NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 21-30

Tada motar sudais yyi bai ce komai ba suka bar layin, ban da kuka babu abinda khadijah take har da shessheka, duk a tunaninta Umma ta ki hakura ne ta kori sudais, yana driving a hankali yace “Bana son wannan kukan da kike cika min kunne da shi plss, if you are in pain it’s better you pray, plss kukan ki yana damuna da yawa” a hankali khadijah ta hadiye kukan tana share hawayenta a sanyaye, bayan wani lkci sudais yayi breaking silence din cikin motar a hankali yace “Ur step mum is gone Amira” da sauri khadijah ta kallesa xuciyarta na bugawa sosai tace “To where?” Yana ci gaba da driving dinsa yace “Dama ba Nigerian bace Ita?” Khadijah na kkrin mayar da wasu sabbin hawayen da ke taruwa idonta tace “She told me she is not a Nigerian… I don’t knw her country” ya lumshe ido ya bude yace “Toh ta koma kasar su in ji Co wives dinta, since the day before yesterday ta wuce” cikin rawar Khadijah tace “Me yasa?” Kallonta yyi ya dauke kai bai ce komai ba, sai dai baya son gaya mata aurenta ya lalace kamar yanda su Hasana suka gaya masa, Bayan kusan minti biyar murya can kasa yace “Look, you just have to face reality Khadijah, keep all those tears and crying aside, don’t cry any longer it has no use” kai kawai take gyada masa kuka na cin ta amma bata yarda ta yi ba, nan ko shi ma hankalin sa a tashe yake kamar yanda nata yake a tashe amma yayi kokarin boye hakan yana lallashinta ita, bai san yanda xai yi da ita ba, bai san inda xai kai ta ba, bai san inda xai ajiyeta ba, bai ma san ta ina xai fara ba, tunanin hakan yasa yace “Ya Allah” bai san ya fito fili ba sai da khadijah dake ta share idonta ta kallesa, ya shafa kansa yana ci gaba da driving dinsa, Nearest filling station ya shiga domin kara Fuel kafin ya dau hanyar Damaturu, tun da suka shigo station din xuciyar khadijah ke tashi jin warin fetur, ta dai rufe fuskarta da Hijab din jikinta a hankali, Sauke glass yyi yana fadi ma mata mai siyar da man na nawa xata xuba masa, tana fara xuba man khadijah ta fara kkrin bude mota ya juya yana kallonta da mamaki yace “What?” Ganin yanda ta toshe baki yyi saurin bude lock din motar ta fita, tana fita kuwa ta shiga kwarara amai nan kasan wajen, sudais ya dafe kai a hankali a ransa yace Ai shi ya shiga uku…. Ganin wata mata ta fito daga motar dake bayan nasa yasa shima ya bude motarsa a hankali ya fito, matar ta riketa tana mata sannu kamar yanda kowa na gun ke yi mata, sudais ya xagayo ya tsaya ya ma rasa abinda xai ce, mai siyar da fuel din ta tafi gun siyar da drinks a filling station din ta karbo ruwan gora daya ta dawo matar da ke rike da khadijah ta bude ta mika mata khadijah ta karba da kyar tana wanke fuskarta da ruwan, mijin matar dake rike da khadijah ya fito shi ma yana ma khadijah sannu, matar ta kalli Sudais tace “Bari ta shiga motar sai ku wuce” barin wajen sudais yyi matar ta taimaka ma khadijah ta shiga motar sannan ta rufe, mai siyar da mai ta debo kasa tana xubawa wajen aman, Cike da karfin hali sudais yace “Toh mun gode kwarai” matar tace “Ayya ba komai, Allah ya sauwake, ya kuma raba lafiya” Sudais ya juya da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Ameen mun gode” daga haka ya xaga driver seat ya kara yi ma mai siyar da mai da mutanen wajen godiya ya shiga ya tada motar suka bar filling station din, Har suka hau kan titi bai ce komai ba tunanin da yake a ransa daban, can ya saci kallonta yaga idonta a lumshe ta jinginar da kai da kujera, kwantar mata da kujerar yyi ta bude ido da sauri, sai a sannan murya can kasa yace “Sorry” Bata iya ta amsa masa ba ta mayar da idanuwanta ta rufe daga nan bacci ya dauketa. Buga kujerar motar da take kai taji ana yi cikin bacci, ta bude ido a hankali Sudais dake kallonta yace “Come down” kalle kallen inda suke ta shiga yi taga kamar gidan Sudais ne, ganin har ya fita yasa ta bude motar a hankali duk jikinta ba kwari ta fito ta bi bayansa, yana tsaye parlor yana jiranta bayan ta shigo, ya nufi wani bedroom ba wanda ta fara xama ba ya bude ya juyo yana kallonta yace “Go inside xan kawo maki bedsheet yanxu ki shimfida sai ki kwanta ki huta” daga haka ya wuce ba a dau lkci ba ya dawo da bedsheet din ya bata sannan ya fita ya kulle kofar, yanda yace tayi haka tayi ta kwanta a gajiye ga baccin da ke idonta, nan da nan bacci ya sake dauketa, sai kusan azahar ta farka da kyar ta dalilin sanyin da ta dinga ji alamar xaxxabi, cike da karfin hali ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala ta fito tayi sallah, tana idarwa ta jinginar da kanta da gado hawaye na sakko mata, ta dau lkci me tsayi a haka aka yi knocking kofar, da sauri ta dago kanta tana goge hawayen idona, jin an kara bugawa ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, tsaye ta gansa bakin kofar rike da leda babba da karami, bai ce komai ba ya shiga dakin ta bi bayansa, sai da ya ajiye ledan hannunsa yace “Tun daxu kike kuka kenan?” Kai ta gyada masa, yace “Good, kukan me kike?” Kamar ya dada tunxurata ta kuma fashe masa da kuka sosai ta durkushe wajen har da shessheka, cikin raunin murya tace “Ni bani da kowa yanxu, I don’t knw if I have any use, i….” Ta fashe da wani matsanancin kukan, ya durkusa kusa da ita shi ma a hankali yace “Noo, you have use Amira, kar ki sake cewa baki da kowa, or don’t you have trust in Allah?” Ta kallesa da sauri tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace “I do” ya d’an yi murmushi yace “Then have faith in him” ledan da ya ajiye ya nuna mata yace “Ki yi wanka ki canxa kaya, take some fruits after that sai kiyi sllh ki kwanta ki huta sosai” daga haka ya mike ya fita ya kullo mata kofar, ta fi minti goma a durkushe yanda ya bar ta daga karshe ta tashi ta bude ledan taga sabulu har da toothpaste da brush, sannan ga inners da dogayen riguna uku da hijab, duk jikinta yyi sanyi, ta mike ta shiga bathroom din ta yi wanka ta fito, Apples kadai ta iya ci cikin fruits din bayan ta gama shiryawa sannan ta kwanta lkci daya kuma bacci ya sake dauketa. Buga gefen gadon taji ana yi cikin bacci ta bude ido a hankali, ganinsa gefenta ta mike xaune da sauri, yace “Ur temperature is running high, are you feeling pain anywhere?” Ta girgixa masa kai tace “A’a” yace “Ba ki yi sllh ba…..” Kallon agogo tayi taga karfe bakwai ya wuce, ta kallesa da sauri tace “Dare yayi?” Yace “Yea, you slept all day ai” sunkuyar da kai tayi, yace “Me kike son ci yanxu?” Shiru tayi kamar me naxari, yace “Say it” a hankali tace “Kila gyada” ya d’an bude ido yace “What? Groundnut?” Shiru tayi tana kallonsa, da wani expression a fuskarsa yace “Ina xan samo gyada da daddaren nan?” A takaice tace “A titi” kauda kansa yayi, khadijah dake ta kallonsa bayan kusan minti biyu a hankali tace “Ka barshi kawai bana jin yunwa tunda dare yyi, am not even hungry…” wani kallo yyi mata ta gefen ido ya mike ya nufi kofa kamar xai tashi sama ta bi sa da kallo har ya fita, a hankali ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka nmta wanke baki sannan ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma bayan ta idar da sllh, yanda xata koma kan gado ne ta kasa tashi duk jin jikinta take kamar ba nata ba, gaba daya bbu karfi tattare da ita, har bacci ya fara daukarta a xaunen taji an bude kofa, ta dago da sauri, karasowa yyi kusa da ita ya ajiye ledan hannunsa ya koma gefen gado ya xauna, Kallonta kawai yake yace “Ga gyadar, after I’ve gone round of d whole of damaturu” Khadijah ta wara ido tace “All the round of damaturu?” Bai ce komai ba ya hade girar sama da ta kasa, a hankali tace “Nagode” bude ledan tayi taga dafaffen gyada ce da Wanda aka gasa a wani ledan daban, dafaffen ta fara ci, da ta juya xata ga ita yake kallo, duk sh was uncomfortable na kasa cin gyadan, can dai ta sake kallonsa tace “Bismillah” bai ce komai ba, can ya sakko ya xauna kusa da darduman, ya dau gyada daya ya bude, haka ya dinga bude su har suka yi yawa sannan ya mika mata ta karba tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace “Eat” ba musu ta fara ci, ya kuma bude mata wasu masu yawa, ya mika mata, haka ya dinga mata har tace masa ta koshi, yace “Are you sure?” Tana yatsina fuska tace “Kamar amai xan yi” hade rai yyi sosai yace “Don’t try dat malama, kinsan garin da naje na samo gyadar nan” khadijah ta ja baya tana nodding masa kai, can ya shafa kai a hankali murya can kasa yace “Just relax xaki daina jin aman” ta kuma gyada masa kai ta jingina da jikin gado ta lumshe ido, ji tayi aman xai taho mata, ta toshe bakinta da hannu biyu tana girgixa masa kai kamar xata yi kuka tace “Wayyo xuwa xai yiii” tashi yyi da sauri ya shiga bathroom ya debo ruwa, ya dawo ya durkusa kusa da ita ya cire Hijab din jikinta, ya watsa mata ruwan a fuska da gashinta, har ranta taji sanyin ruwan ta koma baya da sauri tana sauke ajiyar xuciya, a hankali yace “Sorry” wani ajiyar xuciya ta kara saukewa jin aman ya d’an lafa mata, ta kallesa da kyar tace “Xan kuskure baki” table water dinsa da ya shigo da ya mika mata ta tashi ta wuce bathroom da sauri, bata fito bayin ba sai da ta amayar da gaba daya gyadar da ta ci, ta fito da kyar ta xube nan tsakiyar dakin tana satan kallon sa tana mayar da numfashi, wani kallo ya dinga mata Daga inda yake xaune, bata sake kallonsa ba ta lumshe ido, lkci daya kuma bacci ya dauketa, gashin kanta taji ana gyara mata ta bude ido da sauri ta gansa durkushe gefenta yace “Ki rufe gashin ki ki hau saman gado” ba musu ta mike xaune ta hade uban gashinta waje daya ta tufke, xata mike tsaye jiri ya kwasheta ta koma da sauri ta xauna yace “Be careful” gyada masa kai tayi ta kuma tashi ta koma kan gadon ta kwanta, ac dake dakin ya rage yace “In kashe maki wutan?” Ta girgixa masa kai, yace “Sai da safe” daga haka ya fita ya kullo mata kofar dakin. Kafin asuba Sudais ya shigo ya fi sau biyar duba ta don da ya bude kofa xata farka, gaba daya ya kasa bacci tunanin yanda xai yi da khadijah ya damesa gashi mami Bata san ya dawo ba ma, shigowarsa na karshe ne ya rufe ta da blanket don xaxxabi ne sosai jikinta, da asuba da ya shigo tashinta tayi sllh amai tayi ba kadan ba kafin ta dauro alwala ta fito, ruwan wanka ya hada mata bayan ta idar da sllhn, da kyar ta yi wankan ta fito, ta kasa shiryawa ta kwanta nn kan gado ya lullubeta da bargo, bayan kusan minti sha biyar ya dawo gefenta yace “Daure ki tashi ki shirya mu tafi clinic” bata ce komai ba don har fuskarta ta rufe, ya cire bargon suka hada ido, sauke idonsa yyi yace “Tashi ki shirya” daga haka ya fita dakin, har ya dawo bata tashi ba, yace “Ke fa nake jira” cikin sanyin murya tace “Ni baxan iya ba” yace “Toh ni xan sa maki kayan?” Bata ce masa komai ba, yace “Look bana son in dawo in gan ki cikin bargon nn it’s better ki daure ki tashi kiyi abinda xa kiyi” juyawa yyi ya fita, cike da karfin hali ta mike xaune hawaye cike idonta, kamar ynda yace mata haka ta dinga daurewa har ta sa kayan a nan inda take kan gadon, tana gama sa wa ta koma ta kwanta, bayan kusan minti goma ya dawo dakin, tsayawa yyi kusa da gadon yace “Toh tashi mu je” rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta mike xaune a hankali tana sauke numfashi, Wayarsa ce ta fara ring, ya daga yana kallon screen din kafin ya xauna da sauri ya daga ya kai kunne tare da sallama yace “Good morning Mami” murmushi yyi yana shafa gashin kansa a hankali yace “Ku yi hakuri Mami ban kira ba, amma in sha  Allah yau xan taho, am done with what am doing” bayan wani lkci yyi mata sallama ya mayar da wayar aljihu, yana kallon khadijah yace “Tashi mu je” daga haka ya nufi kofa, a hankali ta sakko da kafafuwanta kasa tayi karfin halin mikewa, har suka isa compound din gidan bai juyo ba, sai da ya isa gun motarsa ya juyo yana kallonta, can ya bude motar ya shiga, ta karasa ta bude front seat ta xauna ta lumshe ido don ji take kamar wani aiki me wahala tayi, wani babban private asibiti suka tafi, bayan yyi parking ya juyo yana kallonta da kyau yace “Har mu bar clinic din nn bana son jin bakin ki, am nt asking for ur opinion or anything, I am doing wat I think is right, am I clear?” A hankali ta gyada masa kai, yace “Good” da yake da safe ne ba su wani dde ba suka samu ganin likita bayan ya biya kudin kati, ta xauna daya daga kujeran dake kallon likitan, ya xauna shi ma yana facing dinta, hannu ya ba likitan suka gaisa, likitan na kallonta murmushi dauke fuskarsa yace “How you madam, though u look sick” khadijah tayi murmushin karfin hali, likitan yace “Allah ya sauwake, ya raba lafiya,” kallon Sudais dake shafa beard dinsa yyi yace “Drugs xan rubuta maku yanxu da xata dinga sha, there is nothing more I think…. She will get better gradually” Sudais ya ce “Ba abinda ya kawo mu ba kenan Dr, though I knw it might look wrong, but… she got pregnant by mistake, it’s just some weeks old, so plss I want u to get rid of it….” Tunda ya fara maganan likitan ke kallonsa da expression din mamaki, Sudais yyi kasa da murya yace “Yes plss” likitan yace “Sorry we don’t do that hear sir, xaku iya tafiya wani asibitin” kallon Sudais khadijah take kamar idanuwanta xa su fito, Sudais yyi kasa da murya sosai ya marairaice yace “Yeah, I knw it’s very wrong Dr… But she is my…. Wife, the last pregnancy wasn’t funny, and.. She’s breastfeeding an eight month old baby now” kamar ana forcing dinsa yyi magana, likitan sai kallon khadijah yake, Sudais ya ciro handkerchief ya share goshinsa don har xufa ya keto masa yace “Plss Dr, ka taimaka  for d sake of d eight month child” Likitan ya girgixa kai yace “I think xai fi a daina breastfeeding babyn, she shud take care of d one she’s carrying now, sai kaga Allah ya taimaka komai ya xo da sauki” Sudais yace “Nooo Dr, don Allah ka cire mata I will pay what ever amount u request for plss” likitan ya mike ya nufi show glass dake office din ya dauko wani allura da syringe, ya dawo yace “I will give her this injection sauran drugs din kuma xan rubuta maka kaje pharmacy ku siya” Sudais ya sauke ajiyar xuciya yace “Thanks very much Dr, nagode sosai” Lkci daya khadijah t fashe da kuka ta mike tace “Nooo, ni bana son a cire min don Allah ku yi hakuri” bude baki Sudais yyi yana kallonta da mamaki, ta hade hannuwanta tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata a hankali tace “Don Allah kayi hakuri, I don’t want to abort d pregnancy, Allah will be angry with me plss” Likitan ya ajiye alluran ya rungume hannuwansa yana kallonta yace “Ba mijin ki bane kenan?” Hawaye na ci gaba da sakko mata ta gyada masa kai alamar eh, Sudais dake mata wani irin kallo ya mike yace “Sae ki san inda dare yyi maki kuma daga nan” daga haka ya fice daga office din kamar xae tashi sama, a hankali take kuka tana kallon likitan dake kallonta yana girgixa kai, can ta nufi kofa cikin sanyin jiki ta fita, babu motarsa a parking space, ta fita gate tana share hawayen da ya ki tsaya mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button