NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Kai ma Allah ya yi maka albarka.
…………………………………
Zaune ta ke akan sallaya tana kuka tana cewa,”Allah na tuba! ka yafe min duk laifi na ne da ban shiga rayuwar shi ba ,da hakan bata faru ba,nayi kuskure.”
“Ba wani kuskuren da kika yi Sabreen ,ke ce alkairi a rayuwar shi,Yaya Naufal yana son ki Sabreen.”
Kallon Farrah tayi da jajayen idanuwanta ta ce,”A’a Farrah baya so na malama Haulat ya ke so ba ni ba..
Tass ta kwashe dukkan labarin abinda ya faru tsanin ta da malama haulat har dalillin da yasa ta ce zata aure shi bayan bata son shi baya son ta.
Saida Farrah ta sauke raguwar ajiyar zuciya sanan ta ce,”Sai yanzu na fahimce wani abu,amma kuma zargi ne kuma ba komai,amma zan yi bincike akai sosai.”
“Me kike zargi?
“Ba komai zan gaya miki komai idan na tabbatar da bincike na,Sabreen abinda kike yi daidai ne,kuma yaya na son ki.”
“Baya so na Farrah.”
“Hm yana son ki,ke ma kina son shi.”
zare ido tayi,”Me? rufamin asiri yaya ba zai so ni ba,nima bana son shi.”
Ganin ba zata iya fahimtar da ita ba yasa ta ce,”Yanzu ki tashi mu je gurin shi.”
“Ni ai tun dazun na shirya ,ke na ke jira.”
Murmushi kawai Farrah tayi,tana mamakin sabreen da bata gane abubuwa sosai.
Tun da safe momy ta tashi daman ba wani barcin kirki tayi ba,tunanin ɗan ta ya hana ta yin barci,ba ita kaɗai ba hatta Dady saida yayi tunani.
Tun da safe momy ta,tashi ta haɗa musu abinci har wanda zasu kai asibiti,saida ta gama haɗa komai ta shirya,tana cikin shirya abinvi hajia ta shigo kicin ɗin a tare su ka gama.
Suna zaune a falon su sabreen su ka zauko kasa,cikin girmamawa su ka gaida su.
Momy ta kalle Sabreen so da kaunar ta yana ƙara shiga ran ta,murmushi tayi mata alama da ta zo gurin ta tai mata,tashi tayi daga kusa da farrah ta dawo inda momyn ta ke.
“Sabreen ya jikin?
“Da sauƙi momy.”
“Masha allah ki kwantar da hankalin ki sabreen karki sawa kan ki damuwa kin ji,yau idan mun je asibitin ke kadai zaki shiga,dan na ga alama ganin mu ke ɗaga mishi hankali.”
Kai ta ɗaga ta ce,”To momy.”
“Yawwa allah yai miki albarka.”
“Amin.”
“Momy ni fa ce,”cewar farrah haɗe da turo baki.
Murmushi momy tayi ta ce,”Allah yai mu ku albarka baki ɗayan ku.”
A tare su ka amsa da ,”Amin.”
Saida Dady ya fito sanan suka ci abinci bayan sun gaisa,Sabreen na jikin shi yana bata a baki kamar wata yarinya,saida ya tabbatar da ci sosai sanan ya gyale ta.
Suna gama ci su ka tashi,motor biyu su ka yi,Dady da su Sabreen da farrah a motor shi,Momy ita da Hajia.
Suna isa asibitin su ka naimi doc zain,bayan sun gaisa ya kalle Dady ya ce mishi,”Tun jiya bai farka ba,ina jin tsoron ya farka ne da wani ɓacen rai a zuciyar shi gaskiya zaku iya..
Katse shi Dady yayi da faɗin,”Dan Allah doc kai mishi allurar da zata tashi shi ,matar shi kaɗai zai gani kuma nasan ganin ta zai kwantar mishi da hankali kamar yadda ita ma ganin shi zai samar mata natsuwa.”
“Okk ba matsala,amma plss karki mishi maganar da zata ɗaga mishi hankali,”ya kare maganar yana kallon Sabreen.
Ɗaga mishi kai kawai tayi alamar eh zata yi yadda ya faɗa.
A tare su ka fita daga office ɗin na shi,har sun kusa ƙarasawa ya juyo ya kalle su ya ce,”Ku tsaya daga nan plss.”
Ba abinda su ka ce mishi illa bin umarnin shi da su ka yi kawai,ita kuwa binshi tayi da sauri yana buɗe kofar ta shiga ita ma.
Saida yai mishi wata allura,kamar a jikin ta za’a yi taji,yana kama allurar ya fita ya barta ita kaɗai.
Akan gadon ta zauna har jikin su ya na taɓa juna,hannuwan ta ɗaura a saman kan shi,kwantaccen baƙin gashin shi mai laushi ta fara shafawa,cikin wata irin murya ta ce,”Miji na!
Kai tsaye muryarta ta kai zuciyar shi,wanda hakan ya harfar mishi da jin daɗi wanda saƙon zuciyar ya isa fuskar shi.
Murmushi tayi ganin murmushi a fuskar shi,ta ƙara faɗin,”Mijina! ka buɗe idon ka,Sabreen ce matar ka!
Murmushin fuskar shi ya ƙara faɗaɗa idanuwan shi su ka fara koƙarin buɗewa bakin shi ya fara motsi.
Dushi-dushi ya fara buɗe nauyayan idanuwan shi wanda har yanzun bakin shi yana motsi.
“Sabreen! ya faɗa tare da sauke idanuwan shi a kan ta,ba wai taji sautin muryar ba ne,ta ga yadda bakin shi ya nuna alamar ita ya kira.
Kallon juna su ka fara yi wani irin baƙon yanayi yana ziyarta ko wannen su ,sun daɗe a haka kafin ta yanke shirun da faɗin,”Ka ji sauki dan allah mu koma gida ga ji,gidan ba daɗi kasan na xaba da kai,ko kana son nayi ta kuka ne?
Murmushi yayi mai ƙyayatarwa muryar ta na mishi daɗi musaman yadda idam tana magana cikin sauri bata tsayawa sauke numfashi.
Lumshe ido kawai yake yi yana kallon ta tana magana lips ɗin ya zubawa ido yana ganin yadda ta ke sarrafa su,yakan rasa dalilin da yasa idan yana tare da ita yakan manta komai da kowa.
“Ka ji Sauƙi ko! mu tafi gida,ba zan ɗinga damun ka ba.”
Murmushi kawai yake yi.
Turo baki tayi ta ce,”Ba xaka yi magana ba ne,zan tafi fah.”
Da sauri ya riƙo hannun ta,saida wani abu ya tsikari zuciyarshi a hankali dan baiyi tunanin zata ji ba ya ce,”Pls stay with me,mai xan ce?
Dariya ta fashe da ita,a ranta tana faɗin,”Ba xaka canza ba halitta ce wanan iyayin na ka. mutum ba lafiya ji yadda ya ke magana.”
Ganin ta fara dariya yasa shi ma ya fara duk da sautin nashi baya fitowa sosai ita kaɗai ta ke ji.
Kallon kallo su Dady ke wa juna dan jin dariyar Sabreen ƙarara mamakin su ya baiyana,momy kuwa da hajia da farrah sai washe baki su ke yi,shi kuwa dady mamaki ne ke ƙara kamashi matuƙa.
Doc zain ne ya zo inda su ke ,shi ma fuskar shi ɗauke da annuri ya ce musu,”Kun ji ko? suna matuƙar son juna,wanan shi ne maganin shi,am srry to say,ba zaku gan shi ba har sai ciwon yayi sauƙi ,amma ita dole a barta anan,yanzu zaku iya tafiya,zan shigar da abincin a bashi,amma zuwa anjima zaku iya dawowa ku ɗauke ta idan ya kwanta.”
Ba wanda yaji ba daɗi a ranshi sai ma jin daɗin da su ka yi,dan samun sauƙin shi na tattare da sabreen ɗin.
Kallon shi Dady yayi fuskar ɗauke da annuri ya ce,”Ba komai doc mun gode sosai kuma mun ji daɗi allah ya ƙara mishi lafiya.”
A tare su ka amsa da ,”Amin ya Allah!,su juyo abin su .
Murmushi yayi doc zain yayi ya ɗau kular abincin ya shiga da ita ɗakin,da sallama ya shiga dariyar da su ke bai bari sun ji sallamar ba.
” Hmm irin wanan love!
A tare su kalle shi suna ƙoƙarin tsagaita dariyar su,shi ma murmushin yayi ya ce,”To ga abinci ya shi sai ya sha magani yadda za ku tafi gida da sauri.”
Murmushi Sabreen tayi ta ce,”To doc nima na ƙagara mu tafi shi ne dai ya ke son zaman.”
Bai ce komai ba,ya fita abin shi yana murmushi.
Kular abincin da buɗe farfeson dan kalin turawa ne da hanta,sai tashin ƙamshi su ke yi, zubu mishi tayi.
“Au sai ka ɗan tashi zaune kaɗan,”Tana faɗa ta kai hannuwan ta kafaɗar shi da zummar taimakon shi ya ɗan zauna kaɗan.
Tsigar jikin shi ta tashi yarr,lumshe ido kawai yayi,wani abu ya mishi yawo a zuciya.
Ɗauko abincin tayi “Ka fuɗe baki da ido,ka ci abinci.”
Buɗe idanuwan yayi,amma ya ƙi buɗe bakin,marairai ce fuska tayi alamar shagwaɓa.
Murmushi yayi komai Sabreen tayi burge shi yake yi,ba wai abincin ba ne ba zai iya ci ba,yana son ya wanke baki ne.
“Ba ka son muje gida ko?
“Ina so ko dan.. sai yai shiru.
Bata naimi ƙarin bayani akan abinda ya kasa faɗa ba,ta ce,”To ka ci dan allah,”cikin shagwaɓa ta ƙarasa maganar.