HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Firgittt! ya tashi kallon ta ya ke yi cike da mamakin abinda ta ke ma dariya.

Cikin dariya ta ce,”Wai Halan yunwa kake ji.”

Cikin rashin fahimta ya ce,”Me?

“zan tashe ka ne ka ƙi tashi shi ne ta hura ma kunne na jajja hancin ka ƙi tashi shi ne da na taɓa ma baki ka fara motsawa kamar zaka ji wani abun.”

Murmushi yayi labarin sabreen yana bashi dariya ya kuma bashi mamaki.

“To meye na dariya.”

Har ta buɗe baki zata yi magana akai kiran sallah,”Kai ka tashi.”

Tana faɗa ita ma ta tashi ta shimfiɗa sallaya sanan ta fara sallar nafila kamar yadda ta saba.

Ganin hakan yasa shi ma ya tashi ya faɗa toile bai ɗau lokaci ba ya fito gurin saka kaya ba bai ɗau lokaci ba ya fita.

Bayan ta idar da sallah ta fara aikin gyara ɗakin saida ta ƙimsa komai sanan ta wuce ɗakin ta,tana zuwa ta gyara shi sanan ta nufi kicin.

Yau bai zauna dan barci bai ishe shi ba,yana shigowa falon yaji ƙamshin abinci yana tashi,kallon hanyar kicin ɗin yayi kamar ya shiga sai ya fasa ya wuce ɗakin shi bai yi mamaki ganin shi tsab ba dan yasan halin ta ne,ya kula da ita sosai tana da tsabta har ta kusa fin shi,kwanciya ya koma yayi.

Bayan ta gama haɗa komai ta koma ɗakin ta,tai wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa,Karuwan jiki sabreen gare ta,irin jikin da ko wani irin shiga yana amsar shi,irin shi ne ka kan kasa gane al-adar mutum idan ya kasance mai yawan shiga iri-iri.

Bayan ta gama shirin ta tsab,kai tsaye ɗakin shi ta nufa,a hankali ta buɗe kofar,ganin shi kwance yasa ta ƙarasa hawa tayi kan gadon,naniƙe shi tayi,shi kuwa bai sani ba yayi nisa yakai ziyara golden pen????

Ita barcin ne ya ɗauke ta.????‍♀nidai nayi nan asha barci lafiya.

~~~~~~~~~~~~~

“Baki san waye mutumin nan ba,bashi da mutunci kar mu koma mu bani mu lalace dan mugu ne.”

Cikin kukan mai sauti Haulat ta kalli momyn nata ta ce,”Haba momy gaskiya mu koma kina gani momy ya daina so ba,na shiga ukku momy ya zanyi.”

“Ai tun farko shi ya kamata ayiwa asirin ba ita ba,da shi aka mawa ya isa ya daina sonki bai isa,amma me kika buɗe baki kika ce min,ke baki son a mishi asiri kin fi son irin son da yake mi ki,to ai gashi kin ga ni irin son da yake miki dai ko yanzu kin ganshi.”

“Har da it..

“Harda ita ko,ke banza ce har yau baki gane avubuwa da dama an gaya miki namiji irin macce ce.”

A sanyaye ta ce,”Momy yana so na ni ce nai bishi abinda yaji haushi.”

“Koma meye da anyi asirin bazai ji haushin ki ba duk abinda kika mishi saida ya baki hakuri.”

“Momy to muje dan allah mu je yanzun nan.”

“Tashi to mu tafi.”

Cikin gaggawa suka tashi ko shiri basu yiba mayafi kawai suka ɗauka,a harabar gidan suka haɗu da sakina ta dawo daga makaranta ko kallon banza ba su yi mata ba.

Ita kuwa tana kallon yanayin su tasan ba hanyar allah zasu bi ba,aran tai musu addu’ar gafara da shiriya ta wuce avin ta.

~~~~~~~~~~~~~

Sama-sama ya fara fuɗe idon ƙamshi ya fara ziyarta hancin shi,na hanzari ya buɗe su dan tabbatar da abin da yaji,a hankali zuciyarshi ta fara bugawa da ɗan ƙarfi,lumshe idanuwa yake yi,kallon hannuwanta yayi waɗan da gaba ɗayan su suna rungume a jikin shi,kafafuwan ta duk suna kan cinyar shi,fuskarta kuwa tana ƙirjin shi kasan cewar yafi ta tsawo.

A hankali yasa zame hannun shi da ga jikin ta ya tallafo fuskarta idanuwa ya zuba mata,numfashin ta yana dokan fuskar shi,a ran ya ce,”kamar mu kasance a haka,”

Ko kaɗan baya gajiya da kallon ta,wani irin yanayi ya shiga wanda bai san irin shi,bai kuma taɓa shiga ba,saida ya ƙarewa halitta fuskarta gaba ɗaya kallon,ɗan ƙaramin bakin ta shi yafi ɗaukar hankalin shi,gai gashin idanuwanta,tsarin fuskar ya mishi kyau,hannu ya kai kan lips ɗin,da sauri ta buɗe ido,sai cikin nashi kallon ƙuda suka fara yiwa juna,cikin muryar da batai yi tunanin zai ji abinda zata faɗa ba ta ce,”Kai ma zaka rama ne.”

Bai ji sautin muryarta ba amma motsin bakin ta ya gani,murmusawa kai yayi.

“Yaushe ka tashi?

“Ɗazun.”

Shiru tayi sanan ta ce,”Kai baku ƙarya ba.”

Janye jikin ta tayi ,wani irin abu ya zake shi a heart ɗin shi,ko kaɗan bai ji daɗin janye jikin ta ɗin da tayi ba,lumshe ido yayi yana jin wani iri a ran shi.

Hannuwan shi ta yanyo,”Ka tashi rana tayi.”

Wani irin yaji kallon hannu yayi sanan ya kalle ta shagwaɓe fuska tayi haɗe da rausaya kai alamar ya tashi.

Kai tsaye zuciyarshi ta amsa umarnin ta,tashi yayi ya banɗaki ya nufa,ita kuma ta fita.

Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi agogon bangon dake manne a jikin bangon fallon ya nuna.

Gurin abincin ta nufa ya ɗan rage zafi amma bai yi sanyi ba zasu ci a haka.

Bayan ya fito daga bayin saida ya zuba kasaita gurin shiri,cikin ƙananan kaya ya shirya sun mishi kyau ainun navy blue rigar sai baƙin wando,saida ya gyara fuskar shi da gashin shi sanan ya fashe jikin shi da turare,sanan ya fito.

Tun daga saman benan ya hangota tsintar kan shi da yin murmushi yayi wanda bai san dalilin yin shi ba,kamar ance ɗago kai ta ɗago suka haɗa ido murmushi suka sakar wa juna,wanda ya fito ne daga ƙasan zuciya.

Zama yayi,ta fara zuba mishi waina ta fara zuba mishi sai lipton da kwai,ita ma shi ta zuba,ba wanda yace ba wani ƙalla saida idan sun haɗa ido su sakar wa juna murmushi.

Dukkan su suka tsince zuciyoyin su cikin natsuwa da jin daɗi da farin ciki da walwala,ita ta fara gaba ci yana jin ta tsaya shi ma ya tsaya kallon shi tayi wai murmushi,”Nima na ƙoshi.”

“Ka ci dai ka ga ni ko ban ci ba,ina da qiba ta,amma kai kuwa idan baka ci ba sai yadda…

“Kin fi ni qiba ne?

“Kam wa zai haɗa ma.”

Kauda zancen yayi ya kawo wani ta hanyar faɗin,”Gobe ne fa!

“Wai zuwa honeymoon ɗin mu.”

“Kin shirya ne?

“ƙwari kuwa ,kai baka shirya ba ne?

“Hmm na shirya zaida ke nake tunanin anya kuwa.”

“Na shirya ma komai da komai ka daina shakka.”

“Komai da komai fa kika ce.”

“Eh komai da komai.”

“To amma kin koya kuwa.”

“Me?

“Haƙƙin miji!

“Ka fasa koya min ne?

Murmushi yayi mai ƙunshe da abubuwa da yawan gaske.

Bai kai ga bata amsa ba ta ce,”Dady ya ce,wai da wuri zamu tafi goben yau sai muje muyi musu sallama,amma fa ina ɗan jin tsoro kar wani abu ya faru mara kyau a can,ko da yake tsoran me zan ji ina tare da mijina ɗan uwa na,nasan ba zaka bar wani abu ya cutar da ni ba.”

Ta ƙare maganar tana kallon shi,yanayin shi kuma ya ɗan canza wanda zai iya alaƙanta wa da maganar da ta mishi.

“Wai zanga fararan muta ne,ai nima kuwa irin sabulon su zaka sai min nayi fari irin na su.”

Dariya ya ɗan yi,”Ai ke zama abin kallo ce a gurin su.”

Saida ta ɗan zare ido,”Wai saboda muni ko.?

Wanan karan saida sautin muryar shi ya fito,ita kuwa ya mutsa fuska tayi tana kallon shi.

????‍♀????‍♀Ina zan iya muku dan firar ku bata ƙarewa.

~~~~~~~~~~~~~

Banka gudu Momy ke yi,har suka isa garin katsina ba wanda ya ce da wani komai,wanan ƙaran tsoron Haulat ya ragu.

Kamar yadda suka yi farkon zuwa yanzu hakan suka yi,saidai shi yanayin shi ya ƙara canzawa ya ƙara muna,kuma bai yi dariya ba kamar wancen zuwan sai uban ihun ta yake yi.

Ya daɗe yana amvaton shi yana ihiuu yana yarfe-yarfe dukan su sun tsorata ainun ganin sun daɗe bai ce musu uffam ba gashi sun daɗe da zuwa.

Cikin mummana kuma kaussar muryar ya ce,”Hatsabibiyar yarinya ce,da ƙyar ƙaranjuug yasha ya kasa kusantar inda ta ke,ba nazara ba nazaraaa,ba zai iya zuwa inda take bahhh.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button