HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

.

????love u guys irin over ɗin nan fah.
Sir Dboy
[12/23, 2:26 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/23, 2:27 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

 

Page 19
…………………………………………………………

_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{MUTANE SUNA DA HALIN MUTUM BIYU NE; NA KIRKI TSARE DOKA MAI ‘KIMA A WAJEN ALLAAH, KO BANZA MARA RABO DA ‘KIMA A WAJENSA.}*_

“`[Sahihul Jaami’i;7867]“`
~~
_Wannan hadisin yana nuna mana cewa shi dan Adam a halinsa dayan abu biyu ne; ko dai ya zama na kirki mai tsoron Allaah ko kuma ya zama na banza mara qima da rabo a wajen Allaah. Allaah Ya sanya mu daga cikin masu halin kirki. Allaahu a’alam._

“`Allah ta’ala yasa mudace“`

________________________

A tare su ka ce, “Me ya faru da ita?

Farrah ta ruɗe sama kawai ta ke nuna musu,cikin inda-inda ta ce,”Sabreen bata da lafiy…

Tun kafin ta rufe baki sun bar gurin saman su ka hau da sauri,suna zuwa su kai kanta lokacin zazzaɓin ya tsanan ta.

“Ƴar aljanna!
Gaba ɗaya hajia ta ruɗe,momy ce tai ƙarfin hali ta ɗauke ta,da gudu su ka fita da ita dukkan su,su na zuwa su ka shiga motor direba ya ja su.

Su na isa asibitin doc zain ya tarbe su,alluran barci yai mata,duk suna tsaye a gurin bayan ya gama ƴan abubuwan shi,sanan ya juyo ya kalle su.

“Momy Hajia akwai damuwa a tare da ita,ban son shiga lamarin da ba nawa ba,ba ita ba ce matar Naufal? kuma kamar ita yai ma laifi?amma ta hakura ta yafe mishi ba lallai sai ya zauna da ita ba idan ba ku san haka,amma yana buƙatar ku yafe mishi yana cikin wani hali ƙiris zuciyar shi ke jira ta fashe,ɗazun bayan fitar ku ya kalle Farrah,ya farka saida yayi zuma sama da ashirin da aman jini da ƙyar mu ka samu yayi barci.”

Tunda ya fara magana jikin su yayi sanyi,hatta hajia saida tayi kwalla farrah kuwa kuka me ƙarfi ne ya kama ta,Allah sarki momy kukan zuci kawai ta ke yi.

Shi kuwa doc ta zain ganin kalaman shi sun shiga jikin sui yasa ya fita daga ɗakin.

~~~~~~~~~~~~~

Haulat kuwa a ƙasa ta taka har unguwar su,kamar wata mahaukaciya tana tafiya tana surutu ga hawaye,tana isa gidan su ta fara jin ihuuu yana tashi,gigicewa tayi jin muryar me ihuun da gudu ta faɗa cikin gidan.

“Haulat nasara a jini na ta ke,ko yanzu na ci nasara,kin gani kin gani,ina ita yarinyar?

Momy ke wanan maganar tana rawa duk ta raba jikin ta da kaya,alamun hauka ƙarara.

Sakina ita da Salma sai kuka su ke yi,sun kasa riƙe ta gashi sai ɓarna ta ke duk ta fasa glass ta yanke hannuwan ta.

Kamar gunki haka Haulat ta koma hawayen da na sani sun wanke fuskarta,”Momy mun cuci kan mu,ba muyi nasara ba ,momy”

Ita kuwa momy sai hauka ta ke yi tana rawa tana ihuu sun yi nasara,da ƙyar salma da sakina su riƙe ta ,a ɗaki su ku kulle ta.

Sakina ta fashe da kuka,”Sanda na ke gaya mu ku,baku saurare ni ba,tun yanzun kenan a duniya,ga haƙƙin mutanan da ke kanku wanda allah ba zai iya yafe mu ku shi ba,yanzu su waye da nasara? kun mata duk nisan jifa ƙasa zai dawo ai…

Luuu Haulat ta faɗi kasa zumamma wanda zuman ne ya katse sakina maganar da ta ke yi,a ruɗe su ka je gurin ta su na ihuuu.

~~~~~~~~~~~~~

A hankali ta fara buɗe nauyayan idanuwan ta,sama-sama ta fara ganin mutanan da ke ɗakin.

“Dady Yaya”dan Allah dan annabi hajia.”

“Ya isa kwanta kin ji ki kwantar da hankalin ki.”

Zaune ta tashi tana hawaye,”A’a Dady dan allah yaya zai mutu ba wllh bashi da laifi dan ..

“Shikenan!

Dukkan su sunji daɗi da har su ka kasa ɓoyewa,ko wanne su fuska ɗauke da annuri hatta hajia.

Sabreen kuwa rungume Dady tayi tana kukan jin daɗi,”Na gode dady muje mu gan shi.”

Daman a lokacin doc zain yana nan yai musu jagora har ɗakin,hatta dady sai da ya tausaya mishi ganin halin da ya ke ciki,Dady da momy ne kawai ba su yi kuka ba,momy na zuciya tayi.

Kusa da shi Sabreen ta matsa tana kuka mai ratsa zuciya,kan shi ta taɓa a hankali ta ce,”Yaya!

Kamar daga zama ya fara jin muryar ta,lokaci ɗaya yaji zuciyar shi wani haske da daɗi yana kai mata ziyara,koƙari ya fara yi ya buɗe idanuwan shi,dan ya kan ta.

Sama-Sama ya fara ganin dushi-dushi,ganin hakan yasa Sabreen ta yin wani yalwataccen murmushi.

a kan fuskarta idanuwan shi su ka zauka,kallon-kallon su kai wa juna,wani irin abu ke ziyarar zuciyar shi,duk sai yaji ya manta da komai.

Wasu hawayen ne su ka fito mata,”Ya jikin?

Hannu ya miƙa mata ta riƙe alamar ta zauna kusa da shi yai mata,zaman tayi kusa da shi,da ido yai mata alama da ta goge hawayen ta.

Su kuwa tsayawa kallon ikon allah su ka yi,abin ya basu mamaki ganin wata ɓoyayyar soyayya a idanuwan su,momy kuwa ita da farrah sun fi kowa jin daɗi ,Dady kuwa mamaki ne ya kama shi,”To daman yana mata irin wanan son kuma zai aikata abinda yayi.”,abinda zuciyar shi ke gaya mishi kenan.

Su kuwa sun manta da akwai wasu muta ne a ɗakin kallon juna kawai su ke,su na fira da ido.

Farrah ce ta ƙarasa gurin basu san da zuwan ta ba,murmushi tayi ta ce,”Yaya ya jikin?

Kallon ta yayi ya ɗaga mata kai,daidai da haɗuwar idon shi da momy,da sauri yai ƙasa da kai,zuma ya fara yi,a ruɗe su ka ƙaraso gurin shi harda Dady duk sun ruɗe,ita kuwa sabreen kuka ta fara yi.

Aman jini ya fara yi nan da nan numfashin shi ya fara koƙarin fita,Ihuu su ka yi gaba ɗayan su banda Dady,jin ihuun yasa doc zain ya shigo a ruɗe ya kore su,da ƙyar dady ya ja Sabreen dan ƙin fita tayi.

nan da nan doc zain ya fara koƙarin taimakon rayuwar shi.

su kuwa su na waje Sabreen sai rusa kuka ta ke yi an kasa samun wanda zai bata hakuri,dan kuwa kukan ya ke yi.

Hankalin momy ya tashi ainun,tasan ganin ta ɗin ta yayi ne,”Taya anya kuwa idan har da gani da zuciyar shi zata buga kenan abinda ya aikata ne wanda na ganshi ya tuno.” sai hawaye,”Hm koma mene ba da san ran ka ba ne Naufal mutumin da baibi mata a india ba sai a nan.”duk a zuciyarta taita maganganu tana hawaye.

Hajia kuwa faɗi ta ke,”Allah sarki Naufal mun yafe ma,kadɗara ce.”

Shi kan shi Dady jikin shi duk ya mutu.

ko doc zain ya fito bayan ya dau lokaci mai tsawa, yana fitowa su ki kan shi.

“Na shaida mu kar ya farka da wani tunani wanda zai fada mishi rai ko ya ga wani avu, a gaskiya yanzun idan ya farka da irin haka to gaskiya va zamu iya komai va, yanzu kawai ku tafi gida dan va zaku samu damar ganin shi ba.”

Gaba dayan su jikin su ya mutu sun tausaya mishi ainun, savreen kuwa sai rusa kuka ta ke yi, Dady ne yai karfin halin jan su,haka su ka koma gida ko wanne jiki a mace hatta dadyn ma.

Ba wanda ya saurari wani kowa da kan shi yayi, da kyar sabreen ta samu tayi sallar isha’i ta kwanta bayan ta kama kwaranyo mishi addu’a, ba ta yi wani barci va ,tana jin kiran sallah ta tashi tayi…

Abubuwa sun dan min yawa kuyi hakuri da wanan

.
[12/23, 2:27 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/23, 2:29 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA* ????

*By*
*Fatima* *Batulah*

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

Page 20

…………………………………
Addu’a ga Wanda Ya ce Maka: Allah Ya yi Maka Albarka:
وَفِيكَ بَارَكَ اللهُ.
wa fika barakallah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button