Nida 21

*_????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION_*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
????????????????????????????????
*NI DA AMARYATA*
Na
Khadeeja Usman
2⃣1⃣-2⃣2⃣
Duk da Hajiya kaka taji rashin dadin abinda Nihilar tace,Amma saita danne Dan ta kunnawa Hajiya Hafsa wuta a zuciya, Dan haka ta washe Baki tare da fadin,
“Ah Kai kace raino aka kawo Mana muyi,to ai hakan yayi kyau,Dan wani lokacin sai ana hadawa dama da ‘yan Tara gutsa ko’a Sami biyan bukata,.Amma dama duk gabza- zabzan matan da kake aurowa ai sunada dalilin aurenka,Dan haka ni Sam banyi fushi ba da abinda ‘yar albarka ta fada,Kinga kiyi hakuri kinji amarya wadda Bata laifi,nice Mai laifin Dana shigo inata masifa,al’amarin gidan ne sai sun saka tsinin baki,Amma ba damuwa tunda bakya so nadaina,taho maza mu gaisa”.
Kafada Nihila ta shiga makewa,Dan koyaushe Aunty Hama na fada mata,kada ta sake da mutane sosai,Dan Wasu mugaye ne,hakan yasa ta Kara lafewa a bayan Alhajin.Da kyar ya lallabata taje suka gaisa da Hajiya,wadda sai washe Baki take da yaba kyau irin na Nihila,har cewa takeyi Wai Allah yasa ta Haifa musu irinta me kyau.Koda ta Fadi hakan kuwa,da gudu Nihila ta mike tayi saman bene Wai ita taji kunyar maganar Hajiyar.inda Hajiya ta daga murya tana fadin,”..bi a hankali ‘yar albarka,karda kiyimin asarar Dan jikalle na,Dan da ganin wannan kyan da biyu kikayi shi,kuruciya ta hanaki fahimta”.
Hajiya Hafsa ko,iya wuya takai wuya Dan bacin ran maganganun Hajiya,amma ta boye Dan gudun samun matsala,mikewa ma tayi gaba Daya ta tafi hadowa Hajiyar abin motsa baki,Dan tasan su Amira kin fitowa sukayi Dan gudun tijarar Hajiya kaka.Tana tafiya Nan ma Alhaji Sani ya Kara matsawa ya shiga kara gaisheta,Nan fa Hira ta barke tsakanin uwa da d’a.
*******”””””*******
Yau kwanan Hajiya kaka biyu da zuwa,Kuma kullum da kalar sakarcin da zata gani a gun Nihila,Amma soyayyar samun jika Namiji yasa sam Bata damuwa,hasalima tabar abin a kuruciya ce, yayin data kasa ta tsare tace bazata Bari a shiga hakkinta ba gurin kwananta.
Yau Alhaji nada Baki,Wasu abokan harkarsu ne suka zo,yaso yaje yasamesu suyi maganar a hotel,sai Kuma yaji ya gaji,Dan haka yace suzo gida su sameshi.Falon Daya tanada Dan irin haka anan suke zaune,yasa an cika musu gabansu da kayan motsa baki.
Nihila ce ta sakko sanye cikin Riga da sikert ‘yan kanti,Dan Sam batada wasu nau’in kayan hausawa,Koda ta fito a falo ta tarar dasu Amira da Hajiya Hafsa zaune suna hira, kasancewar yau weekend ne basuda makaranta,cikin dariyarta data Saba ta nufi gurin Hajiya Hafsa tana fadin,” mama kalleni kiga yadda nayi kyau ai nasan nayi kyau sosai,Kuma ko baba ya ganni nasan wallahi sai yace nayi mugun kyau”,sai Kuma tayi narai-narai da ido kamar zatayi kuka,sannan tace,amma na duba dakinshi baya Nan ban San Ina ya tafi ba,ta karasa maganar tana matso kwalla.
Murmushi hajiya Hafsa tayi,da ita kadai tasan ma’anar shi,sai cewa tayi,”ah ah! ba inda yaje,Yana can falonsa tare da baki,kawai kije can ki Nuna Masa kwalliyar ya gani,ta fada cike da mugunta.Ai da gudu Nihila ta nufi kofar fita Dan zuwa gurin Alhaji.Ameera ce ta kalli maman nasu,kamar zatayi kuka tace,”haba ya Zaki turata idan taje ta bashi kunya Kuma fa?Kum……”uwaki Amira! Ta ta katseta,tabashi kunyar Mana,sai me?ko uban wani yace ya auro Karamar yarinyar,wallahi ki kiyayeni Dan Naga yanzu wani sanabe Kika fito dashi na yimin katsalandan,wallahi ki kiyayeni Dan Zan mugun Saba Miki,shashashar banza kawai”,ta fada cikin bacin rai.mikewa Amira tayi tabar gurin,ranta bace da maganganun maman nata,Dan ta fuskanci yanzu maman nata ta fito da wani sabon salon da ada Bata santa dashi ba.Itako Hajiya Hafsa,bayan Amira tabi da harara tana fadin,sakarya kawai,tare da Jan dogon tsaki.
Itako Nihila tana zuwa kofar falon bakin,Bata yi wata-wata ba,kawai ta Danna Kai ciki,can ta hango shi zaune Yana dariya da alama wata maganar sukeyi tsakanin su ta abokai,Bai ankare ba sai Jin Nihila yayi a jikinsa tana fadin,”wa na Kama? Shine ka tashi da sassafe ka gudu ka barni ko,yanzu ma kwalliya nayi shine nace saina Nuna maka,naje dakinka baka Nan shine mama tacemin kana Nan Wai inzo in Nuna maka,kalli kaganni nayi maka kyau ko? Dan Aunty Hama tace idan nayi kwalliya in dinga tambayar ka ko nayi kyau? In kace banyi ba sai in sake wata”,ta karasa maganar tana kallonshi shi Dan Jin amsar dazai bata.
Yana shirin yin magana,yaji muryar Daya daga cikin mutanen Yana fadin,”wow! Alhaji Ina kasamu wannan beautiful din baby’n,ko diyarka ce,Dan dama rowar ganin yaran namu kk mana,Dan kasan haka suke,Dan Kar mu nemi iri ko? Gaskiya to nidai daga yanzu baba Zan dinga kiranka,Dan Ina ruko in lokaci yayi, danni wlh I saw my……ai kafin Alhaji yayi magana kawai sai tsinkayar muryar Nihila sukayi sannan gata gaban wannan mutumin,Dan ya Sosa Mata inda yake Mata kaikayi,wato turancin Daya fara,Dan haka ji sukayi tace,
“Hey abokin baba! Me he you see,is my miji,I love you,Kuma shima he love me,this is soyayyar gaskiya,kasan shi baba ba ruwansa,yacemin Wai shi mij…..Bai Bari ta karasa ba,kawai sai ji tayi ya dauketa cak ya nufi hanyar fita da ita, wutsil-wutsil ta shiga yi tana fadin,”saukeni baba,Dan so nakeyi inyi Masa bayani sosai Dan yasan Nima inajin turanci”.Bai kulata ba har Saida ya Isa kofar falon sannan ya ajiyeta,tare da kallonta,cikin hade Rai yace” wuce ki shiga ciki, mahaukaciyar banza kawai,Inna Kara ganinki idan nayi Baki wlh sai ranki yayi mugun baci,stupid girl kawai!
Ganin yanayin Daya Mata magana yasa ta shige da gudu,tana me fasa kuka,Hajiya Hafsa dake zaune a falo dasu ummi da humaira,duk dariya suka kunshe,Dan su dama sun Fara daukar haske,batabi ta kansu ba ta haye sama tana kuka,Wanda kukanta da Hajiya kaka ta jiyo yasata fitowa tana tambayar me aka mata,duk sukace Basu Sani ba,Nan ta shiga kwalawa Alhaji Sani Kira,jin shima shuru,yasa ta Fara kokarin hawa saman,Dan zuwa taji me aka Mata,duk da ciwon da kafafunta keyi,Amma haka ta Fara hawa saman benen.
Itako Hajiya Hafsa ji tayi kamar sallah,yayin da shi Kuma Alhaji Sani,Yana komawa ya sallami bakin,Wanda lokaci guda sukaga sauyi a tattare dashi.
Yana shigowa falon cikin bacin Rai ya kalli Hajiya,wadda ke zaune ranta fesss,ko ba komai tasa yanzu yafara Jin kunya ai cikin abokai,tunda budurwar zuciya ya aro yanzu ya yafa.
Kallonta yakeyi baice Mata kala ba,sai da yadau mintuna kafin yace yaran su tashi su bashi guri,dukansu sim-sim suka mike Dan barin falon.kallon Hajiya yayi kafin ya fara magana,”yaushe Kika Zama haka Hafsa? Inba rashin mutunci ba kin San halin yarinyar Nan Kika tashi Kika turamin ita Kuma kin San inada baki! A matsayinta na matata ace taje ta same mu ko hijabi babu,kina kallonta Kika barta,wato ma harda fada Mata cewar ga inda nake ko?”
“To meye laifina Kuma? Ta fito ta tambayi Ina kake? nace mata ka fita,Bata wani tsaya jiran me Zan Kuma ce mata ba,tasa Kai ta fice” binta kake son inyi in kamo ta kome?
“Hmmm! Yaushe Kika Fara karya Hafsa? Duk da ban Dade da yarinyar Nan ba,Amma nasan bazata min karya ba,Dan Banga alamun hakan a tattare da ita ba,Idan da bake Kika ce Mata ga inda nake ba,nayi imanin bazata jeba”.
“To Shikenan! Naji Ni na Nuna Mata,laifi ne danta bukaci ganin mijinta nace ga inda yake?”
“Kwarai kuwa laifi ne,tunda ke ai bazaki fita a haka ba,meyasa Baki sata tasa hijabi ba,Kuma meyasa Bakima hanata zuwa ba,tunda kin santa da barin zance ai”.sosai hakan yaja musu bacin Rai domin kuwa fada sukayi Wanda Basu taba irinsa ba,hakan yasa Alhaji ya kuduri aniyar Sanya Nihila makaranta,domin ko ba komai Hajiya tayi Masa gorin wayasa ya auri jahila,Wanda yayi mamakinta kwarai,Dan Saiya ga kamar an canza Masa itane,domin batada wannan dabi’ar Sam Bai santa da ita ba.
*****”””””*****
Tun daga wannan ranar Alhaji yasa aka Nemo Masa Wanda zai dinga koyar da Nihila a gida,amma me? Tunda malamin yafara koya mata,Sam Bata wani maida hankali sosai,hakan yasa Alhaji ya nema Mata makaranta me kyau yasata,Sam ya watsar da duk wani buri nashi akanta,ya dauki aniyar sai tayi karatu,tasan meye rayuwa sannan zai kusance ta.
Sai da ya sanar da Aunty Hama akan ta yiwa Nihilar magana ta dage da karatu,aikuwa Saida tayi da gaske kafin Nihila ta Fara maida hankali.
Ita kuwa Hajiya kaka Koda ta fuskanci ba ciki ne da Nihila ba,Nan fa ta shiga bin kwakkwafi.a haka ta fahimci kamar ba abinda ma ya shiga tsakanin shi da yarinyar,Amma Saida tasan yanda tayi ta tambayi Nihila cikin hikima,wadda ita Sam bama ta fuskanci inda zancen Hajiyar ya dosa ba……..
Haka rayuwa ta Fara ci gaba da tafiya yayin da komai ya Fara sauyawa a gidan Alhaji inda a yanzu abubuwa da dama sun faru.Alhaji Sam yanzu yakoma harkokinshi inda Aunty Hama ta Fara koyawa Nihila hanyar da zatabi ta dinga tambayar Alhaji kudi,aikuwa inta tambayeshi Yana Bata komai yawanshi,domin shi indai a cikin gidan shi ne,to fa baya Jin barnar kudi ko nawa ne,Dan haka yanzu sun Tara kudi masu yawan da suke tunanin sun kusa kaiwa kudin aikin,Wanda ita a tsarin Anty Hama da zarar sun Gama hada kudin aikin to zata San yadda zatayi auren ya mutu.
*Muje zuwa*
_yanzu aka fara_
*Alkalamin khady* ✍