NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

“Washh hajiata ba zan iya kai kayan na n gurin motor ba”
“To daman ai ba ke zaki ɗauka ba Naufal zai ɗauka”
Juyowa yayi ya kalle hajiar.
“Ko ba zaka ɗauka ba ne”
kasa magana yayi dan ɓacin rai bai iya cewa komai ba ya ɗau kayan,har yayi dan nisa Sabreen ta kira shi “Ƴaya tsaya na duba wani abu”
Tsayawa yayi yana mata wani irin mugun kallo ,wani murmushi yayi na mugunta dan ya ga yadda zai mata ,ruwan da ke hannun shi ya kalla,a hankali da dubara ya buɗe ruwan yayi kamar zai sha ya zubar a ƙasan gurin.
Allah sarki Sabreen bata sani ba,kuma dai ita ma bata san ba ko wacce fansa ake ɗauka ba.
Cikin yanga ta tawo habba sai jinta tayi dimmm ta zame ta faɗi har saida ƙafarta tayi ƙara.
“Waiyooo Allah na hajia ta ,ta sake ihuu da karfi.
Da gudu a ruɗe hajiar ta ƙaraso gurinta “Na shigo ukku ƴar aljanna me ya same ki ,gaba ɗaya hajia ta ruɗe .
Ko mutsi daga inda yake bai yiba,kallon su kawai yake yi yana murmushin mugunta.
Sabreen ga raki kasa tashi tayi ita kuwa hajia ta ƙara ruɗewa.
chin chiɓar ta aka yi har cikin motar,shi kuwa ko gyalenta bai taɓa ba,gashin kanta ya mishi kyau bai taɓa tunanin a 9j xa’a samu me kyaun gashi ba.
Motar shi ma ya shiga ya fara tafiya a hankali yake jan motar yana jinta tana raki,murmushi kawai yake yi.
“Yanzu ina zamu?
ya faɗa hankali kwance.
Cikin faɗa hajia ta ce “wacee irin magana ce haka,gana ganin halin da muke ciki”
“hajia daman naji ta ce wai tana son na kaita duk inda na sani ne”
“Toh a hakan”
ta juyo da kallon ta gurin sabreen ɗin “Sannu kinji ko muje asibiti ne?
Da sauri ta ce “A’a muje gida ki shafa min magana ”
“to yadda kika ce ƴar aljanna”
Wanan karan har saida haƙuranci suka baiyana “Wai ƴar aljanna”
Gida ya maida su ,amma bai shigaba a harabar gidan ya tsaya suka sauka yai wucewar shi.
Ranar a ɗakin ta hajia ta kwana.
~~~~~~~~~~~~~
Ƙiran sallar farko hajia ta farka,ɗakinta ta koma.
Sai shidda saura Sabreen ta farka tana farka ta ma manta da tana da ciwo a kafa saida taji zafi,amma haka nan ta ɗaure tayi sallah,ko kaɗan sabreen bata wasa da ibada.
Bayan ta idar ta sallar wata dubara ta faɗo mata,da sauri ta tashi ta hau shirin makaranta,Cikin kankanin lokaci ta gama shiryawa,ƙafar tana mata mugun ciwo amma haka nan ta ɗaure ta sauko ƙasa.
Ɗakin hajia ta nufa tana kiranta”Hajiata! hajiata?
Da sauri hajiar ta durgo daga saman gadon ta “Ƴar aljanna lafiya ƙafar ce..
ganinta da kayan makaranta yasa ta ƙasa maganar.
Murmushi Sabreen tayi dan tasan kallon da hajiar ke mata,mugun ƙarfin hali tayi ta ƙara gurin hajiar cikin tafiya mai kyau ta ce “Kin gani ko hajia naji sauƙi sosai yau ina da test ne shi yasa zanje da ba inda zani”
Cikin wata irin siga hajiar ta ce”Sabreen kiyi hakuri karki je”
Murmushi Sabreen ɗin tayi ta ce “Hajiata wai baki yarda da ni ba ne,baki ga yadda nayi tafiya ba ne,naji sauki sosai zamu yi test ne shiyasa”
Tana ƙarasa maganar ta isa gurin hajiar kwanciya tayi akan ta.
“To Sabreen duk abinda kike so shi zanyi ,dan bana son ɓacin ranki ko ƙaɗan”
Wani lafiyayayyan murmushi Sabreen ɗin tayi ta ce”Hajiata ina sonki !
“ni ma ina sonki Savreen ki kula sosai kinji bana son wani abu ya same ki”
“to hajita zan kula sosai,bari na tafi kar tana yi latti,byee sai na dawo,tana gama faɗa ta tashi.
Hajiyar ta ce “ba zaki bari na raka ki ba ”
“Eh ki huta abinki lokacin har ta bar ɗakin.
Gaisawa da direban suka yi sanan ta shiga motar,a tsorace yake dan jiya yasan planing ɗin su bai yiba,kuma yasan Sabreen bata yafiya ba hakura zata yiba taurin kai gareta.
Jin bata ce mishi komai ba har suka isa makarantar ya bashi mamaki tunani ya farayi wani irin hukunci zata ɗauka kuma.
Ba mutane a makarantar sosai.
office ɗin malama haulat ta nufa kai tsaye ta shiga.
Zaune take akan kujerarta tana duba wasu litattafai cikin wani tsadaddan material wanda yai matukar yi mata kyau,fuskar nan a yamutse kamar kullum.
Saida ta tsorata jin an buɗe kofa ba’a ƙwanƙwasa ba.
Cikin ɓacin rai ta kalli Sabreen”Ke wacce irin dabbace jahila mara hankali”
Har Sabreen ɗin zatai magana ta fasa ko meye ta tuno? ohoo.
Takai tsawon minti talatin a tsaye a gurin ,ita kuma malama haulat ganin bata da niyyar magana yasa ta fita lamarinta ta cigaba da abinda take yi.
Ganin mutane sun fara yin yawa yasa Sabreen ta kalli Malama Haulat ɗin cikin ɓacin rai ta ce”Ke wawiya karki ƙara kira na da waɗan nan sunayen”
“Ɗago kai Haulat tayi cikin mamaki tsaye ta
tashi tana kallon Sabreen ɗin.
Ganin ta tunzura yasa Sabreen ɗin kara faɗin “ni ba wawiya bace ke ce wawiya kuma dabba jahila”
Ran Haulat ɗin yai mugun baci,bulalar take kan tebur ɗin ta ɗauko,ta zubawa Sabreen a jiki.
Haba ai abin naima ya samu ai da Sabreen ta sake wani irin gigitaccen ƙara ta zube ƙasa tana ihuun gaske tana birgema a kasa haɗe ta faɗin ” waiyo Allah na zata kashe ni ƙafata ciki na waiyo kaina kai na nashi ukkku hajiata ku taimake ni zata kashe ni!!!
Dan tsabar mamaki Malama haulat tsayawa ma tayi tana kallon ta jikin ta duk ya mutu.
gafin ka ce me office ɗin ya cika da mutane Sabreen tana ganin haka ta fara nishi tana ɗauke numfashi ai sai suka ƙara ruɗewa ga malama Haulat tsaye da bulala a hannunta.
A ruɗe aka ɗauke Sabreen wani ɗaki aka kaita ita kuwa sai ɗauke numfashi take yi tana kiran hajia.
Ganin za’a mata allura ai sai ta fashe da kuka tana faɗin” waiyo ƙafata ku kaini gurin hajiata ƙafa ta ta ƙaryamin ƙafa”
da sauri ya duka ƙarfa ya ganta taji ji kuma ta kumbura duk da ba wani haske gareta ba amma ƙafar tayi ja.
Gaba ɗayan malaman makarantar sun ruɗe suna tsoron kai wani abu ya faru da Sabreen ɗin.
Allura ya mata tana ihuu tana kuka dan bata son allura amma haka nan suka mata cikin ƙamƙanin lokaci barci ya ɗauke ta.
~~~~~~~~~~~~~
Ranshi a ɓace ya kalli haulat wacce ita ma ranta a ɓacen yake ya ce mata”yanzu me kika aikata kina son ki ja mana wani abu ne a makaranta dan baki san waye wanda ke ɗaukan nauyinta ba ne,duk abinda ta miki ba zaki iya kawo kararta ba,zaki yi mata irin wanan dukan yanzu ga shi ta samu matsala a ƙafa,ni wllh yanzu ban san yadda zanyi ba,ansa ya miƙa mata wata takarda.
gabanta yai mummunan faɗuwa kallon takardar ta tsaya yi.
“Ki ansa nace” ya faɗa cikin faɗa.
jiki na rawa tasa hannu ta ƙarɓa.
“mun takatar dake na sati biyu”
Dumm Dumm gaban haulat ya fara faɗuwa da ƙarfin haske haɗe da zaro ido tana kallonshi.
“Tashi ki fita ya faɗa rai ɓace”
jiki ba ƙwari ta tashi…
……………………………………
tirkashi!!!!
gaskiya ni comment na ke so,bana son wani tnx ko wata heart haba ga tawa ga taku ai sai tamin yawa.
ku ƙara gyara zama dn zanyu zan fara.
.
[12/9, 1:07 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: _ ????σѕт ????у ????яσυρ ???? ???? ????уρє ????αυѕα ????σνєℓѕ ????σσк ????нαтѕαρρ 08064400100_ ????????
[12/9, 1:10 PM] ????° ???? D°????⭕Y????????: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*????
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
Page 4
……………………………………………
Fita tayi daga cikin ajin ranta a ɓace,ita kuwa ko a jikin ta daman hakan take so ,tana jin zafin maganganun da Aunty ke gaya mata,shiyasa ta ke son ganin ɓacin ranta.
” *Sabreen* *Muhammad* *mai* *taƙama*”
Da ƙarfi ya kira sunan cikin faɗa.
“Kina ina?yana maganar yana kallon ƴan class ɗin.