HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Sun isa harabar gidan yayi farkin ,yana yin farkin ɗin ta fito da gudu tai cikin gidan.

Kallon yadda tayi gudun yayi,yasan irin yadda ta ke son hajia a fili ya ce,”Ke nan Savreen zata iya zama da ni a matsayin mijin ta,hakan yana nufin ta aminta da ni,an ya kuwa ,koma me nene zan gano.”

Shi kaɗai ya ɗinga saƙa yana warwara.

Ita kuwa tana isa falon ta dunga kwala ma hajia kira.

“Hajia ta! Hajiata!

Hajiyar tana ɗakin ta da sauri ta fiton falon jin muryar Sabreen Rungume juna suka yi suna ihun jin daɗin ganin juna.

Saida suka gaji da tsayuwar sanan suka zauna sanan suka gaisa cikin farin ciki da jin daɗi.

Bayan sun gama gaisawa d daɗewa sanan ya shigo da sallama a bakin shi.

Hajia tana amsawa ta ce tun kafin yakai ga zama,”Da ba zaka shigo ba ne,ko baka so ta zo ba ne.”

Saida ya zauna sanan ya kalle ta yana murmushi ya,”Na isa na hana ta zuwa gurin bugun zuciyarta muradin ranta.”

Dariya suka yi su dukkan su kuwannan su yana cikin yanayin jin daɗi,bayan sun gaisa da shi suka fara fira.

Kallon Naufal hajia tayi fuska ɗauke da annuri ta ce,”Naufal na gode,na gode lallai ka haifu,duk da Sabreen jikin ka ce dole akwai so a tsanin ku amma dole mu jin ji na ma dan abinda kayi ba ko wanne ɗa ba.”

“Haba hajia ni kashe min jiki kuke idan kuna min godiyar ne.”

Amma can ƙarƙashin zuciyar shi tunanin abinda ta ce yake yi,”Akwai so a tsananin ku” yana son ya gane wani irin so ne wanan.

Kallon ta yake yi yana son su haɗa ido amma taƙi yarda da hakan ta faru.

A zuciyarta ta ce,”Ba wani so wanan ne zai so ni, tabb kin saɓa number hajia.”

Suna gidan aka kira sallar maqrib ya fita yayi su ma,su ka tashi zuka yi,bayan ya dawo saida suka ci abinci sanan suka tafi.

Saida hajia ta bata garin magarya da sabon magarya sanan suka tafi.

Har suka isa gida ba wanda yai ma wani magana,ɗakin shi ya tafi ita ma ɗakinta ta wuce dan ta chanza kaya.

Dan samon tayi wanka ta saka riga dugowa mara nauyi ba kwalliya a jikin rigar sai da ta fashe jikin ta da tararen da ta saba amfani na shi sanan ta fara gyara ɗakin ta duk da kafin su tafi ta gyara.

Yana isa ɗakin shi ya faɗa kan gadon kan shi na kallon saman ɗakin,sauraran bugun zuciyar shi ya tsaya yi,ya daɗe a haka sanan ya tashi yai toilet.

~~~~~~~~~~~~~

Kuka sosai haulat ke yi,”kin gani momy har yanzu ba wani labari tun muna kan hanya kika sa a fara saka ido amma ba wani labari sai ganin su ma da aka ce anyi suna jin daɗi har da kiss fah aka ce ya mata.”

Dafa ta momy tayi,”Ki kwantar da hankalin ki,na gaya miki aikin shi a ranar ya ke yi,kuma yanzu baki ga gobe tayi ba ance bata hauka ce ba,yau komai dare sai aikin mu yayi ki kwantar da hankalin ki.”

“Hankali na ba zai iya kwanciya ba momy.”

“Na gaya miki ki kwantar da hankalin ki idan wani abu bai faru ba sai mu koma goven.”

Duk wanan abun da suke yi sakina tana jin ,idanuwan ta sunji ja kwalla dam a idon ta.

Cikin raguwar murya ta ce,”Momy ba kyau kuyi tsoran allah,dan…..

“keeeeee dan uban ki ,ki ɓace daga nan kafin na buɗe ido na.”

Gaba ɗaya jikin sakina rawa ya fara yi,da ƙyar ta iya jan ƙafar ta,ta bar gurin.

Ita kuwa momy taita vamvami kamar karamar mahaukaciya sai kwace ma sakina albarka ta ke yi.

~~~~~~~~~~~~~

Da sallama ya shiga ɗakin yana tashin ƙamshi,ganin kamar hankalin shi baya jikin shi yasa,ta lallaɓa ta vayan shi ta rufe mishi ido da hannuwan ta.

Mai da idanuwan yayi ya rufe su,dan yasan ita ce,a hankali zuciyar shi ta fara bugawa hannayen shi ya ɗauka kan na ta,sai da yaji wani irin jin lallasar fatar mai.

Cikin wata irin siga wacce shi kan shi ba zai iya bambance yanayin ba ya ce,Sabreen!

“Maimaita.”

“Sabreen!

“Waw na baka kyautar Abuja harda kaduna ba,kasan me? ta sake shi ta dawo inda ya ke zaune taff da shi ta zauna,har suna gogan jikin juna.

Kallon ta yayi ya sake mata wani irin kyakyyawan murmushi sanan ya ce,” taya zan sani.”

“Ka bala’in iya kiran sunan da indiyanci kike kira gaji daɗi ku….

Dariya ta fashe da ita sosai ya dara ita kuwa bin shi da kallo kawai ta ke yi dan bata ji abin dariyar da ta faɗa ba.

Saida yayi me isar shi sanan ya tsaya bai ɗaure fuska ba ce kalle ta ya ce,”Wai da indiyanci,kai sabreen kina da abin dariya.”

“Toh ai gaskiya na faɗa wa gaji yana kira na irin yadda kake kira na?

“Hajia da Dady.”

“A’a su da hausa su ke kira.”

Murmushi yayi mai ɗauke da annuri,”Hm kina da abin dariya,na tambaye ki.”

“Uhum!

“Wai lokacin nan da na zo gurin hajia a lokacin ban daɗe da dawo wa ba,har na same ki a falo kina kallo kika banza da,naga kina da dariya a lokacin me ya sa ki dariyar?

Yana kai ayaa ta fashe da dariya,kallon ta ya ke yi tana dariya kamar irin wancen lokacin,taya da yayi.

Saida suka yi me isar su sanan su ka tsaya,suna kallon juna,wani irin abu ke ta so mishi a rai.

Cikin yanayin jin barci ta ce,”Barci na ke,bari na kwanta.”

Bata jira cewar shi ba ta,tashi saida ta shiga bayi nayi al-awla sanan da tayi nafila tayi addu’o’i iri iri sannan kwanta,duk yana kallon ta,tana kuma ƙara birge shi,addu’o’in da yaji tana yi yayi magana dan wasu mai iya ba,wasu ya manta su.

“Na hakura nayi rayuwata da ita,bata da matsala ko kuma hakan zai saka iyaye na su ji daɗi sosai.”

Nannauyan numfashi yayi sanan ya ƙara faɗin,”kai abin is not easy taya? to daman ai matsalar tawa ce,” dafa kan shi yayi wanda ya ɗau zafi,wata zuciyar tana tausar shi akan ta zaduda kawai wata kuma na bijiro mishi da abubuwa marasa amfani.

Safa da marwa ya kw yi a tsakiyar ɗakin yana kuma kallon ta ,ta duƙunƙune guri daya tana varcin.

Tausayin kanshi ya kama shi tabbas yana da buƙatar macce,kuma yasan idan har mai samu yadda yake so ba,har wani ɗan lokaci zai iya samun matsala.

Kamar wanda aka ba umarnin ya zauna can kuma ya tashi tsaye,hura hanci ya fara, a fili ya ce,”Ba zan iya cutar da kai ba,bayan allah ya ƙubutar da ni.”

Murmushi yayi me ƙyayatarwa har da lumshe ido da hura hanci,”Ban san ta yadda zaki ji al’amarin ba amma dole zanyi Sabreen, ba yadda..

.
[12/23, 2:22 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/23, 2:24 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

Page 17
………………………………………………

Kwanciya yayi ɗan nesa da ita kaɗan,ya daɗe yana saƙa da warwara, yana jin tana barcin ta hankali kwance,shi kuwa sai juye yake yi sai ƙarfe ɗaya saura sanan barci ya ɗauke shi.

Kamar dai kullum kiran sallar farko ke tada ita yau ma hakan ne,tana tashi da kunna hasken ɗakin kallon inda yake tayi saida tayi murmushi ganin yadda yake barcin hannayen shi gaba ɗaya a ƙirjin shi.

Saida tayi alwala sanan ta matso kan shi ta taɓa sanan ta ce,”Miji na ka tashi lokacin sallah.”

Shiru barci yayi nisa ganin hakan yasa ta matso kusa da hunnan shi ta hura mishi iska,motsi yayi amma bai buɗe ido ba,hancin shi ta fara ja nan ma shiruu na koma gurin idon shi ta fara shafa batar idon nan ma shiruu,ganin hakan yasa takai hannunwan ta kan lips ɗin shi ruwan alwalan da bai bushe ba na hannunta shiyasa lips ɗin suka jiƙe,shafasu ta ke yi,ta shafa da ƙasa ta shafa na sama nan da nan ya fara juya su kamar me kokarin cin wani abu,ganin hakan yasa ta fashe da dariya,wacce tai nasara isa ga dodon kunnan shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button