NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Ki ɗauko min ban ganta ba.”
Tashi kawai tayi ta dufi ɗakin nashi inda ta ajiye nan ta ɗauko,kunna wayar ta,pic ɗin shi ne wanda ya ɗauka a india a gaban wayar saida ta kalli pic ɗin sosai sannan ta taɓe vaki,”Ko kyau ina farin namji ya ga kyau kamar wani macce,dariya tayi ta ƙara cewa,”Uban yan iyayi zaka ga aikin Sabreen lokacin da ka ji ka manta wata haulat a rayuwar ka.”
Number Haulat ɗin ta shiga naima,”My dear”, ta ga an rubutu blocking ɗin number tayi.
Tai murmushin mugun ta sanan ta ce,”Hm malama ta nasan ke wacece,amma ke baki san ko ni wacce ba,ba taƙamar yana son ki ba idan ya manta da ke zanga tsiyar da zaki iya yi.”
A falon ta same shi,miƙa mishi wayar tayi,”Gashi!.
Amsa kawai yayi,”Muje ko.”
“Eh.
Kamar wasu masoyan gaskiya haka suka jeru sun yi kyau gashi kayan su iri ɗaya.
~~~~~~~~~~~~~
Tun a hanya Haulat ke kiran number shi wayar a kashe kamar tayi kuka.
“Momy tun jiya wayar shi a kashe ya zanyi momy?
“Ki kwantar da hankalin ki,ai na daɗe ina gaya miki kaidin mata da yawa,halan ma duk ita ce,amma yanzu za’ayi maganin ta dan uban ta shege idan ta fara bin bola sai mu ka tsiyar abun.”
Duk yadda Momy ke kokarin kwantar mata da hankali ta ƙasa,dan hankalin ta ya kasa natsuwa duk wani iri ta ke ji a ranta,wanda bata san ko meye ba.
~~~~~~~~~~~~~
Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gidan su Dady,cikin natsuwa da sallama a bakin su ,su ka isa cikin falon.
Suna isa dady ya taso da kan shi ya tarbo Sabreen riƙo hannun ta yayi su ka dawo inda ya ke zaune kan cinyar shi ya zaunar da ita,ba yau ba ne ranar farko da dady ya taɓa zaunar da ita kan cinyar shi ba,amma ba ta taɓa jin kunya irin na yau ba,kasa gaida shi tayi dan kunya.
“Sabreen ya kike? ina fatan komai lafiya,idan yana miki wani abu da baki so ki gaya min karki ji komai,kinji Sabreen.”
Saida ta ɗago kai ta kalle shi,shi ma kallon ta yayi yana son jin amsar da zata gayawa dady.
Ƙasa tayi da kan ta,”Ba komai dady.”
“Kin tabbatar.”
“Eh!
Ajiyar zuciya ya sauke sanan ya ce,”Masha allah komai daɗi,haka ne ke,kallon Naufal dady yayi,ƙasa naufal ɗin yayi da kai yana shirin gaida shi ya tari hanzarin shi.
“Naufal ka haifu,Lallai ka nuna min kai ɗa ne,na gari mai tarbiyar,naji daɗi Naufal na gode ma ka,da ka riƙe min Sabreen da kyau allah ya biya ka na god…
“Dadyn dan allah ka daina godiya,ni ya kamata nayi godiyae.”
Farinciki da jin daɗi ya ƙara mamaye dady,ƙarara fuskar shi ta nuna irin farincikin da yake ciki.
Duk wanan abun da ake yi Momy da Farrah suna zaune a ɗakin.
“Nima zan ma godiya Naufal ka cika min burina,Jibe insha allahu za ku tafi honeymoon kasar turkey..
.
[12/23, 2:19 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/23, 2:22 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
Page 16
_________________________
*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
_*Sayyiduna Aliyu yace; Manzon Allaah(ﷺ)* *yace min; KA RI’KA (ADDU’A KA NA) CEWA; {YA ALLAAH KA SHIRYENI, KUMA KA DAIDAITA NI (A KAN HALAYEN ‘KWARAI.}*_
°
“`[Sahihu Muslim;2725]“`
~~
_Muma sai mu dage da yin wannan addu’ar neman shirya da kuma hali na kwarai. Allaahu a’alam._
“`Allah ta’ala yasa mudace“`
。
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
………………………………………………………………
Gaba ɗaya jikin Naufal yayi sanyi tunanin halin da zuciyar shi ta ke ciki yake yi.
Ganin yayi shiru yasa Dady ya ce mishi, “Naufal ko ƙasar ce ba ka son zuwa?
Murmushi yayi sanan ya ce,”A’a ina so sai dai ban san ko Sabreen ba.”
Kallon Sabreen Dady yayi wacce har yanzu tana kan cinyar shi,cikin murmuahi mai ɗauke da farincike dady ya ce,”Sabreen ba ki son zuwa ƙasar ne?
“Ina so.”
Ai nasan ba zaki ƙi ba my Sabreen.”
Haba Alhaji ka barsu mu gaisa mana,tun zuwan ta ka janyo ta jikin ka,ka hana ta zuwa guri na,Sabreen ta so kin ji.”
Dariya dadyn yayi ya ce,”ba gwara ke ba kuna haɗuwa ni fa tun bikin sai yau ba abin ki ce ta zauna a guri na ba ne.”
“Ah…Momyn zata yi magana ya katse ta.
“Sabreen ta shi ki je gurin momy ko.”
A kunyace ta miƙe ta isa inda momyn ta ke,jikin jin kunya ta gaida ita.
Bayan zun gaisa ta koma inda farrah ta,cikin raɗa ta ce mata,”Oh su Aunty Sabreen manya,to ki tabbatar kin dawo min da baby a cikin ki.” Cikin dariya da zolaya tayi maganar.
Muntsinin ta Sabreen tayi har saida tayi yar ƙara sanan ta gyale ta,taja bikin ta tai shiru kamar ruwa ya ci ta.
Dady ya ce,”Sai kun dawo ne za’a yi maganar makarantar Sabreen ko kuwa,”ya faɗa yana kallon Naufal.
“Eh a bari mu dawo kamar zai fi,amma yadda ka gani dai.”
Sai da Dady ya ɗan murmusa sanan ya ce,”Naufal kai fa mijin ta ne,ka fi ni iko a kan ta yadda ka ce ɗin hakan za’a yi.”
Fira sosai suka yi harda Naufal ɗin dan tunda su ka zo basu fita ko ina ba har Dady ,sai lokacin sallah su fita su dawo har la’asar sanan suka fito,sai sun biya gurin hajia kafin su wuce.
Kafin su tafi saida Momy ta bata magangunan mata kala-kala tun daga zamfara da sokoto ta saka aka siyo mata,ta kuma ce mata kar ta yi amfani da su sai sun je honeymoon sanan ta sha.
~~~~~~~~~~~~~
“Kin san meye honeymoon kuwa? bai kalle ta ba yayi maganar.
Saida ta kalle shi sanan ta ce,”Eh ba shi ne mata da miji ke zuwa wata ƙasa ba,cin amarci.”
“Shi fa zamu je.”wanan ƙaran ya kalle ta.
“Eh ko baka so ne,ni fa matarka ce ta sunna.”
Ta taɓo mishi idan yake mishi kaikayi,zuciyar shi ta fara dan bugawa zuciyar shi ta mishi ce,”Tsoran me kake ji Naufal wanan ne gaskiyar lamari ita matar ka ce ta sunnah.”
Da sauri ta riƙe hannuwan shi,ta ce a ɗan ruɗe,”Yaya ka manta ne zaka wuce gidan hajia ko ba ka so na je ne?
Taka birkin motor yayi da sauri,kallon ta yayi ido cikin ido sanan ya ce,”Yanzu idan na ce bana so ki je ba zaki je ba?
“Eh Momy da hajia duk sun gaya min duk abinda miji na ya ce baya so kar nayi kuma idan ya hanani yin abu kar nayi,idan ka ce baka son zuwa ba zan je ba.”
Lumshe ido yake yi yana kallon lips ɗin ta yadda ta ke maganar,idanuwan shi har sun canza kala bugun zuciyar shi ya ƙaro,cikin izza da zafin nama ya janyo ta jikin shi ya haɗa bakin shi da tana ya fara kissing ɗin ta,abin mamaki yau bata yi koƙin ƙwatar kan ta ba,cikk ta tsaya yana juya harshen shi cikin bakin ta,shi kuma jin ta natsu ya saka ya ƙara zaƙewa,lalubarta ya fara yi ,jin ya fara taɓa jikin ta yasa ta ja jikin ta da sauri tana sauke ajiyar zuciya.
shi kuwa gogan kife kan shi yayi akan sitiyarin motor yana sauke nannauyar ajiyar zuciya,zuciyar shi kamar ta fasa ƙirjin shi ta fito dan bugawan da ta ke yi.
Bata ce mishi komai ba,har tsawon lokaci ba wanda ya iya yin magana a cikin su.
Ganin bashi da niyar magana gashi yamma na yi,ya saka ta mishi magana,”Yamma tana yi mu tafi.”
Bai yi tsammanin jin wanan maganar daga bakin ta ba,yayi tunanin ɗan iska zata ce mishi,ɗagowa yayi yana so su haɗa ido taƙi bari.
“Sabreen! da ƙyar maganar ta fito dan ma ta saba da jin maganar shi da ,da ne ba zata ji abinda ya faɗa ba.
Kan ta a ƙasa ta ce,”Na’am.”
Har lokacin idon shi yana kan fuskarta,yana son fahimtar yanayin ta,ganin yana ƙara shiga wani hali dan kallon ta yasa ya ja motor da gudu baya ya juya ,ya kai ta gidan hajiyar.