HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Ya Naufal!

Yaya yayi nisa nishi ya fara yi,janye jikin ta tayi da ƙarfi ita ma haƙin ta fara yi.

Sun daɗe a haka suna nishi wanda kowa ke jin na kowa,can ya ja motor cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gidan.

Tunda yayi fakin ɗin ya tsaya yaƙi saukowa,ganin hakan yasa ta ce,”ka zauko.”

Tana gama faɗa ta sauko gaba tayi bata tsaya jiran shi ba.

“ke ce kaddara ta Sabreen dole na karɓe ki ba yadda na iya,nasan wata rana zan son ki.”

Ya daɗe yana tunanin ya amincewa zuciyar shi yin rayuwa da ita cikin kulawa ga alƙawarin iyayen shi baya son ya saɓa musu,kuma ko da ba alƙawari Sabreen abin tausayi ce marainiya ta uwa da uba dole a tausaya mata,ya yaken wa zuciyar zai koyan son ta idan sun je turkey .

Ita kuwa kai tsaye ɗakin shi ta nufa saida yi ɗan gyare-gyare sanan ta shiga bayi tayi wanka ta tauro alwala,shafa’i da wutiri ta yi.

Tana cikin yi ya shigo murmushi yayi dan san tayi sallar isha’i zama yayi bakin gadon yana kallon yadda take sallar komai daidai cikin natsuwa,bayan ta gama ta fara addu’o’i duk yana jinta saida ta yi komai sanan ta tashi da nufi ɗauke sallayar ganin shi yasa tayi murmushi.

“Ka shigo? na haɗa ma coffee?

“Eh lipton ki matsa lemon tsami.”

“To wai kana jin daɗin shi ne.”

“Eh!

“Nima zan haɗa na sha.”

Vata tsaya jin avin da zai ce mata va ta bar ɗakin,saida ta shiga ɗakin ta sanan ta sauko kicin ɗin ,cup biyu ta haɗa duk ta saka lemon tsamin sanan ta nufi ɗakin.

Da sallama a bakinta,ta isa ɗakin,can ƙasa ya amsa mata gaban shi ta je ta ajiye mishi sanan ta ɗau na ta.

“Kin saka ma naki lemon tsamin ne?

“Eh baka ce akwai daɗi va.”

“Magani ne fah kuma bai kama ta ki sha ba.”

“maganin me? ko ma na meye tunda kai kasha nima zan iya sha,oh yanzu gobe iwar haka muna can garin ƴan gayu.”

Kallon ta kawai ya ke yi yadda ta ke jero zance wani kan wani,murmushi kawai yake yi,kuma taƙi dainawa zai yi ta ke yi.

Can ta gaji lokacin ta sanye lipton miƙa tayi da sauri yai ƙasa da kai dan baya son yaji wani abu.

Cikin muryar jin barci ta ce,”Ni barci na ke ji kar na makara gobe.”

Tashi tayi ta hau akan gadon yana kallon ta,ta rufe da bargo,murmushi kawai yake yi yana jin wani irin baƙon yanayi yana kai wa zuciyar shi ziyara.

Bai tsaya wani tunani ba ya kwanta nan da nan barci yai awan gaba da shi.

>>>><<<<

Kamar dai kullum yau ma hakan ita ta fara tashi da jin kiran sallar farko na asuba,bata tsaya tashin shi ba ta fita ɗakinta,ta nufa na zuwa ta fara haɗa ƴan abubuwan da zata naima Dady ya ce gidan akwai kayan sakawa amma saboda tsoro zu ɗau abinda zasu bukata,haka ta haɗa abubuwan ta a cikin akwati duk abinda tasan zata buƙata,tana gamawa ta shiga bayi tai alwala,da ta fito saida tayi nafila sanan ta wuce ɗakin shi tashin shi tayi dan lokacin an kira sallah,yana tashi ya shiga yai wanka ya ɗauro alwala,ko kafin ya fito ta fara gyara ɗakin,yana fitowa ya tafi masallaci ,ita kuwa ta gyara ɗakin tsab.

Yana dawowa Dady ya iso dan shi zai kai su tashar jirgin,tara da hajia su ka zo dan ta ƙara yi musu sallama basu wani ɓata lokaci ba suka ɗau hanyar ,saura minti hudu jirgin ya tashi,hajia da Sabreen kuwa sun sha kuka.
????????Wai sai ƙasar turkey.

~~~~~~~~~~~~~

“Ke dan allah ki kwantar da hankalin ki wahalar da muka yi ba zata tafi a vanza ba,kawai dai yanzu kiyi ta kokari ki samu wayar shi yana jin muryar ki aiki zai fara,idan ya so zai ki bishi ƙasar ma.”

Ita kuwa Haulat ɗin wacce ta zuba uban tagumi a gaban Momyn tana hawaye da wayar a hannun ta.

Dafa ta momy tayi,”Ki kwantar da hankalin ki idan sun sauka ki ƙara kira ,karki manta ba duk abinda kika faɗa shikenan to meye da damuwa.”

“Kina ganin zai ɗau wayar kuwa.”

“Dolen shi ba,ai ki fara shirin zuwa ƙasar turkey private zaki hau ya kai ki yau ɗinnan komai dare.”

“Taya Momy.”

“Wai yaushe kika zama banza ban sa ni ba,kuna yin waya ya turo miki kuɗi ki bishi.”

“Je ki fara shiri ma,kuma idan jin je karki rama ma ƴar iskar matar ta shi,ku ƙuntata mata dan uban ta duk ita ce ta bamu matsala.”

Wani irin farin ciki ya mamaye Haulat da rawar jiki ta tashi ta fara shiriii.

~~~~~~~~~~~~~

Ƙasar turkey kyakyyawar kasa ce mai abubuwan birgewa,yanayin tsarin garin da yadda al-adar mutanan garin ya ke shi yafi komai birgewa.

Tunda suka zauko Sabreen ta fara zare ido tana kallo riƙe shi tayi gamm kamar wani zai ƙwace shi.

Wata tsadaddiyar motor da wani ɗan afirka a cikin ta yazo tarbar su,cikin harshen turanci ya gaida su cikin girmamawa,suna shiga motor ta lafe a jikin shi.

“Lafiya ko garin bai miki ba ne?

gaɗa kai tayi alamar a’a,taɓa jikin ta yayi,dan ya lura yanayinta ya canza da zuwan su.

Cikin nuna kulawa ya ce,”Baki da lafiya ne?

“A’a lafiya lau,yaya karka barni plss.”

Saida gaban shi yai mummunan faɗuwa,”Sabreen ba zan barki ba ki kwantar da hankalin ki ,amana ce a guri na,taya zan bar ki na je ina? kin san ban isa na ce gida babu ke ba,ke fa ƴar uwata ce ,zan kasance da ke har abada.” cikin sigar lallashi ta tausasawa yayi magnar.

Ɗago da kanta tayi wanda ta kwantar da shi akan ka faɗar shi,ta kalle shi yaƙe tayi.

A zahirin gaskiya tunda suka zauko dga jirgin faɗuwar gaba ya kamata jikin ta ya mutu,wani irin yanayi mara daɗi ya shiga zuciyarta.

Sun daɗe zuna tafiya a motor bata ɗago ba balle ta kalla yanayin garin shi ma haka,wani irin abu mara daɗi ya ke ji a ranshi.

Wani hamshaƙin gida dan madaidaici direban ya nufa yana isa mai gadin wanda shi ma ɗan africa ne ya buɗe musu hamshaƙin get ɗin,karamin gida ne amm huɗuwar ta yi yawa,wanda idan kwatantawa zai ya ɗauke mu fiye da shafi biyar.

Yana tsayar da motorn ya fito da sauri ya buɗe musu,hannunwan ta ya riƙo su ka fito cikin su ba wanda ya tsaya kallon gidan sun bi bayan mutumin da ya kawo ne ,sun ɗanyi tafiya kafin suka isa cikin lafiyayyan falon suna isa ya tsaya,cikin harshen yar musu barka da zuwa ya juya.

Zaunar da ita yayi a kan kujerar da ke fallon kallon falon ya tsaya yi ,ya mishi kyau ainun,ita ma kallon falon tayi tai gutun murmushi ta ce,”Gidan yayi kyau sosai.”

Kallon ta yayi ya sakar mata murmushi,”Nima yamin kyau,tashi mu je ɗaki muyi wanka muyi sallah sai mu fito mu kewa ya mu ƙara ganin gidan ko.”

“Eh!

Hannunta ya riƙo suka nufi wata hanya wacce su ke tunanin ita zata sada su da ɗakin kwana,hakan kuwa ɗaku na ukku ne a jere,fuɗe wanda su ke kusa yayi suka shiga,ai nan suka yada ido dan haɗuwar ɗakin har yafi falon kyau gashi babba harda tavi da kujeru a ɗakin sai gadon ne ɗan ƙarami.

Basu wani tsaya ɓata lokaci ba,gurin ajiyar kaya ya nufa yana duvawa ya gane ɗakin ta ne,dan kayan mata ne.

“Ki shiga bayi kiyi wanka.” ya faɗa haɗe da nuna mata bayin ,ba musu ta shiga,tana shiga ya fita ɗayan ɗakin ya shiga yana dubawa kowa yaga ɗakin shi ne,bayi ya shiga shi ba wani tsayawa kallon haɗuwar bayin yayi ba,dan ba yau ba ne farkon ganin gida irin shi ba.

ita kuwa ta zuba ƙauyanci kamar wacce ta fito a zaria ba abuja ba.

Da ta fito baya ɗakin sakin jikin ta tayi ta saka kaya duguwar riga cikin wacce ta tawo da ita,sallah ta fara yi.

Shi ma hakan sallah ya fara yi,tun yana sallah yake jin ringin ɗin wayar shi har ya idar ana kira,kafin ya idar anyi jira goma sha bakwai,yana idarwa ya nufi gurin wayar sabowar number ya gani,gaban shi yai mummunan faɗuwa yana gurin har aka ƙara kira amma bai ɗauka ba,number ya zubawa ido number 9j ne bawai yasan mai number ba ne,yadda gaban shi ke mugun faɗuwa ne yasa ya kasa ɗauka,wani kiran ya ƙara shigowa,yai jan hali ya ɗau wayar da kalmar “Hello” a bakin shi..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button