi sallah sanan ta fito kicin ta shiga ta haɗa musu abinci sanan ta koma ɗakinta tayi wanka,doguwar riga ta saka ɓaka ba kwalliya a jikin rigar amma yadin rigar zai tabbatar ma da rigar bata yara ba ce,ta kama jikin ta komai ya fito kamar yarda allah yayi shi,hula ta saka bata ɗaura ɗan kwalin rigar ba.

Turaren miski shi ne turaran Savreen dan haka shi ta shafa a jikin ta sai da haɗa da wani turare wanda hajia ta kawo mata,ba abinda ta sha ko mai bata shafa ba,amma kasancewar yanayin fatar jikin ta mai kyau ce baka ce bata shafa mai ba.

Cikin tafiyar ta irin ta kasaita ta ƙaraso falon,yana zaune yadda ya zauna zaka tabbatar da hanlakin shi ba’a jikin shi yake ba,saida ta ƙaraso daff da shi ta ce,”Miji na tunanin me kake yi ne?

ɗagowa yayi ya kalle ta,fuska ba yabo va fallasa,kamar bazai yi mata na ba,sai kuma ya ce,”Ina tunanin mosoyiya ta ne,” ya kuma ɓata rai ya kau da ganin shi daga gare ta.

Haushin gaske taji cikin raunanniyar murya ta ce,”Ai mata gare ka.”

“Matar da bata san haƙƙin miji ba.”

“Zan koya kaji,” da shagwaɓa tayi maganar.

Murmushi yayi har sai da haƙuran shi su ka baiyana,ya rasa dalilin da yasa yake son yi mata magana akan aure.

“Zaka koyamin?”

wanan karan dariya yayi sosai,”Sabreen ƴar hajia.”

“Eh ba zaka koya min ba.”

“Baki iya ba kike ce kina son aure,saboda fiti na irin ta ki.”

“Ba fiti ba ne.”

Bai ce mata komai ba dan bashi da lokacin yin magana da ita,baya cikin yanayin jin daɗi ko kaɗan abubuwa sun mishi yawa,gashi yana bugatar macce ga wacce yake so ba aure take so ba,gashi baya jin zai iya kula matar shi.

Ɗakin shi ya tafi,yana zuwa ya faɗa kan gadon.

Ko kaɗan Sabreen bata ji haushi ba dan taɗau alwashin duk abinda zai mata ba gudu ba ja da baya zata shanye har sai lokacin da ta tabbata ya manta da haulat sanan zata rabu da shi.

Ɗakin ta bishi ,da salama a vakin ta,ta isa ɗakin hannuwan ta ɗauke da tiren abinci,kusa da shi ta ajiye abincin,”Ka ɗaure ka tashi ka ci abinci.”

Tabbaa yana da buƙatar amici,shiyasa bai yi mata musu ba,ya tashi ta zuba mishi ya fara.

Kallon yadda yake tauna abincin take yi,yana tsaka da ci aka kira sallar Isha’i kasancewar akwai masallaci a nan unguwar ta su.

Yana gama ci ya tashi ya fita,duk da bai gaya mata inda za shi ba tasan masallaci zai je.

Yana fita ta kwaahe kayan da maida su ma’ajiyar su kicin,sanan ta dawo ɗakin ta gyara,ta koma ɗakin ta,tayi sallah,bayan da idar ta koma ɗakin shi baya nan ,falo ta zo ta ganshi zaune yana kallon tivi ita ma zama tayi indian film ne,daga satar kallon shi ta gefen ido,shi kuwa gaba ɗaya hankalin shi ya tattara akan film ɗin kasancewar yana jin yaran,gajiya tayi gashi yaƙi mata mgn gashi bata gane komai a film ɗin.

“Mijina Barci ne ke ji,sai ka tawo,” tana gama faɗa ta wuce ɗakin shi kai tsaye,tana zuwa tayi alwala sanan tayi addu’o’in da suka zama jikin ta sanan ta kwanta.

Karfe goma sha ɗaya da rabi ya tashi,saida ya kashe komai sanan ya hawo sama dakin shi ya nufa,bai yi tunanin zai ganta ba,mamaki ya tsaya yana,taya zai iya kwanciya tare da ita,ya daɗe yana tunani sanan ya je nesa da ita ya kwanta,wani iri ya dunga ji zuciyar shi tana bijiro mishi da su,ƙin sauraran zuciyar yayi,a haka har barci barawo ya ɗauke shi.

~~~~~~~~~~~~~

Tun asubar fari Haulat ta tashi a gaggauce tayi sallah,ta shirya wayar momyn na ta kira saida tayi kira biyu sanan ta ɗauka.

“Momy baki tashi ba ne?

“na tashi jira ni a falo gani nan zuwa.”

Ko sallah bata yiba tsabar sauri,a falon suka haɗe lokacin ƙarfe biyar,motor momyn suka hau, kamar waɗan da zasu birnin sin,dan tsabar sauri ko da takwas tayi suna kaduna.

Ƙarfe ɗaya da wani abu suka isa garin katsina,saida suka wuce birnin ta suka fara ratsa dajujjuka sanan momy ta tsayar da motor a wani ƙungumin daji mai yawan duwatsu,kasancewar haulat bata taɓa zuwa ba hakan ba karamin tsoro da ji, Amma tsabar ƙiyayya da guguwar ɗaukan fansa da ke tashi a zuciyarta ya hana ta baiyana tsoron ta.

Tunda suka fito momy ke rike da hannuwan ta,basu yi magana ba ko kaɗan,sunyi tafi mai tsawo akan duwatsu,kafin suka iso wata ƴar bukka wani irin hayaki na tashi daga cikin,da ido momy tayi mata alama da zu juya ma’ana da baya da baya zasu isa har cikin bukkar.

“Ya murmurken kulumruke,ɓaaɓun ɓuturen ƙaranjauuu,Da baya -da baya fitinan jan jaburan ƙaranjauuu na kan dutsen wuta yana muku barka da zuwa.

Sun daɗe a tsaye fuskar su tana fuskan ta waje kamar yadda suka shigo.

Wata irin rikitattan ihu yayi mai tsoro ta zukatan bayi.
Sauka kaɗan haulat da zuba da gudu momy ta riƙo ta.

Wata dariyar yayi sanan ya ce,”An baku izinin zama.”

A Hankali suka juyo suka zauna,cikin tsoro haulat ta ɗauke kanta,sakamakon ganin munin halittar shi,gaba ɗaya idanuwan shi a waje su je,girman su ya kai girman ƙwai,ga su jajir,haƙura zakwa-zakwa suma jajir wani ƙazamin miyau ne wawwara ke dilaluwa daga bakin shi,mummuna ne fiye da tunanin ko,ni kai na ban iya ganin shi ba,sai jaruma bloody ce ta tsaya ta kalle shi ta siffan ta min yadda yake.

Tun da ya kalle Haulat ya ƙura mata ido harda lasar harshen shi.

“Me kuke so ai mata? ya faɗa cikin wata irin mummunar murya wacce zata iya tsorata dodan kunne.

Cikin rawar jiki Momy ta ce,”Muna so a haukata ta,sanan kuma ta bar garin gaba ɗaya tayi can wata uwa duniya.”

Razananniyar dariya ya ƙara yi,”Wanan ƙaramin aike a gurin jabarun ƙaranjuuu na saman dutse.”

Saida ya ƙara bashewa da dariya sanan ya ce cikin kausassiyar murya,”kin san sharaɗin farko kafin a fara aiki,ya kalle haulat ya lace baki,ƙaranjuuu yana vukatar ki,ya nuna haulat da munanan hannuwan shi kamar na kutare,saida gaban ta yai mummunan faɗuwa a razane ta kalli momy.

Cikin ihuuu ya ce,”Ba’a ma ƙaranjuuu musu duka ce dukk wanda ya tako nan zai yabi umarnin ƙaranjuuu,kuna ɓata ma ƙaranjuuu lokaci .”

“Na shiga ukku yanzu wanan mummunan kazamin zai kwanta da ni.”

Idanuwan ta har sun ciki taff da kwalla,har lokacin idon ta yana kan momy

Cikin raɗa momy ta ce mata,”Minti nawa ne ki ɗaure kawai kar ran ƙaranjuu ya ɓace ya fasa aikin kuma ya hukunta mu.” tana gaba faɗa ta bar ɗakin kamar yadda ta shigo da baya-da baya.

Waiyo ni tirrrr da irin wanan ƙazamar rawuyar ya allah ka kare mu ka tsare imanin mu ba mu da wayau ba mu da dubara ya allah.

Ko da momy ta koma ɗakin ita ma haulat ta fito cike da ɓacin rai.

Ita ma momyn kwanciya yayi da ita sanan ya basu umarnin wuce wa…

.
[12/23, 2:17 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/23, 2:19 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
Page 15
……………………………………

Addu’ar Saduwa Da Iyali:
بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button