HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Taɓa fuska tayi ,bata ƙara cewa komai ba,da juya ta fuskanci tivi.

“Assalamu alaikum ya faɗa a hankali ita kanta sallamar kamar da turanci yayi na ce da Sabreen nan hhh da tasha dariya.

A tare suka amsa mishi kowanne su fuska ɗauke da Annuri ,Farrah ce ta fara magana “Yaya ka dawo”

cikin yatsine ya ɗaga mata kai bai ce komai ba.

Ita kanta farrah bata son hali irin na shi ga rashin kula mutum ga sharewa ga yatsine.

“Naufal ya hajiar”

“Tana lafiya tana gaida ke wai anjima zata shigo”

Yana faɗa ya tashi cikin yauƙi yabar falon.

“Allah momy yaya ya ƙara Chanjawa daa da ɗan sauki ,amma yanzu tunda ya dawo abin ya ƙaru”

Murmushi momyn tayi dan nasan gaskiya farrah ta gaya mata.

~~~~~~~~~~~~~

Cikin shigar doguwar jira ƙirar dubai ta ke baƙa ce rigar ta matuƙar amsar jikin ta kamar dan ita aka yi rigar,rolling tayi da ɗan ƙaramin gyalen waw,masha allah *Sabreen* kyakykyawa ba wani haske gare ta ba,amma akwai kyau kamar me,ɗan karamin bakin ta wanda yake kamar an zana shi,shi ke ƙara fidda kyawun ta,hancinta dogo ne amma ba siriri ba ne tana da cikar fuska ga fararen haƙora da ido gata da yalwar gashin gira da na ido ,ga iya murmushi hmmm abin dai sai wanda ya gani dan kamar a novel lolx to meye wanan..

????????‍♀????????‍♀yehh yanzu zan fara.

ga me bukatar shiga grp ɗin 08155184562

comment
shire
✅ote me on wattpad@fatimaumarmoddibo

~Bhartoolerty~
[12/6, 9:38 AM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/9, 1:05 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

Page 2

…………………………………
Cikin yanga ta ƙara su falon tana murmushi ta ƙagara gobe tayi,dan taje makaranta ta rama abunda Malama Haulat tayi mata.

“Kai masha Allah ƴar Aljanna kinga yadda kike da kyau kuwa ”
Hajiya ta faɗa tana kallon Sabreen ɗin.

Washe baki tayi ta ce”Hajiya ta ai ke na biyo shiyasa nayi kyau”

Ƙarasawa gurin Hajiyar tayi fuskan nan tata ɗauke da annuri, kan jikinta Hajiyar ta kwanta.

“To tashi muje tunda kin shirya”

Murmushi tayi tuno Gidan su Naufal zasu je,wanda ba wani tazara a tsakanin su dan a layi ɗaya suke.

“To muje ta faɗa haɗe da tashi ta fita gurin direba ta nufa ,yana ganinta ya taso a ruɗe.

“Kai kaji dai abinda na gaya maka,wallah inda aka samu matsala kasan abinda zan ma ba zai na gayama ba,da zaran ka ga kira na goben sai ka shirya,kasan yadda zaka yi da mai gadin makarantar ka kul….

“Ya dai lafiya ko wani abun ya miki ne” faɗar Hajia.

“A’a ba abinda ya min ,muje ko”

Buɗe musu motar yayi suka shiga,ba wani lokaci suka ɗauka ba dan daman duk a layi ɗaya ne.

Baban Gida ne mai ɗan karan kyau amma bai kai na su.

Hajiyar Gidan da farrah suna zaune a falo suka isa cikin falon.

Ba wanda Sabreen take jin kunya a rayuwarta sama da iyayen Naufal musamman hajiyar shi.

Har kasa da duƙa a gaban ta ce “Ina wuni momy ya gida”

Fuska ɗauke da annuri ta kalle ta ce mata” Lafiya lau Sabreen ya makarantar baki son zuwa gidan nan bansan abinda aka miki ba”

Ita murmushin tay ta ce “Ba komai momy zan dunga zuwa”

“Yawwa ko kefa ƴar gatan hajia”

Dukkan su suka yi murmushi,momy ta gaida hajia cikin martabawa da mutuntawa.
Inda farrah take nan Sabreen da zauna suna shiri da ita sosai ɗan farrah bata da iyayi da nuna iyawa da alfahari da gadara shiyasa suke shiru sosai da ita.

Hajia ta kalli Momy ta ce “Wai ina mutan india ne,ya zo ya bamu tsarabar mu ”

“Sun fita tare da Alhaji amma yanzu zasu dawo tunda yasan da zuwan ku”

“To allah ya kawo su ”

“allah yasa kar nayi dariya” sabreen ke faɗi a zuciyar ta.

Basu wani jimaba sai ga sunan ,Alhaji babban mutum ne kallo ɗaya zaka mishi ka fahimce hakan ga Annurin fuskar ko da yaushe kamar yana murmushi haka fuskarshi take irin ta hajia.

Da sallam suka iso falon,Shi Naufal ba wanda yaji tashi sallamar dan bala’i irin nashi.

Kan kujerar da Hajia ke zaune a nan Alhaji ya Zauna fuskan nan tashi ɗauke da murmushi
“Sabreen zo nan Alhajin ya kirata.

Cikin jin kunya ta taso kasa da tsugunna,yasa hannu ta ɗago ta ya zaunar da ita kan cinyar shi.

Wani gululun takaici ya kama Naufal “Duk kun lalata yarinya da gata sai abinda ta ke so ake yi ba dole ta lalace da dinga yiwa mutane fitsara ba,kamar wanan katowar yarinyar zaka zaunar da ita kan jikin ka ”

Duk a zuciyar shi yake wanan bambamin yana wani yatsina fuska kamar wanda ke kallon ɗanyan kashi.

“Sabreen ya gida ya makaranta?

“Lafiya lau dady”

“Masha allah Sabreen ki dage kinji,yanzu tunda ga yayan ku ya dawo kafin ya fara Aiki zai ɗinga zuwa har gida yana miki lesson”

Dumm Dumm gaban shi yai mugun faduwa,”shi xai ɗinga yiwa ƴar rainin wayun nan lesson kuma sanan shi zai bita har gida bama ita zata zo ba” a zuciya yake wanan tunanin dan baya gardama da dadyn shi.

“Aiki ja wanan ba zai iya da ni ba,nima kuma ba zan iya da bala’in kiliibin shi ba,yanzu ya zanyi”

“Naufal kullum zaka ɗinga zuwa indan ta dawo daga makaranta ka ji”

Maganar da dadyn yayi shi ya katse musu tunanin da kowannan su ke yi a zuci.

A sanyaye ya ce “Toh dady ,yana gama faɗa ya tashi zai wuce rai ɓace,dady yai saurin kiran shi “Naufal ka fito musu da tsarabar su,indan ka shiga ɗaki”

“To dady ya faɗa fuskar nan duk ta jagwalgwale da ɓacin rai.

Ya dade bai fito ba,har saida suka je daining table suka fara cin abinci sanan ya fito hannun shi dauke da kaya.

Yana zuwa ita ya fara miƙa mawa ,wani abu ne a baƙar jaka,ita ma kamar yadda ya ɓata rai haka tayi ta ce”Na godeee”

Ko nuna almar yaji bai yiba balle ya bata amsa.
“Ke baka ji ta ce ta gode ba” Dadyn ya faɗa.

Bai kalla inda take ba ya ce “u are wllcm”
Cikin salon kilibibi.

Dariya ce da zuwa Sabreen duk yadda taso ta shanye kasawa tayi saida tayi ciki-ciki bata so a gane sai da hau yin murmushi me kama da dariya

Iri ɗaya da abinda yaba ma Sabreen yaba farrah sai momy da hajia kowanne nashi a rufe,har ya juya sai tafi dady ya kira shi “Ina zaka ba zaka tsaya muci abinci tare ba yaushe rabonka da zama cikin ƴan uwa ,wai me yasa baka son mutane ne ,kuma har ƴan uwanka”

Bai ce mishi komai ba yaso ya zauna akan kujerar dake fuskantar Sabreen.

Kallon shi take yi tana son yin dariya ganin yake kallon abinci kamar kashi,yana fara cin abincin Sabreen tai kasa da kanta dan tasan zata iya yin dariya.

Bayan sun kammala cin abincin suka dawo falo.

*ASALIN* *SU*

Maryam sunan hajia na ainihi ƴar asalin kauyen bauchi ne,cikin rashin gata da taso gurin iyayenta,har suka mata aure,Muh’ad mai taƙama shine babban ɗan ta kuma shi ne mahaifin Sabreen,sai rabi’u (Alhaji)mahaifin su Naufal.

Muh’ad mahaifin sabreen yana zuciyar naima kuma ya taso yana son karatu duk da tasarar shekara ɗaya da rabi ne a tsanin shi da Rabi’u amma haka ya hakura da karatun shi dan kanin nashi yayi,tun yana shekara goma mahaifin su ya rasu,shi ya ɗau dukkan nauyin su ci da sha sutura da makarantar rabi’u,wanan ne dalilin dayasa Hajia ke mugun son shi.

Bayan rabi’u ya kammala secondry ,yayi iya kuƙarin shi har samu gurbi a ABU zaria ya tafi ,bayan tafiyar muh’d ya cigaba da naiman kuɗi yana kula da kansu kuma yana turawa Rabi’u.

Bayan rabi’u ya kammala karutun digirin shi ya dawo gida,aka fara fafatukar naiman aiki,Cikin sa’a allah yasa ya samu a garin abuja.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button