HAUSA NOVELNI DA MALAMATA Complete Hausa NovelNOVELS

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

Cikin ɗauki da zumuɗi ya fara shiri saida ya ƙara yin wanka sanan,wasu ƙananan ƙaya ya ɗauko masu kyawun gaske ash colour sun mishi kyau yana cikin saka takalmi wayar shi tayi ƙara jin ringin ɗin dadyn shi yasa ya ɗau wayar da sauri haɗe faɗin “Assalamu alaikum”

“wa’alaikai sallam Naufal yi sauri yanzun nan ka je gidan hajia zasu fita kai so ke son ka kai su kayi sauri sun shirya kai suke jira”

Bai tsaya jiran amsar shi ba ya katse wayar.

Jifa yayi da wayar yana jin wani irin mugun takaici a fili ya ce “Wani irin abu ne wanan kuma duk wanan mara kunyar yarinyar nan ce Sabreen ita zata ce ni take son na kai su dan ta raina ni”

Hhhh allah sarki yana sauri yaje ya rage zafi gurin Haulat Sabreen zata hanashi.

Ranshi a ɓace ya tashi ya ya ɗau key ɗin motarshi rai a ɓace sai hura hanci yake yi ,a ranshi ya ce “Zan gyara miki zama Sabreen sai kin yi dana sanin cewa ni zan kaiki”…

wai ke kuwa sabreen kin ɓuture kowa yana son ɗaukar fansa a kanki.

Idan kuma ta afka da su shikenan.

Ranshi a ɓace ya isa Gidan,yana shiga falon ya hangota da irin kalar kayan shi ranshi ya ƙara ɓace,ji yake yi kamar ya janyota yayi mata mugun duka.

“Sai dai ka mutu dan baƙin ciki amma ni ba zan chanja kaya ba,kuma sai ka kaimu yawo”

Sabreen ta faɗa a zuciyarta tana watsa mishi harara ta gefan ido.

Hajiya ta kalle shi ta ga yana ɓata rai ta ce mishi”Kai Naufal nifa ban san irin haka idan ba zaka kai mu ba,ai da ka gayama wanda ya turoka ,ka zo kana baɗa rai kamar wanda aka yima wani laifi”

Banza yayi da ita,shi a tunanin shi bata sonshi ko kaɗan,dan kullum cikin tsungama da faɗa take mishi

Jiri Sabreen ta fara ji amma dan tsabar ƙarfin hali haka suka fito ita ce a gaba ma,duk dan ta bashi haushi yasa ta hau gaban motor tana murmushin ƙarfin hali.

Har sun fita daga layin su,cikin Sabreen ya fara murɗawa tun tana daurewa har ta kasa wani rikitaccen ihu ta sake.

“Innalilahi wa’inna ilairaji’um shi ta fara faɗa.
“Waiyo allah na hajiata faɗawa kan jikin Naufal tayi da sauri ya taka burkin motar ya tsaya a ruɗe.

Hajia kuwa har ta fara kuka tsabar ruɗewa.

Ai motor ta musu ƙarama dan yadda Sabreen ki juyi tana birgema a ruɗe Naufal ya ɗauko ta kamar ƙaramar yarinya suka fito waje,ƙanƙame shi tayi tana ihu mai ratsa zuciya.

Gaba ɗaya ta kashe mishi jiki dan yadda ta maƙalƙale shi gaba ɗayan ƙirjin ta manne su a nashi ƙirjin.

Ganin ta fara ɗauke numfashi ya ƙara ruɗa su,cikin azama da zafin nama ya sunkuce ta,bayan motar yasaka ta hajia ta shiga,a kiɗime yake jan motar da gudu.

Allah yasa basu da nisa da Special Hospital,suna zuwa likita suka amshe ta da gaggawa aka kaita emergency.

Gaba ɗaya hajia ta ruɗe sai kuka take yi “Waiyo allah na Sabreen karki barni dan allah da me xanji ga rashin mahaifin ga naki”

Naufal ya janyota jikin shi a hankali cikin sigar lallashi ya ce mata “Kiyi shiru hajia ba abinda zai sameta kiyi hakuri”

Duk irin lallashin da Naufal yayiwa hajia taƙi hakuri,sai yanzun ne yaƙe ƙara tabbatar da mugun son da hajia ke mata.

Bayan minti talatin likitan ya fito,hajia tana ganin ya fito ya nufe shi da sauri tana kuka ,cikin kukan ta ce”Liki…likita ƴar…

“Zamu iya ganinta,Naufal y faɗa ganin hajia ta ƙasa magana.

“Eh zaku iya ganinta ,yaew ka same ni a office”

“okk tnx”

Tun kafin su gama magana hajia ta shige,tana shiga ta ganta a kwance an saka mata drip da alamun barci take yi,kusa da ita hajia ta je tana kuka ta shafa kanta ta ƙasa magana.

Kallonta Naufal yayi tundaga ƴan yatsun ƙafarta har zuwa fuskarta,ɗan guntun murmushi yayi ganin fuskar ta ɗauke da annuri duk da kasancewar barci take yi,tsintar kanshi da jin mugun tausayinta yayi,tuno yadda take da tsiwa da ƙarfin hali amma gata kwance,” hmm banda ciwo da yaushe yarinyar nan zata ƙanƙame ni kamar zata haɗe jikinta da nawa guri ɗaya”
ya faɗa a zuciyarshi cike da jin tausayinta.

“To meke damunta?

Wanan tambayar da yayi wa kanshi ita ta tuno mishi da kiran da likitan ke mishi.

“Hajia bari naje gurin likitan ,bai tsaya jin cewarta ba ya wuce.

Zaune yake a cikin office ɗin likitan bayan sun ƙara gaisawa likitan ya jefu mishi tambaya” Kwana nawa take yi idan tana al-ada kuma duk bayan wata nawa take yi”

Zare ido Naufal yayi dan bai san ta inda zai fara bashi amsa ba.

Murmushi likitan yayi ganin halin da yake ciki,sanan ya ce “ba kaine mijinta ba”

Da sauri ya ce”A’a ni yayan ta ne”

“ok to ina mahaifiyarta”

“Mahaifiya ya faɗa a hankali cikin rashin sanin amsar da zai bada.

“A gurin wa take zaune” likitan ya ƙara jefo mishi wanan tambayar.

“Hajia bari na kirata”Naufal ya faɗa y miƙe tsaye ya fita jiki a mace”

Yana zuwa ya ga hajia zaune kusa da Sabreen ɗin tana kuka,tausayin sabreen ya ƙara ji.

Sai yanzu ya tuno da bai gayama su momy ba,wayar shi ya ɗauko ya kira momyn ringin ɗaya tayi momy ta ɗau wayar.

“Hello momy muna asibiti fa Sabreen bata da lafiya”

“innalilah wa’inna ilairaji’un momy ta faɗa a ruɗe.

“Wani asibitin?

“Special hospital.

Yana faɗa ta katse wayar.

A tare suka zo asibitin ita da Farrah,har lokacin sabreen bata tashi ba.

Har gurin ƙarfe goma na dare,Naufal ya so ta farka yana nan,amma taƙi haka nan suka dawo gida,Haulat ta kira shi yafi sau biyar bai ɗauka ba ,bai ma ga kiran ba dan a motor yabar motar.

Yana isa ɗakinshi ya kirata ya sanar da ita abinda ke faruwa,bata ji daɗi ba,shi kanshi ya nuna mata bai ji daɗi ba.

Ƙarfe goma sha ɗaya Sabreen ta farka,ta ganta a gadon asibiti tuno abinda ya faru tayi tsaki ta ja tuno yadda tayi wa Naufal ranta ta ce”Yanzu zai raina ni” ????ji bala’i irin na Sabreen.

~~~~~~~~~~~~~

Tunda sassafe Naufal ya tashi kamar yarda ya saba dai mafarkin nan yau ma hakan,wanka yayi sanan ya shirya,zama yayi yana duba computer tarshi.

kiran Dady ne ya shigo da sauri ya ɗauka haɗe da sallama,faɗa dadyn ya fara mishi mai yasa bai gaya mishi Ankai Sabreen asibiti ba.

Naufal yayi mamaki irin son da suke yiwa Sabreen.

Ƙarfe tara suka shirya suka tafi asibitin har lokacin Sabreen bata tashi ba,dady ya ruɗe ganin halin da Sabreen ke cike.

Shi da hajia suka je gurin likitan tambayar hajia yayi awata nawa take al-ada,Hajiar ta ce mishi”takan kai wata uku ko huɗu ko biyar bata yi bayi ba,amma idan ta fara takan yi kwana bakwai”

Likitan ya ce “To gskeyi dole idan har ana son ta daina wanan matsanaicin ciwon ciki a mata aure.

“Aure! hajiar ta furta a hankali.

Alhaji ya kalli likitan ya ce “to mun gode sosai ya miƙa mishi hannu,sanan suka fito jiki ba ƙwari kowanne da abinda yake tunani a ranshi.

Har lokacin Sallah Sabreen bata tashi ba,Naufal bai so ba,bayan sun tafi sallah ta farka da ƙyar ta samu ta ci abinci sanan tasha magani ta ƙara kwanciya.

Kwana nan Sabreen Ukku a asibiti aka sallame su,har lokacin ba su haɗu ba,Kuma dady ne yakai su gida.

~~~~~~~~~~~~~

Cikin sky blue ɗin material riga da sikit sun mata kyau matuƙa,tafiya take yi tana yanga kamar zata ƙarye dan yadda ta ke rangwaɗa ga dugun takalmi ta saka a bakin glass,tana isa cikin glass ɗin ɗaliban suka tashi tsaye.

“Goodmorning Aunty Haulat!

Saida ta zauna ta gama iyayinta da yamutsa fuska sanan ta amsa musu.

Kamar yadda ta saba koyar da su cikin iyayi da kilibibi yau ma hakan tayi.

Tunda ta shigo cikn ajin ta ke wurga ido ko zata ga Sabreen amma bata ganta ba,tayi mamaki da bata ganta ba,har ta fara tunanin ko latti zata zo nan ma shiru ba amo ba labarin Sabreen a makaranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button