HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Yau kwanan Sabreen ukuu a asibiti tare da Naufal,yanzun kam jiki yayi sauƙi sosai da sosai,shaƙuwa ta shiga tsakanin su mai ƙarfi,musamman Naufal wanda ya gama tabbatar da ya kamo da ciwon son Sabreen,wanda yake jin duk wani fitar numfashin su tare su ke fita,ga wani irin mugun kishi.

Zaune ta ke kan kujera shi kuma yana zaune kan gado idanuwan shi duk sua kan ta,tunani ta ke yi a ran ta,”Ta ina zan fara mishi maganar su dady gashi yau za su zo gurin shi,yanzun ya zan yi,” ɗago wa tayi haɗe ido su ka yi tai murmushi murmushi da ido yai mata magana da lafiya kuwa dan ya ga fuskar ta akwai abinda ta ke son faɗi.

Saida ta ja garuwar ajiya zuciya sanan ta ce,”Ɗazun su Dady sun zo kana barci,”idanuwan ta suna kan shi dan taga yanayin da zai shiga.

ƙasa yayi da kai wani abu yana bijiro mishi a rai,ganin hakan yasa ta kama hannuwan shi ,ta raunana murya ta ce,”Dan allah karka ji wani abu wllahi dady da momy duk sun yafe ma,kaddara ce,ka kwantar da hankalin ka.”

Runtse idanuwan shi yayi abubuwan da suka faru suna dawo mishi,ahankali ya buɗe su,saida sabreen ta tsorata ganin yadda idanuwan su ka canza sukai jajir,rungume shi tayi,”Dan allah kayi hakuri kar wani abu ya same ka,ba wanda ke fushi da kai.”

A hankali yaji zuciyar shi tana mai sanyi,amma yana jin nauyin iyayen shi harda sabreen ɗin,saidai ya kasa gane dalilin da yasa ya aikata irin wanan ɗayan aikin ki,ji ya ke kamar ba shi ba,taya zai yi zina abinda ya tsana a duniya,wasu zafaffan hawaye sukai nasarar zubu mishi,ƙokarin yin magana yake yi amma maganar taƙi fitowa.

Kuka Sabreen ta fashe da shi,saida yaji wani radaɗi a ran shi,cikin kukan ta ce,”Dan allah kayi hakuri nasan ba laifin ka ba ne laifi na ne,bana sun su dady su zo su ganka a haka,kayi shiru.”

Shafa kan ta yayi yana jin zafin hawayen ta,tamkar shi ke yin su,janye ta yayi su ka fuskanci juna da ido yayi mata magana da tayi shiru,zuwa yanzu Sabreen ta iya magana da ido sosai ,ita ma da idon tayi mishi magana ta yayi hakuri ya natsu,share mata hawayen yayi,shiru su ka yi kowannen su yana ƙokarin samawar zuciyar shi.

Sun ɗau lokaci a haka suna kallon juna kafin sabreen ta janye jikin ta,kasa ce mata komai yayi duk da kasancewar ba ji daɗi ba,bayi ta shiga wa wanke fuska sanan ta fito,ta dawo ta zauna ɗan nisa da shi sanin su dady zasu iya zuwa any time,kallon ta kawai yake yi yana mamakin hali irin na ta,yasan ya mata mugun laifi amma bata nuna mishi ba ko kaɗan sanan har ta ke ɗaurawa kanta laifi,lallai yasan halin dady kuma ba xai manta kalaman shi ba,yanzu ya yafe mishi wanda ko shakka babu sabreen ɗin ta buƙaci haka,runtse idanuwan shi yayi yana ƙara jin wani irin mugun azababben son sabreen na ratsa zuciyar shi lallai ta haifu,shi kuma yaci amanar iyayen shi da marainiyar allah.
ganin yadda ya kulle ido yasa sabreen kiran sunan shi,”Ya Naufal!,kai tsaye zuciyar shi ta amsa saƙon muryarta,a hankali ya bude idon.
“Yah kayi hakuri dan all..
“Ke kin hakura.”
“Na hakura ai baka min laifin komai ba,ni ka hakura duk abinda haulat tayi dan na ji haushi ne sann…..

Sallamar su dady ne ya katse ta,da sauri ta ƙarasa gurin shi,amma ta kasa rungume shi,shi ne ya rungumu ta,shi kuwa naufal yana jin su yai ƙasa da kai wata irin kunya ta mameshi musamman momy.

Kowannen su kallon su naga naufal wanda yai ƙasa da kai,farrah ce ta fara ƙarasawa gurin shi,fuska ɗauke da annuri ta ce,”Brother ya jikin?

kan shi a ƙasa ya ce,”Da sauƙi sosai.”
“Allah ya kara sauki yaya.”,yaji daɗin yadda yaji tana mishi magana wanda hakan yasa ya ɗan ji daɗi.

“mutum india ya jikin? kabar amarya da damuwa gaskiya kaji sauƙi kasan bana son ganin damuwar ta,gashi ka siye zuciyar mu,” cikin dariya ta ƙasara maganar,dariya kowa yayi harda momy da dady wanda ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba.

Kusa da shi kaɗan momy ta matso shi kuwa har lokacin kan shi na ƙasa bai hadda ido da kowa ba,duk sun fahimce kunyar su yake ji sai tausayin shi ya ƙara kama su.
“Naufal ya ƙarfin jikin.”
Rawa bakin shi ya fara ji,”da saauƙƙii.”
ganin ya fara daburewa yasa ta faɗin,”Sauƙi sosai,dan yau zamu koma da kai gida, gidan duk ba daɗi “,idanuwan ta na kan shi,ta ƙarasa maganar,lumshe ido yayi yana jin wani irin sanyi a ranshi momy ce ke mishi magana kamar yadda ta saba kenan batai fushi da laifin da ya aikata ba,ganin yanayin da ya shiga yasa dady ƙarasowa inda yake ya ce,”Naufal halan dai baka son zuwa gida ne.”

Lokaci ɗaya yaji bugun zuciyar shi na ƙaruwa,koƙarin faɗa da numfashin shi ya fara yi wanda ke koƙarin ɗaukewa,ganin hakan ya ruɗa su dady sosai,zama yayi kusa da shi ya dafa kafaɗar shi ya ce,”Naufal gudun iyayen ka kake yi? kana tsoran mu ne? naufal ba ka da wasu bayan mu,ko meye ya faru mu iyayen ka ne,plss my son ka kwantar da hankalin ka,kaddara ce wanda,Allah da kan ce ya ce,” *Idan* *yana* *son* *mutum* *da* *alkairi* *sai* *ya* *jarabce* *shi* .”

Saida ya numfasa sanan ya ɗaura da faɗin,”Naufal allah yana son ka da alkairi ya jarabce ka dan ka kiyaye gaba,ba lalai abinda ka aikata ɗabi’ar ka ba ce,ko kana da kuɗirin aikata hakan ba saidan kaddara ce jarabta,mun ƙara fahimtar abubuwa da yawa faruwar wanan abun,wanda ni kai na,na gane kuskure na,na gaya ma irin waɗan nan kalaman ,wanda yanzun allah ya nuna min,kuskure na duk sanadin faruwan hakan,sry my son mubar hakan a matsayin kaddara,” jin hawaye na son fitowa daga fuskar shi yasa ya tsaida maganar badan ya gama ba.

Maganganun Dady sun yi tasiri sosai a jikin su,musamman naufal wanda yake jin shi wani iri tamkar an canza mishi duniya,rungume Dadyn yayi wasu zafafan hawaye su ka fara bin fuskar shi haɗe da kuka mai sauti,shi kan shi dadyn hawayen da yake makalewa su ka fito,haka zalika ko wanne da ke ɗakin saida ya kuka,sun daɗe a haka su na kuka ba wanda ya kalle wani balle yai kuƙarin ba da hakuri.

Shafa kan shi dady yayi yana faɗin,”Is okk kayi haba kai fa namiji ne.”
ai kamar ƙarawa naufal kukan ya ke yi, daɗi ya haifar mishi da kukan,jin ya ƙara sautin kukan yasa sabreen ta kara fashe da matsanaicin kuka,da sauri hankalin su ya dawo gare ta,dariya su ka yi dukkan su har dady da naufal ɗin sanin abinda yasa ƙara kukan.

“Ka gani ko,” dady ya faɗa yana kallon naufal ɗin wanda shi kuma idanuwan shi yana gurin sabreen.

“Ga gani ko,ni kai shiru dan allah dan ta samu tayi shiru ita ma,” cewar hajia wacce idanuwanta ke kan naufal.
fashe wa da dariya su kara yi,ita kuwa sabreen gurin momy tayi tana kuka ta rungume ta.

“Kiyi hakuri kin ji,ƙyale su ba ruwan mu da su,” cikin rarrashi tayi maganar su kuwa,dariya su ke kasa-kasa.

Sun sake jiki sosai kamar ba wani abun da ya fara,duk yadda su ka so naufal ya sake jiki ya kasa,dan ya kasa haɗa ido da kowa a cikin su,yana son kallon sabreen amma ya kasa dan tana jikim momy,yana dai ɗan taɓa fira kaɗan kaɗan,ba su damu ba dan sun san daman ba sai son mgn ba ne.

Tun daɗe suna fira jikin jin daɗi da nuna kulawa,wanda naufal yaji daɗi matuƙa wasai yake jin zuciyar shi sai wani daɗe ma ta jake ji mara misaltuwa,tun mantar da shi abinda ya faru,sun so a sallame su yau amma doctor zain ya ƙi,dole sai gobe shi kan shi naufal ɗin bai ji daɗi ba,ya so zuwa gida,amma ya nuna musu yau da gobe duk ɗaya ne a gurin allah,har gurin motor sabreen ta raka su farrah sai zolayarta ta ke yi bata kula ta,anan ma saida su ka rarrashe ta sanan ta ɗaurr bata yi kuka ba,tana tsaye har motor su ta bar asibitin sanan ta juya lokacin an kira sallar maqrib,tana zuwa ɗakin yana fitowa daga bayi,kallon juna su ka ji yayi kamar ya shekara bai ganta ba,murmushi su kai wa juna,da saure ya ɗauke kai tuno yayi alwala,sallaya ta shimfiɗa mishi ya hau,ita ma bayin ta shiga ta ɗauro alwala,baya da shi kaɗan ta tayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button