HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi.

__________________

Kallon Haulat Momy tayi sanan ta maida hankalin ta gurin tuƙi ta ce,”To baga shi ba mun wuce gurin minti nawa ne?yanzu wa yasan munyi ,ko shi bai sani ba tunda umarnin ƙanjuung ne,kuma yanzu zaki ga aiki cikin gaggawa.”

Duk yadda Momy ta ke ba Haulat baki abin yaƙi dan jikin ta ya mutu,ranta bai so ba,ta so ta hakura amma tsoran abinda zai yi musu idan suka ƙi yarda yasa ta amce amma har ranta ta so hakura.

~~~~~~~~~~~~~
Kiran Sallar farko Sabreen ta miƙe,haɗe da addu’a a bakin ta,sanan ta dirgo daga kan gadon bayi ta shiga ta ɗauro al-wala sanan ta fito,har lokacin yana kwance yana sharar barci abin shi,kusa da shi ta matsa daff hannunta saka a kan shi tana shafa kwantacciyar zumar shi,a hankali kamar mai raɗa ta ce,”Miji na!ka tashi lokacin sallah.”

Kamar daga sama yake jin muryarta cikin kunnan shi,a hankali ya fara buɗe ido,har ya ware su kan fuskarta idanuwan suka sauka,sun daɗe suna kallon s
juna,har wani lumshe ido yake yi,ta shi tayi zubur tabar inda ya ke.

“Ka tashi kar a tada sallah ka rasa jam’i.”

Lumshe ido kawai yake yi,yana son macce mai riƙon addini tana ɗaya daga cikin ra’ayin shi.

Sallaya ta shimfiɗa ta tada iƙama raka’atanin fijjir zata yi,yana kallon ta birge shi ta ƙara yi,dan yasan ba’a tada sallah ba nafila ta ke yi,ganin ta fara yi yasa ya tashi ya shiga bayin,saida yayi kwankan tsarki kamar yadda ya saba yi ko wacce safiya.

Lokacin da ya fito da idar tana zaune akan sallayar yana kallon bakin ta yasan tasbihi ta ke yi ,bai ɗau lokaci gurin kallon ta ba,dan karya rasa sallah kamar yadda ta faɗa mishi,farar jallabiya ya saka ya ɗaura hula akan shi sanan ya fice.

Bayan sun idar da sallar saida ya zauna jin huɗuba,abinda bai taɓa yiba kenan tun dawowar shi daga india,ya rage abubuwa da yawa, a rayuwar shi wanda da ba hakan ya ke ba.

Tun yana falo ya fara jin sautin karatun al-qur’ani yana tashi,mamaki ya gama shi jin muryar sabreen,kasa yarda yayi har saida ya shiga ɗakin ya ganta tana karantawa,zama yayi yana sauraran yadda ta ke karantun cikin natsuwa kamar wata balarabiya.

“Kai daman yarinyar nan ta iya karatun haka mai daɗin gaske,to a ina ta koya?,a garin su,tun tana shekara tara dady ya gayamishi ta sauke al-qur’ani kuma tun a lokacin tana da hadda izufi goma,amma ban taɓa jin tana yi ba? to a gaban ka zata yi,yadda ta ke da rawar kai da ƙiriniya ba zaka ɗauka haka ta ke da ilimi ba.”

Duk shi da zuciyar shi su ke wanan zancen ya tambayi kan shi sanan kuma yaba kanshi amsa.

Ya daɗe yana sauraran zazzaƙar muryarta,wanda bai san lokacin da barci ɓarayo ya ɗauke shi ba.

Saida ta haɗa izufi biyar sanan ta rufe al-qurnin ta yi addu’o’in naiman tsari kamar yadda addinin ya zo mana da su sanan ta tashi ,ganin yayi barci yasa ta fita a ɗakin ,ɗakin ta,ta wuce wanka tayi dogowar riga ita ce kayan da tafi so a rayuwarta,ta atamfa da saka orange colour da ɗan ratsin brown sai fari,kayan sun mata kyau ainun ɗauren gwaggwaro tayi ganin kicin zata shiga yasa ba tai komai a fuskarta.

Karin kumallo ta haɗa musu kunon gyaɗa sai soyayyan danganin turawa sai ferfesu hanta,sai ta soya indomi da kwai da sayayyan kwan sai lipton.

Bayan ta haɗa komai sanan ta koma ɗakinta,ta ƙara yin wani wankan dugowar riga ta ƙara saka wa,ƙirar dubai pink ne kalar rigari sai akai adon rigar da blue ɗin stone,rigar ba irin me kama jiki ba ce,amma duk da haka ta amshi jikin ta kuma kirarta ta baiya na,ɗan ƙaramin gyalen rigar ta yafa sanan ta feshe jikin ta da turaren da shi ne turaren da ta saba saka wa,light makeup tayi sai plat shoe kalar blue,tayi kyau ainun.

Safa da marwa yake yi a cikin bedroom ɗin shi ,”Me ya kamata nayi? Savreen zaɓin iyaye na ce,kuma bata da matsala ko kaɗan nabi umarnin mahaifana na zauna da mata ta,to amma ba ra’ayina bace,meye matslar hakan zan iya rayuwa da ita,inah da kamar wuya ita Haulat fa? ba da aure ta ke so na ba,na ƙyale ta kawai,a’a taya bayan ina son ta,ita ma tana so na,soyayyar ƙarya tunda ba auran ka ta ke son yi ba.”

da ɗan ƙarfe yake maganar yana girgisa kai,”Taya? ba zan iya rayuwa da ita ba,to ya zanyi.”

Marar shi tai wani irin murɗawa dafe ta yayi ,ya dawo ya zauna,”Ina bukatar macce,wata zuciyar ta ce mishi,”To ai kana da ita halal ɗin ka ce,ba zaka sha wahala gurin shawo kan ta ba.”

“Zata raina ni.”

Wata zuciyar ta ce mishi,”Wani raini mutuni na sai girman ka da zata ƙara gani,kayi tunani mai kyau.”

“Assalamu alaika!

Bai tsaya tantance muryar ta ba ya amsa sallamar.

ƙarasowa ciki tayi saida ya lumshe ido dan wani irin asirtaccen ƙamshi da ya doki hancin shi,a hankali ya buɗe idannuwan shi ya sauke su akan ta,wani irin baƙon yanayi ya siyar shi zuciyar shi.

Ita kuwa ganin hakan yasa ta ƙara faɗaɗa fara’arta harda fari da fararan idanuwan tayi,ƙara takowa tayi daff da inda yake zaune ,ta duƙa cikin wata irin muryar ta ce,” Ka tashi lafiya? ya gajiya?

Har lokacin bai ɗauke idanuwan shi a kan ta ba,wani irin abu zuciyar shi ke mishi.

jin yayi shiru yssa da ɗago kai wani murmushin ta ƙara sakar mishi,bai san lokacin daya maida mata martani ba.

“Tana gama kwarin kumallo ka sauko mu ci.”

Ɗaga mata kai kawai yayi,ta tashi ta fara gyara ɗakin har lokacin yana nan ya kafe ta da ido,duk inda ta je binta da ido yake yi.

“Kayi wanka ne?

“A’a.” ya faɗa a taƙai ce.

“Ba zaka yi yanzu ba ne.”

“Zanyi.”

“To ka tashi dan Dady ya kira ni wai muje yana naiman mu.”

Tana rufe baki ya tashi,gyara gadon tayi sanan ta fita.

Bayan ya fito daga bayin yaji wani irin ƙamahi wanda duk lokacin daya ji shi yakan ji wani iri a ranshi.

Wanan shi ne sirran turare Naufal hatta so yana tsufa komai yana tsofa kuma yana gundura amma turare baya tsofa baya gundura kullum ka ji ƙamshin shi sabo ya ke zuwa kamar baka taba ji ba.

Kallon ɗakin yayi tsaf komai a kimtse yadda yake ganin sabreen da sakuwa bai taɓa tunanin zata iya aiki ba,yana son tsafta a rayuwar shi.

Tuno zasu je gida yasa ya saka shadda blue tasha aikin sama ,ta mishi kyau ainun da hula ita ma blue takalmi blue saida ya gyara fuskar shi sosai da kayan kwalliyar maza san ya feshe jikin shi da turarruka ma su ƙamahin gaske,zai yanzu ya tuno da wayar shi naiman ta yayi bai gane,bai damu ba dan yasan sabreen zata san inda ta ke tunda ita ke gyara ɗakin.

ƙasa ya sauko tun daga kan matattakalar ya hango ta,har ya iso cikin falon idan shi yana kan ta.

Jin ƙamshin turaran shi yasa ta waigo haɗa ido suka yi ,ta sakar mishi wani amintaccen murmushi shi ma sakar mata yayi.

“yawwa muyi sauri kar ya gaji da jiran mu.”

Bai ce mata komai ba,gurin abincin ya wuce ya ja kujera ya zauna,ita ta zuba mishi gunun gyaɗa ta zuba mishi har saida ta kusa shika cup ɗin dan tasan yana son gunun gyaɗa sosai.

“Sabreen!

Saida ta ɗago ta kalle shi sanan ta ce,”Na’am miji na!

“Kin dafa lipton?

“Eh gashi nan shi zaka sha?

“Eh plss ki matsamin lemon tsami a ciki.”

“Baka da matsala.”

Kicin ɗin ta koma ta matsu ruwan sanan ta dawo,ta haɗa mishi da lipton ɗin.

“gashi sai me zaka ci?

Dan galin turawa da kwai su kama kaɗan ya iya ci.

“Sabreen ina waya ta?

“Wayarka tana ɗaki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button