NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Tana zaune tana lazimi ya idar da sallar har ya gama lazimin ya juyo ƙura mata ido yayi yana jin wani abu yana tasar mishi,saida ya lumshe ido sanan ya ce cikin nakasassar muryar shi,”Me kika roƙar mana.”
ɗagowa tayi ta kalle haɗe da sakar mishi murmushi,”Wa zan ma addu’a idan ba ku ba,kai Dady hajia momy farrah,ku ne duniyata rayuwata.”
Tausin sabreen ya ƙara kama shi,”lallai bata waɗan da su ka fi mu,zan raini ki sabreen zan kula zan miki gata,kin min komai kin temaki ni kin min gata..
“Ya dai? ina kallon ka ɗazun kasa cin abinci ka yi.”
Tashi yayi ya ɗauke sallayar ya koma ya zauna,da ido ya kira ta,kusa da shi ta zo janyota jikin shi yayi ya rungume ta tsamm,wata irin ajiyar zuciya ya fara sauke wa,zuwa wanan lokacin sabreen ta saba da runguma gurin naufal,saidai bata bari yai mata kiss duk yadda ya so.
“Ka ci abinci ka sha magani “,ta faɗa tana kokarin janye jikin ta.
“Meye sa ki kuka ɗazun?
saida ta gama janye jikin ta sanan ta ce, “ba komai.”
Runtse ido yayi yana sauraran bugun zuciyar shi wanda ke buguwa da son sabreen,”Allah yasa ki amci da soyayyata sabreen ban san lokacin da zuciyata ta kamu da son ki ba,”a ran shi yai maganar.
Abincin ta zubo mishi kamar yadda ya saba ita ke bashi a baki,yaci sosai sanan ya sha magani,xama su ka yi su na jiran kiran sallar isha’i,ƙura mata idanuwan shi yayii,yana jin wani irin abu a ran shi kamar ya janyo ta ya haɗiye ta yake ji.
Jin kiran sallar yasa duk su ka tashi shi ya fara shiga yayi alwala sanan ita ma ta shiga,bayan sun idar da sallah,ya koma ya kwanta baya jin yin magana ita kuwa bata matsa mishi ba,dan ba wani damuwa tayi ba,kwanciya kawai su ka yi,kowa yana saƙar zuciya daga haka har barci yai awan gaba da su.
Kiran sallar farko ya tashi sabreen daga barci,tana tashi tayi addu’a sanan ta tashi gurin shi ta je dan tashin shi.
Shi kuwa a lokacin yana tsaka da mafarkin da ya saba yi,hannu ta kai ta taɓa shi,”Ka tashi lokacin sallah yayi.”
Can cikin mafarkin yake jin maganar,ga shi a lokacin su na cikin love.
“Ka tashi! da ƙarfi ta faɗa wanda yasa ya tashi da sauri,yana haki yana nishi,a kan fuskarta idanuwan shi su ka sauka,janyo ta yayi jikin shi ya rungume ta yana wani irin nishi.
“Yah lafiya kuwa,ko jikin ne?
Daman ba’a cikin haiyacin shi ya ke ba,yasan dai yaji tana magana amma bai fahimtar abinda ta ke faɗi,hankalin shi baya jikin shi,gaba ɗaya ya ruɗe ya fita haiyacin shi,ta ko’ina a jikin ta yake kai hannuwan shi,ruɗewa tayi jin yana kokarin zura hannuwan shi cikin rigarta,gashi ta ƙwatar kan ta.
Cikin zaƙuwa yake wasa da halittar ƙirjin ta,zuwa yanzu Naufal ya ruɗe ya fita haiyacin shi,koƙarin yaga mata riga ya fara yi,kuka ta sake me ɗan ƙarfi shi be san ma tana yi ba,ganin yana ƙara kuƙarin raba ta da kayan jikin ta yasa ta ganna mishi cizo a kafaɗa,yaji zafi hakan yasa ya sake ta,yana sakin ta,ta faɗa bayi da gudu tana kuka.
Da ƙarfin gaske yake sauke ajiyar zuciya,ji yake kamar yayi hauka kwanciya yayi ya runtse ido,wani abu ke bijiro mishi a rai,ji yayi ba zai iya hakura ba,ko kaɗan bai taɓa tunanin haka sabreen ta ke ba,zumbur ya miƙe sai kuma ya dawo ys zauna,yana kuƙarin ba zuciyar shi hakuri,safa da marwa ya fara yi,duk dan yaji sauƙin abinda yake ji,da ƙyar ya isa sarrafa zuciyar shi ta hakura.
Ita kuwa tana faɗawa bayin ta fashe da kuka wanda bata san dalilin yin shi ba,saida tayi me isarta sanan ta tashi ta ɗaura alwala,kasa fitowa tayi dan tsoro da kunyar shi ta ke ji gashi lokacin sallah na tafiya.
Ganin bata da niyar fitowa gashi lokaci yana yi kuma sai yayi wanka yasa ya fita daga ɗakin,dan ba zai iya magana ba,balle da ita.
Jin shiruuu yasa ta ɗan leƙo ganin ba kowa yasa ta fito,ta fara sallah,tana cikin sallah ya shigo bayi ya shiga,yana fitowa ya fara sallar shi ma.
Gaba ɗaya kunyar shi ta ke ji,kan ta a ƙasa ta ɗan kimtsa ɗakin,bayan ya idar da sallar ya dawo ya kwanta,dariya yayi ganin yadda ta jin kunyar shi a ran shi ya ce,”Akwai aiki kuwa.”
Ƙarfe bakwai daidai su Dady su ka iso asibitin ba su je office ɗin doc xain ba kai tsaye ɗakin suka nufo,suna zuwa sabreen ta washe baki tai kan su,cikin so da ƙaunar juna su ka gaisa,har naufal duk sun gaisa sosai cikin jin ɗaɗi,har lokacin naufal yana kula da sabreen bata yarda sun haɗa ido ba dariya ma ta ke bashi.
Basu tsaya ɓata lokaci ba,su ka tafi gurin doc xain dan ya basu takardar sallama,ya kuwa basu tare da musu fatan alkairi.
Har gurin motor doc zain ya raka su,yai musu sallama.
Naufal da Dady suna gama su kuma suna baya,har su ka isa gida,suna zuwa sabreen tai ɗakin farrah,shi ma ɗakin shi yayi,kowa ya watse.
“Yadai malama.”
Kallon farrah sabreen tayi haɗe da taɓe baki,ta juyar da kan ta kawai.
Dariya farrah tayi ta ce,”Yarinya kenan ai ina kula da ke a asibiti “,cikin dariyar da zolaya ta ƙarasa maganar.
“ke fah ƴar iskace,ƴar sa ido kawai.”
“Naji gayamin kun yi ne,kai lamarin ku sai ku asibitin ma.”
Da sauri Sabreen ta tashi ta fita ɗaga ɗakin tana faɗin,”Idan na biye miki wuta zaki kai mu banza ƴar isaka kawai.”
Dariya farrah tayi sosai,tana mmk hali irin n sabreen.
Tana fita tayi ɗakin hajia,saida hajia ta gama yi mata tsiya sanan ta barta,ta kwanta.
Shi ma yana zuwa ɗakin shi ya kwanta bayan yayi wanka da tunanin sabreen a ran shi,addu’a yake yi allah yasa dady ya barsu zu je gidan su.
Ita dai momy bata koma barci ba,abinci ta haɗa musu me rai da lafiya bayan ta gama ta koma ɗaki tayi wanka sanan ta fito,lokacin ƙarfe goma sha biyu da kwata,ɗakin Dady ta. shiga barci ta tarar yana yi tashin shi tayi,dan lokacin sallah yayi bayan ya tashi yayi wanka ya nufi ɗakin naufal dan su tafi masallaci tare,kafin naufal ya shirya an kira sallah,yana shiryawa su ka fita ya so ganin ta a falo .
Saida hajia ta idar da sallah sanan ta tashe ta,bayan tayi sallar ta koma ta kwanta hankali kwance ba tunanin komai a ranta.
Bayan sun dawo lokacin duk suna falo,ware idanuwa yake yi amma be hango ta ba,wani iri yaji yana marmarin ganin,”yanzun cikin nan mun dawo gida haka zaki tunda min,”ya faɗa a ran shi ,duk sai yaji da basu dawo ba.
Bayan sun zauna sun Dady ya tambaya ina sabreen,Hajia ta ce,”Barci ta ke yi.”
“Ayyah ku barta ta huta tana buƙatar hutu,da nayi tunanin ko yau zaku tafi sabon gidan ku wanda na siya.”
Wani irin daɗi ya kama naufal wanda saida ya kasa ɓoyewa kowa ya fahimce hakan.
“Amma ina jin ku ƙara hutawa bari dai sabreen ɗin ta tashi.”
Nan ma saida labarin zuciyar shi ya isa fuska,”Ya dady zai yi haka”,ya faɗa a ran shi,yanzu ba zai iya kayan wata mgn akan wanda dady yayi ba,da ya ce wani abu.
Har su ka gama cin abinci sabreen bata tashi ba,hankalin shiul baya gurin su,duk abinda su ka ce daga eh sai a’a ya ke cewa.
Tashi yayi ya shiga ɗaki,lokacin kowa ya tashi dady ya fita,wayar shi ya ɗauka,number farrah ya kira tana ginin kiran ta ɗauka da sauri.
“Ke turomin Number Sabreen yanzun nan”,yana gama faɗa ya kashe wayar.
Dariya farrah tayi,”Hm su yaya manya,ko number matar ta ka baka da shi,tana mgnr tana tura mishi number.
Tunda ya katse wayar ya ƙura ma wayar ido yana jikin numberta,ganin soƙon ya shigo ya buɗe da sauri,kiran number yayi a ƙufule,ringin wayar ta fara yi ,ya ƙagara ta ɗauka.
Lokacin tana barci bata ji kiran ba ,har wayar ta katse,kira ya ƙara yi amma bata ɗauka ba,wani jin zafi yaji a zuciyar shi,gaba ɗaya sai yaji ya ruɗe taya zata mishi haka,idan ta guje shi a lokacin da yake fuƙatar ta,bai san yadda zai yi ba.