NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Murmushi yayi dan ta bashi dariya ma,”Ba zan ƙara ba.”
“Idan ka ƙara xan gayawa Dady da hajia.”
“Na yarda yan zo taso nayi miki wanka.”
“A’a bana so.” ta saki kuka,kallon ta yake yi yana jin wani irin mugun son ta na ƙara yawa a ran shi.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin daɗi da ƙaunar juna tun sabreen bata yarda tana son naufal ba har ta yarda.
Farrah kuwa an daidaita da doctor zaina an saka ranar bakin su,lokacin sabreen na ɗauke da ciki.
Sakina kuwa ita da salma sun zu gurin naufal da iyayen shi duk su ka gaya abinda ya faru,dady kuwa har kuka yayi shi da momy da ma hajia,suka ƙara godewa sabreen dan ba dan ita ba da basu hakura ba,sun yafe mata har sabreen wacce daman bata da riƙo ka kaɗan.
An yi bikin farrah cikin jin daɗi an gashe naira dan lokacin naufal ya zama babban mutum mai ƙuɗin gaske,bayan bikin da sati biyu Sabreen ta haifi ɗa namiji sunan mahaifin ta ya ci su ke kiran shi da Ayman kyakyywan yaro mai kama da iyayen shi,bayan sun yi arba’in.
Suka tafi kasa mai sarki saida,sanan su ka wuce malesia anan Sabreen zata cigaba da karantun ta.
Bayan shekara hudu Sabreen ta gama karantun ta computer ta karanta,a lokacin ta ƙara haihuwa ƴa mace,ita ma farrah ta haihu.
rawuyar jin daɗi da so da ƙaunar juna,Hajia kuwa girma ya ƙara kamata sosai.
Kwance ta ke kan cinyar shi tana kallon shi tana murmushi shi ma kallon na ta yayi.
“Haske nah!
“Yadai Baby nah
Saida ta murmusa sanan ta ce ,”Haulat zamu saka wa ƴar mu.”
Ɗa ƙyar ya iya maimaita sunan,”Haulat wani irin suna ne kuma haulat,ba daɗi ki canza wani.”
Murmushi tayi a ranta ta ce,”Hm ni Sabreen na saka ka manta da haulat kamar yadda na faɗa.”
A fili kuwa cewa tayi,” to mu saka mata Amina ko khadija ko fatima.”
“Sunaye masu daɗi da daraja,dukka ya kamata mu saka mu su sunan fa,dan haka yara huɗu xamu ƙara ya kashe mata ido…
*ALHAMDULILAH*!
[ad_2]