NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Saboda riƙon alkawari da amana da biyayya irin na Rabi’u yasa ogan shi ya aure mishi ƴar shi Zainab ƴar ɗaya takk ƴar gata ga mahaifinta masu kuɗin gaske ne.
Bayan Auren Rabi’u ya ƙasa gaya ma ƴan uwan shi yayi aure gashi har matar da samu ciki,bayan shekara biyar ya lokacin zainab ta haifi Naufal yana d shekara huɗu,Rabi’u ya zo gida da sha tara na arxiƙi,kuma ya ƙasa gaya musu yayi aure,kwana biyu yayi ya koma abujan.
Bayan tafiyar shi hajia(maryam)ta matsa mishi yayi tunda abubuwa sun daidata gashi yana ta manyan ta.
Bayan shekara hudu da tafiyar Rabi’u aka kira shi yayan shi zaiyi aure,a lokacin ya yanke shawarar zuwa da iyalan shi.
Hakan kuwa ta faru ,basu nuna ɓacin ransu ba ko ƙaɗan sai ma farincikin da suka yi ga Naufal ya girma a lokacin yana da shekara takwas.
Bayan bikin muh’ad Da shekara ɗaya aka haifi Naufal,lokacin Haihuwar Naufal allah yayi wa mahaifiyarta rasuwa.
Sabreen ta taso a hanun hajia cikin jin dadi,har ta girma,ta fara zuwa makarantar firamari har ta kai aji shidda.
Rana ɗaya aka wayi gari Muh’d ya rasu ,hajia tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita dan tana matuƙar son shi,A lokacin da Rabi’u yaji yayi kuka kamar me dan duk duniya yafi son yayan shi sama da komai ,a lokacin Sabreen bata da wayau sosai.
Wanan ne dalilin dayasa suke matuƙar son Sabreen musamman Hajia dan son ɗanta ne ya koma kan sabreen ɗin gashi tana jin tausayin ta.
Bayan rasuwar shi da sati ɗaya Alhaji rabi’u yaso ya ɗauke hajia suka dawo Abuja.
Lokacin basu daɗe ba Naufal ya tafi india karatu.
Da aka kai Sabreen makaranta aka ce primary 3 za’a maidata,taƙi yarda da gyar da zauna a aji biyar.
Sabreen bata iya turanci ba,tana ji dai,ta tsana kilibaban mutum da mai nuna shi wani ne da son na iya ta gadara da taƙama.
wanan kenan nan to muje zuwa,kashh shadow tayi kira bari na tafi ma haɗe anjima⛹♀⛹♀.
.
Sir Dboy
[12/9, 1:05 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/9, 1:07 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: ???? *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
Page 3
___________________
Ta kai tsawon minti biyar a gurin da Malama Haulat ta barta , tsabar takaici da baƙin ciki, yasa ta ƙasa komawa cikin motor ,sai da direban ya fito ya mata magana sanan ta koma cikin motor.
Karfe hudu da rabi suka isa Gida,cikin ɓacin rai ta isa falon ,ko sallama bata yiba.
“Kee! ya buga mata tsawa.
Tsayawa chikk tayi bata kuma juyo ba,ganin bata da alamar juyowa yasa ya ƙara faɗin “Wai ke wacce irin yarinya ce kina ganin mutane ba zaki iya gaida su ba,kuma dan rashin tarbiyya ko sallama baki yi ba”
Yadda taji maganar yasa ta tabbatar da Naufal ne dan iyayin da taji yana yi,ɓacin ran da take ciki ya hana da yin dariya.
Juyowa tayi Zaune ya ke akan one siter ta ganshi yasha baƙin glass fuskar nan a dagule kamar wande ke zaune a cikin bola.
Kamar zata ce mishi wani abu ta fasa,tai wucewar ta zama da sauri.
“Ɗuk ɗady ne zai ja min raini kamar ni za’a ce na zo har gurinta”
Cikin ɓarin rai yayi maganar wanda ɓacin rai har ya samu gurin zama a fuskarshi shiyasa ɓacin rai ke mishi kyau,tashi yayi yabar gidan gaba ɗaya.
Tana isa ɗakinta ta shige toilet ta daɗe tana watsa ma jikinta ruwan sanyi.
“Ba abinda na ya taɓa min rai ban rama ba,karki yi tunanin zan gyale ki dan kin kai ne ƙarshe zan miki abinda sai kin zubur da ƙwalla da idanuwan ki,kuma sai kin ce na haifu ni sabreen muh’d mai taƙama,bana ɗaukar bashi” wasu zafafan hawaye suka biyo kyakykyawar fuskarta.
Tana cikin yin Sallah hajia ta shigo ɗakin ,zama tayi har ta idar.
“Ƴar aljanna lafiya ki kuwa ,ki faɗamin abinda ke damunki zan miki maganin shi komeye shi”
Sabreen bata iya ɓoye ɓacin ranta ba shiyasa hajia ke ganewa.
Kan jikin hajiar ta dawo ta kwantar da kanta,ta ƙaƙalo murmushi ta ce “ba komai hajia ta kin san ina gaya miki abunda ke damu na,karki damu ba komai”
“Taya ba zan damu ba,dumwarki damuwa take sa ni ”
“hajia zan sha ice-cream muje ki sai min”
“Ice cream to yar aljanna muje direba ya kai mu ko”
Tai saurin katsi ta” a’a Yaya Naufal nake son ya kai mu”
Hmm baka san waye Sabreen ba da zaka min tsawa ni nace ka zo gidan mu ko da zaka sauke fushin ka a kai na ,a zuciyarta ta ke wanan tunanin haɗe da yin murmushin mugunta.
Cikin sigar rarrashi hajiar ta ce “Naufal to shi zai kai mu,karki damu je ki shirya,wai ba alhaji ya ce yazo yau ya miki karatu ba”
taɓe baki tayi “hm ai dan raini ne ba zuwa zai yiba”
“Bari zan haɗa shi da dady ”
Murmushi tayi na jin daɗi ta ce ” to ki kira shi bari na chanja kaya” tana faɗa ta tashi ta nufa gurin kayanta ,ita kuma hajia ta fita falo.
Cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga ta shirya ,rigar ta matuƙar yi mata kyau kuma ta kama jikinta wanda yasa dukkan shape ɗin ta ya baiya na,pich colour ne rigar da ratsin baki,bata ɗaura ɗangwalin ba ɗan karamin gyalen kayan ta yashi a kanta,kana iya hango baƙin gashinta mai santsi,duk da tana da ɗan tsawonta amma tana son dugon takalmi,shi kuwa ta sa ɓaki mai ɗan karen kyau,bata yi wata kwalliya mai yawa ba,huta sai kwalli da pink ɗin jan baki wanda yai ma ƙaramin bakin ta kyau.
Cikin yanga da ƙasaita take saukowa daga matattakalar.
Hango shi tayi a zaune cikin ɓarin rai duk da ɓarin ya saba zama a fuskarshi ,amma yanzu kam kana ganin shi kasan ɓacin ran mai tsanani ne,yai hura hanci yake yi yana wani yamutsa fuska.
Cikin fara’a ta isa fallon ,kallon shi tayi tana murmushin mugunta ta ce “Ya Naufal ina wuni ya gida ya aiki?
Ko kallon inda take bai yiba,ya miƙe tsaye “Zamu iya tafi?ya faɗa cikin salo da ƙaƙale.
Kasa ɗaurewa tayi saida dariya a zuciyar ta tana faɗin”Bala’i Wai hausa ma sai an mata ƙaƙele wannan da kai ka kawo yare da ni kuwa bani ba koyan magana”
Hajia ta kalle shi rai a ɓace ta ce”Kai kana jin tana gaida kai wai meyasa kake wa yarinyar nan haka ne”
Taƙaici kamar yayi kuka,gashi yanzu da yayi wani abu zata gayawa dady shi kuma baya son ɓacin ran dadyn shi ko kaɗan.
Wani mummunar kallo ya mata ya ce “Me kika ce Sabreen maimaita ban ji ba”
Saida da lumshe idon daya kira sunanta ji tayi kamar ba wanda ya taɓa kiran sunan da daɗi,sabo sunan ya dawo mata,ydda ya kira har zuciyarta saida ta ji shi,amma saboda hali irin da Sabreen cewa tayi haɗe da taɓe fuska”Salo sunan ma da turanci za’a faɗa kai dai abunka yayi yawa”
A zuciyarta tayi wanan mgnr amma a fili cewa tayi” Cewa nayi ina son ganin gari,zaka kai ni duk inda ka sani”
Bai san lokacin da wani tsadaddan murmushi ya fito ba saida jin haƙurin shi a waje iskar falon ta duke su.
Ba komai ne ya haifar mishi da wanan tunann ba sai jin mamakin sabreen da ƙarfin hali,ita gani take ita me wayau ce.
“Laaah ashe ya iya murmushi to ko me yasa yayi ? ohhhon mishi .
Ta tambayi kanta sanan ta ba kanta amsa.
Har ya bar falon ,binshi a baya suka yi ,yayi tunanin a gaba zata zauna sai ya ga kuma ta zauna a baya.
Sai zubawa hajia shagwaɓa take yi da biyu ganin yana ɗan gutun tsaki yasa ta ƙara yinta da salo ma.
“Kun lalata yarinya,kun koya mata fitsara” a zuciyarshi yake wanan maganar.
ostrich bakery wanda ke unguwar sarki ya fara kai su,kaya mai yawan gaske ta zaba duk da biyu tayi hakan dan hajia ta saka Naufal ya ɗauka.