NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Wata razanannar ihuu yayi wacce dan tsoro har hantar cikin su saida ta juya,hatta kasar gurin da bukkar zai da ta girgisa.
Bayan wasu ƴan mintina sanan komai ya lafa shi ma ya tsagaita.
Cikin rawar murya momy ta ce,”Yaanzuu shiii yaaron f.”
Ai kamar ta ƙara tunzura shi ya ƙara buga wani sabon ihhu na tsawon sakonni sanan ya murtuke fuska,ƴan karance karancen shi da kalle-kallen shi yayi sanan ya bushe da muguwar dariya saida yayi mai isar shi sanan ya ce,”Akwai nazarraa Nazara,me kuke da bukatar ai mishi?
Har momy ta buɗe baki zata yi magana haulat ta katse ta,”Ya so ni kamar ya mutu sanan sai abinda na ce zai yi magana ta kaɗai zai ji sai yadda nayi da shi.”
Dariya ya bushe da ita ,sanan kuma ya murtuke fuskar,”Wanan ƙaramin aiki ne amma akwai sharaɗi bai tsauri…
Kallon Momy Haulat tayi a tsorace sai zare ido take yi.
“Hhhhh maganar tsoro babu ita tunda kuka kawo kan ku ƙaranjuuug ya amshi saƙon ku dole ku yarda da sharaɗin.”
Tsuull! fitsari ya zubowa Haulat tsabar tsoro da farga ba,kallon momyn take yi wacce ba alamar tsoro da fargaba ko kaɗan a idon ta.
Kallon shi momy tayi ta ce,”Kasan ni indai akwai nazara to ina amincewa da ko wani irin sharaɗi.”
Dariya ya ƙara fashe wa da ita,wanan karan saida na tsorata da gudu na fito ina haki ina naiman taimako duk na ruɗe na kasa gane hanyar da zan bi,kawai sai ga Aunty beelat janyo hannu na tayi muka fara gudu,kwatsam sai ga ommu deedat da motorta tayi fakin a gaban mu,ai tsorum muka taɗa,ina shiga ng bloody a ciki janyo ni jikinta tayi ta fara jijjiga ni tana ban baki nayi shiru cikin raɗa ta ce min,”Bloody na ki kwantar da hankalin ki kinji ga shadowwn ki tana jiran ki tun dazun.”
Cikin hanzari na ɗago na kalle ta????????????♀????♀????♀????♀????♀kunga dole na kama ɗariqa shadow tayi kira????????.
.
Ina mugun -mugun son ku har raina,ba abinda zan ce saidai allah ya barni da ƙaunar ku a raina❤.
[12/23, 2:24 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/23, 2:25 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
Page 18
…………………………………
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{BABU WANI AIKI DA AKE ‘DORAWA AKAN MIZANI YA SANYA MIZANI YAYI NAUYI KAMAR KYAWAWAN HALAYE DA ‘DABI’U, KUMA LALLAI MAI KYAWUN HALI YANA SAMUN MATSAYIN MAI RAYA DARE DA IBADA, DA RANA YA RAYA DA AZUMI.}*_
“`[Sahihut Tirmizy;2003,Sahihul Jaami’i;1620]“`
_Shi kyawun hali yana dauke da dumbin alkhairi wanda mai yi zai amfana da shi Duniya da Lahira. Allaahu a’alam._
“`Allah ta’ala yasa mudace“`
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
_______________________________
Wata mahaukaciyar dariya yayi mai haɗe da ihuu sanan ya murtuke fuska ya kalle Momy ya ce,”Kin yi nisa! asiri zai kama shi amma kuma duk sanda ya ƙarye kan ki zai dawo zaki haukace ne.”
Ya kara bushewa da dariya sanan ya ɗaura da faɗin,”Kuma asirin ba mai nisan zango ba ne,duk sanda ya tambaye kan shi akan naiman dalilin da yasa yake bin umarnin ki kamar raƙomi da akala to ranar zai ƙarye.”
Haulat dan tsabar tsoron jin abinda ya faɗa saida fitsarin da yake zulluwa ya fito gaba ɗaya,zuciyarta ta shiga buguwa da karfin gaske zufa duk ta wanke ilahirin jikin ta,kallon Momy tayi wacce ita kan ta tana cikin tsoro da tashin hankali.
Murya na rawa Momy ta ce,”Mun amince!!
Ya kwarara uban ihuuu yana kallon ta yana tasar baki,”Duk sanda yaji muryarki asirin zai fara aiki.”
Ita kuwa Haulat kamar gunki haka ta koma,saida ya ƙara kwanciya da su sanan suka tafi.
~~~~~~~~~~~~~
Bayan sun kama firar suka shiya gidan su hajia suka nufa a can suka tadda dukkan su momy da dady da farrah,fira suka yi sosai dan Naufal ma ya manta da wata haulat ni kuwa na ce daman ba son nata yake yi ba.
Har bayan maqrib sunan nan zaune a falo Dady wacce Sabreen ke zaune akan cinyar shi ya zaunar da ita kasa gaban shi,kiran Naufal yayi ya zo kusa da ita ya zauna.
Cikin dattijowar murya ya ce,”Naufal!
Naufal wanda ke zaune a kasa gaban Dadyn kusa da matar shi ɗukar da kan shi yayi ya ce,”Na’am Dady.”
“Naufal ba zan iya misalta maka irin farincikin da na ke ciki ba,duk da nasan ka ji magana ta kuma ka bi umarni na ka amshe matarka da hannu biyyiyu,amma hakan ba zai hana na ƙara tunatar da kai akan amanar da ka ɗauka ba,Naufal Sabreen amana ce na danƙama, ka sani Naufal ko wani irin yanayi zaka tsinci kan ka a rayuwar nan idan har ka cutar da sabreen ban yafe ma ba ko bayan ba raina bani ba ka.”
Zuciyar Naufal ta fara bugawa da mugun ƙarfin wanda faruwar hakan yai sillar haifar mishi da mutuwar jiki,bai yi tunanin zai iya magana va yai karan banin buɗe bakin shi,”Dady na ma alkawari ba zan cutar da ita ba komai rintse komai wuya zan rayuwa da ita zan kyautata mata.”
“Yawwa Naufal Allah yai maka albarka.”
Jin amsar da Dadyn ya bashi ne ya tabbatar mishi da ya faɗi abinda ke ran shi kenan.
“Naufal ka ga Sabreen ba sabawa da zuwa irin ƙasacen nan tayi ba ,dan haka sai ka kula da ita sosai,Sabreen matar ka ce nasan ka fi ni sanan yadda zaka kula da ita,tsananin son da na ke mata ne yake sawa naga kamar ba wanda zai iya kula da ita,Naufal karka cutar da sabreen dan ni zaka cutar ,idan ka kyautata mata ka kyautata min,ina son sabreen fiye da tunanin ka jinin jiki na ce,ka kula da ita k….
“Ya isa haka kamar yadda kake son ta shi ma yana son ta matar shi ce,”
Cewar hajia ,kallon Naufal ɗin tayi fuskar ta ɗauke da murmushi wanda shi har lokacin kan shi yana ƙasa,”Naufal ba abinda zan ce ma sai abu ɗaya ni ma na baka amanar Sabreen shi ne kawai abinda zan faɗa ma,matarka ce ka fi mu sanin yadda zaka kula da ita,allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya.”
Dukkan su suka amsa da amin,sanan momy ta kalle shi ta ce,” nima abu ɗayan zan faɗa ma ka riƙe amanar Sabreen Naufal allah ya kaiku lafiya.”
Nan mu suka amsa da amin,sanan suka ɗan taɓa firar duk akan tafiyar su ɗin labarin garin su ke yi,da gidan ya zasu sauka.
Duk abinda ake yi jikin Naufal a mace,zuciyar shi ta cunkushe wanda hakan ya hana shi yin tunanin komai.
Sai ƙarfe takwas suka tashi zasu koma gidan su,Sabreen tayi kuka kamar ranar auran ta tunda goben tun biyar zasu bar gida ba haɗuwa zasu kuma yi ba,da ƙyar aka janye jikin ta gurin hajia.
“Kiyi hakuri ki daina kukan nan plss.”
Kallon shi tayi cikin kukan ta ce,”Ji na ke kamar na tafi kenan bazan dawo ba.”
Saida gaban shi ya faɗi taka burkin motor yayi da sauri ya juyo
ya kalle ta,janyo ta jikin shi yayi ,”Hava ƴar aljanna yaushe kika zama haka ne ban san ki da rauni ba fah,taya zaki ce haka zamu dawo cikin ƙushin lafiya.”
“Ba zamu daɗe ba ne.”
“Eh ai sai yadda kika ce,idan kina so a fasa zuwan ma za’a fasa.”
“A’a ina son zuwa.”
“Kina son cin amarci kenan.”
Murmushi tayi ta ɗaga mishi kai alamar eh.
“To ai baki iya komai ba.”
“To ba ka ce zaka koyamin ba.”
Ɗago kanta yayi kasancewar akwai haske a motor yasa ya ga fuskarta da kyau lipa ɗin ta ya fara kallo,haɗa bakin shi da nata yayi sun ɗau lokaci suna abu ɗaya kafin ya fara fita haiyacin shi,ganin abin yafi ƙarfin ta yasa ta fara koƙarin zame jikin ta,amma ta kasa.