NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Baki na ba’a wanke ba.”
“Hm kai ana ta kai kana ta kaya.”,a ran ta ta faɗa a fili kuwa cewa tayi,”Toh bari na kawo ma roba da ruwa ko.”
Tana faɗa ta ajiye abincin ta nufi bayin,maclean da brush,sai ta ɗibu ruwa a wani cup sai ta tawo da ɗan ƙaramin ruba kamar bahu me faɗi.
Da ɗayan hannun ya ɗan wanke bakin,taɓe baki kawai ta ke yi ganin haƙuran basu yi datti ba,ya gama ta maida da su bayin,ta zubar da ruwan.
Har ta shiga bayin ta fito idanuwan shi su na kanta.
“To bismillah! faɗa haɗe ta ɗan murmushi,shi ma murmushin yayi ya buɗe bakin ta fara bashi,a hankali yake ci,ka ɗauka haɗiyewa kawai ya ke yi,ba taunawa ba.
Yaci sosai shi kan shi bai san ya ci da yawa ba,”Yawwa nawan saura magani,”yana gani ta ɓallo magani dan daman likitan ya gaya mata yadda zata bashi.
Miƙa mishi tayi ba musu ya amsa ya sha,saida ta ɗan gyara gurin sanan ta dawo ta zauna.
Murmushi tayi ganin irin kallon da yake mata,gashi tana son yi mishi maganar su Dady tana jin tsoro.
“Ki ce wani Abu.”
Saida ta murmusha sanan ta ce,”To na gaji da magana ni kaɗai saidai kayi ta kallo na ka ƙi magana.”
“Ina jin daɗin yadda ya kike magana.”
Dariya tayi sosai ta ce,”nima ina jin daɗin yadda kake magan har dariya kake ban”
Lauya harshe tayi ta ce,Ki ce wani Abu,” ta fashe da dariya ta ce,”Haka kake magana fah.”
Dariya yayi yadda tayi maganar y mishi daɗi,suna nan zaune aka kira sallah da sauri ta tashi tayi yana kallon har da iddar tayi addu’a tana zaune a gurin ya ce,”Amin!
Bayan ta tashi ta dawo ta zauna,”Me kika roƙa ne?
“Me kuwa banda allah ya ba miji na lafiya.”
Dariya yayi yana jin wani irin farinciki na ratsa zuciyar shi,duk ya manta da komai da kowa.
A haka su ka cigaba da fira cikin farinciki da jin daɗi musamman Sabreen duk wata kalma da zai faɗa dariya ta ke bata,har lokacin la’asar ta tashi tayi sallah yana kallon ta har da idar ta dawo ta zauna suka cigaba da fira jikin jin daɗi.
Bayan maqrib su Dady su ka dawo tare da abinci,ko wannen su yana son ganin naufal amma suna tunanin ganin zai iya jan matsala shiyasa ba wanda ya tunkari wani da maganar,kai tsaye office ɗin doctor zain su ka nufa bayan sun gaisa Dady ya ce,”Doctor ya koƙari ya me jikin?
Fuskar ɗauke da annuri ya ce,”Alhmadulilah! jiki yayi sauƙi sosai abin mamaki gaskiya yaran nan su na son junan su sosai,amma zaku ƙara hakuri da rashin ganin shi har nan da kwana biyu da zuwa lokacin insha allah jikin zai yi sauki sosai.”
“Ba komai likita allah ya ƙara sauki,am..zamu iya ganin sabreen ɗin?
“Why not bari na kira ta,”yana gama faɗa ya fita.
Da sallama ya isa ɗakin fuskar shi ɗauke da annuri ganin yadda su ke fira ko gajiya basu yi abin ban sha’awa.
“Kai wanan irin so haka.”
Murmushi Sabreen tayi a ranta ta ce,”Wani so ana zaune ƙalau.”
A fili kuwa murmushi tayi ta ce,”Ya koƙari doctor?
Saida Naufal yaji wani irin abu ya soke shi a zuciya ganin yadda sabreen ta ke zubawa doctor xain murmushi,shi ma zai murmushin yake yi,lokaci ɗaya ya ɗaure rai,yai ƙasa da kai.
“Alhmdulilah! ya me jiki?
“Jiki yayi sauƙi.”
“Ai kuwa naga alama,allah ya ƙara sauƙi Sabreen ki zo ki amsar mishi magani.”,yana faɗa ya juyo bai tsaya jin amsar da xata ba shi ba.
Wani irin haushi mai ɗauke da mugun kishi ya kama Naufal taya zai ce ta bi shi,kuma harda kiran sunan ta,a hankali yaji zuciyar shi ta fara mishi zafi.
Hannuwan ta,ta ɗaura kan ƙirjin shi,lumshe ido ya fara yi yana ajiyar zuciya a hankali ga tsigar jikin shi ta ke tashi.
“Ya dai magani zan amso fah,koma ba daɗewa zan yi ba,wai ba ka son gaji sauƙi ne kafi son ganin mu cikin damuwa.”
har lokacin bai buɗe ido ba,a hankali yake sauke ajiyar zuciya,muryarta na ratsa kunnan shi tana shiga cikin zuciyar shi.
“Ya hakuri yanzun zan dawo.”
Jikin shi ya mutu bai jin zai iya yin magana kai kawai ya ɗaga mata alamar eh,ganin hakan yasa ta janye hannuwanta daga ƙirjin shi,ta fita saida yaji wani iri.
Kai tsaye office ɗin ta nufa,ganin su dady yasa ta washe baki ,gurin dady tayi ta rungume shi tana jin son shi na ratsa sassan jikin ta,sun daɗe rungume da juna kafin su ka janye,cikin jin daɗi da soyayya su ka gaisa da kowa,bayan sun gama gaisawan zasu tafi har bakin motor ta raka su,Dady ya kalle ta ya ce,”Sabreen Kin cika ƴa abin alfahari allah yai miki albarka ya ba mijin ki lafiya da zuri’a ɗaiyaba.”
Saida tayi ƙasa da kai sanan ta ce,”Amin Dady n gode.”
Duk sukai sallama da juna su ka tafi,kamar tayi kuka ta daɗe a gurin kafin su ka tafi,saida ta ɗauki abincin sanan ta wuce ɗakin,na zuwa yayi barci,kusa da shi ta zauna ta ƙura ma fuskar shi ido tana jin wani irin abu a zuciyar shi.
Har lokacin sallar isha’i bai tashi ba,har ta idar ta sallar shiru,ta ci abincin bai tashi ba,har ta gaji ta kwanta.
“Kiyi hakuri karki barni zan rayu da ke,ina buƙatar ki..”cikin wata irin sigar numfashi mai ɗauke da nishin kuka yayi maganar.
“Ah..Ahh ..ni ka barni bana soo…
“Ɗan allah…”firgitt ya tashi yana nishi da haki ga wani irin abu da ya ke ji a zuciyar shi mara daɗi,idan da sabo ya ci ya saba da irin wanan mafarkin amma ya kasa savawa,ya daɗe yana sauke ajiyar numfashin ,kafin ya ɗago kan shi,a ɗayan gadon ya hango ta,tana barci kasancewar ɗakin da haske bata kashe wuta ba,ji yayi kamar ya tashi ya tunkare ta dan yana cikin tsananin sha’awa,da ƙyar ya iya faɗa da zuciyar shi akan tai hakuri,a haka har barci ɓarawo ya ɗauke shi.
Asubar fari sabreen ta tashi alwala tayi da tada sallah har ta idar da sallar asuba bai tashi ba,bayan ta idar ta tawo ta zauna kusa da shi,idanuwa ta zuba mishi,har ƙarfe tara naufal bai tashi ba,doctor zain ya shigo ya duba shi,har su Dady su ka xo bai tashi ba,sun daɗe kuma sun leƙo sun gan shi,har su ka tafi bai tashi ba.
.
Kuyi hakuri posting din dazu an samu tsallake sai dai Kuyi hakuri wlh sbd ba laifina bane nima a haka littafin yazo min.
.
[12/23, 2:29 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/23, 2:34 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA* ????
*By*
*Fatima* *Batulah*
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
Page 21 (last)
…………………………………
Asubar fari sabreen ta tashi alwala tayi da tada sallah har ta idar da sallar asuba bai tashi ba,bayan ta idar ta tawo ta zauna kusa da shi,idanuwa ta zuba mishi,har ƙarfe tara naufal bai tashi ba,doctor zain ya shigo ya duba shi,har su Dady su ka xo bai tashi ba,sun daɗe kuma sun leƙo sun gan shi,har su ka tafi bai tashi ba.
Ƙarfeɓgoma sha biyu da kwata daidai ya farka lokacin tana zaune kusa da shi akan kujera,akan fuskar ta idanuwan shi su ka ƙarasa buɗewa,murmushi tai mishi ,shi ma murmushin yai mata.
“Ka tashi? ya jikin? yau ka daɗe baka tashi ba,kasan yanzun ƙarfe nawa ne?abincin ka har yayi sanyi.”
Murmushi yayi wanda saida haƙuran shi su ka baiyana,ganin yadda ta ke magana ba ko tsayawa.
Tunowa yayi bashi da tsarki da sauri yai koƙarin miƙewa,taimakon shi tayi ya miƙe zaune,ta kalle shi ta ce,”Ya dai?
“Bani da tsarki zan yi wanka.”
“Baka da tsarki.” ta faɗa cikin rashin fahimtar inda ya dosa a mgnr tashi.
“Eh xanyi wankar tsarki bani da tsarki.”
Bata tambaye shi ta shige bayi,ta haɗa mishi komai da komai,sanan ta fito ta temaka mishi ya tashi ya shiga bayin,saida ta ƙara gyara gurin tsabb,bayan ya fito ya zauna ta sulale ta fita ganin yana koƙarin cire kaya a jikin ta,murmushi yayi kawai,ya saka kayan shi,yaji daɗin jikin shi sosai,kafin ta shigo har ya fara sallah,ko da ta ahigo ta ga yana sallat taji daɗi ,guri ta samu ta zauna tana kallon shi,saida yayi lzahar ta kwana ukku sanan ya idar,bayan ya idar ya dawo su ka zauna ta bashi abinci ya ci kaɗan sanan ya sha magani su ka cigaba da firar su cikin jin daɗi.