NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 31-40

 Har Khadijah ta isa bakin titi kuka take bata damu da mutanen dake kallonta ba, ta ma rasa inda xata bi gashi ko sisi bata da shi, all this while Sudais na cikin motarsa yyi parking motarsa ya dinga bin ta da kallo har ta d’an yi nisa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido yana kiran Allah a xuciyarsa, he is just confuse, a hankali ya ci gaba ya fara driving motar har ya iso dai dai inda take ya tsaya ya wani

hade rai cikin tsawa yace “Ina kika san xaki tafi yanxu?” Ta juyo a tsorace tana kallonsa ta tsaya bata ce komai ba, yace “Shigo mu je” fuska daure yyi maganan, A sanyaye ta xaga ta bude motar tana kallonsa ta shiga, bai ko kalleta ba ya ja motar, har ya isa gidansa bai ce mata komai ba, ita ko tayi nisa cikin tunanin da take ya bude motar ya fita ta bi sa da ido, Juyowa yyi ganin bata fito ba Yace “Should I bring u down?” girgixa kai tayi ta fito ya kulle motar ya nufi entrance din gidan ta bi bayansa, kana ganin yanda yake tafiya kasan a gajiye yake, xaune ta gansa parlor ya jinginar da kansa jikin kujera bayan ya xauna ya lumshe ido, a hankali ta xauna kasa ta takure waje daya sbda sanyin parlon, bude ido yyi bayan wani lokaci ya kalleta, suna hada ido ya dauke kai, khadijah dai sai kallonsa take, yanda ya tsura ma ac dake aiki a parlon ido yasa xaka gane tunani yake, a hankali khadijah tace “Xan yi wanka…” sai a snn ya juya ya kalleta, a takaice yace “In kai ki bayin kenan?” Ta girgixa masa kai, yace “Toh tashi ki tafi” mikewa tayi ta wuce dakin da ya saukar da ita, wanka tayi ta fito ta shirya ta sa Hijab, yana nan yanda ta bar sa, har ta iso kusa da shi kuma bai sani ba, duk jikinta yyi sanyi ta durkusa nan kusa da shi cikin sanyin murya tace “I knw I am a burden, u don’t knw where to start from, and u don’t want to send me away cos you’ve got a good heart… You look so responsible to keep me in ur home, you have parent and elders that won’t take it likely…. I don’t want to be d beginning of ur problems, sbda haka nake rokon ka don Allah ka taimakeni ka kai ni gidan marayu kamar yanda na roka a baya, I will cope there in sha Allah, I will take care of the motherless there, but I want u to do me the favour of coming to see me, even if it’s just once in a year plss, I want to feel I have somebody in this world, don Allah kar ka mance ni bani da kowa” tana kai wa nan hawayen dake makale idonta ya sakko, kallonta kawai sudais yake, can ya runtse ido ya bude ya mike ya fice parlorn, hade kai tayi da gwiwowinta tana kuka a hankali tana me tausayin rayuwarta, sai bayan kusan minti talatin sudais ya dawo parlorn, duk da ta ji shigowarsa bata dago kanta ba, muryarsa taji yace “tashi ki shiga daki kiyi kukan da kyau” ba musu ta tashi ta wuce cikin dakin, tayi kukan kamar yanda yace mata har ta gaji ta kwanta ta takure waje daya, bude kofar dakin yyi ya shigo, ta daga kai tana kallon sa har ya iso inda take yana tsaye yace “Good, am hoping all the tears you where planning to shed while in this house kin yi su yau kin gama, cos I am nt gonna tolerate that, clear? Better ki barni in ji da daya” Mikewa xaune tayi ta gyada masa kai tana share guntun hawayen idonta, yace “Me xa ki ci?” Ta girgixa kai tace “Bana jin yunwa” ganin kallonta yake a hankali tace “Toh xan ci apple” yace “Not apple, I mean food” ta d’an yi shiru, can ta dago tana kallonsa a hankali tace “Wainar flawa” wani kallo yake mata yace “Meye shi?” Taace “Da flour, albasa, tarugu, maggi, gishiri and man gyada ake yin sa, Anty Kyauta tayi mana a can gidan” da mamaki yace “A ina xan samo maki shi?” Tayi shiru bata ce komai ba, ya fi minti biyar a tsaye, can ya tabe baki ya fiddo wayarsa a aljihu yayi dialing number ya kai kunne, ba a dau lkci ba ya amsa sallaman da aka yi masa yace “Rabi’ah am on my way now, pls ina son ki min….” Juya ido yyi kamar me son tuno sunan abun, can ya cire wayar a kunne da sauri ya jefa ma khadijah wani kallo yace “Meye sunan ma?” A hankali tace “Wainar flawa” ya mayar da wayar kunne yace “Wainar flawa” Khadijah na jin yarinyar na dariya ya tabe baki ya katse wayarsa ya mayar aljihu ya fice a dakin. Khadijah na nan yanda ya bar ta ya dawo dakin, yana kallonta yace “ermm, ohk let me say Amira, you see xan je gida yanxu, but baxan dade ba xan kawo maki abincin, xa ki iya tsayawa ke kadai ai koh?” Ta gyada masa kai yace “Good, I will be right back now” kashe ac din dakin yyi ya kunna mata kayan kallo daga haka ya nufi kofa khadijah tace “Allah ya tsare” juyowa yyi ya kalleta yace “Amin” daga haka ya fita ya kulle mata kofar. Kwanciya tayi duk da sonta da kallo ta rufe idonta. Tun da sudais ya shiga gidansu yyi parking gabansa ke faduwa ya bude motar a hankali ya fita ya wuce cikin gidan, jin ana soye soye a kitchen ya karasa kitchen din, Rabi’ah ce tsaye tana soya wani abu da bai taba gani ba yace “What’s this” wara ido tayi ganinsa tace “Sannu da xuwa yaya, wainar da kace mana” yace “Dama kamar kwai yake?” Ta gyada masa kai tana yar dariya ya tabe baki yace “Mami fa?” Tace “Tana bedroom da su Anty Maryam” bai ce komai ba ya haura sama yyi sallama kofar dakin maminsa, Kanwar mami da kanninsa biyu dake Dakin ne suka amsa masa ya shiga ciki, kallon uban kayan dake jibge a kasa ta ko ina a dakin, ga boxes masu tsada dake ajiye su ma, dukawa yyi ya gaida mami ta amsa da fara’a tana masa tambayar ya hanya, yace “Alhmdllh” sannan ya gaida Anty Maryam ta amsa da murmushi tace “Welcome barrister” sai a sannan ya amsa gaisuwar kanninsa ya mike ya koma can karshen gado ya xauna, Mami tace “Ka ga sai yau Maryam ta karbo sauran akwatunan xa a xuba kayan ciki yanxu” a hankali yace “Ohk” Mami tace “ka gama gyaran da kace a can gidan naka” ya gyada kai yace “Eh Mami” Mami tace “Toh maa sha Allah” Yana ta xaune har suka gama jera gaba daya kayayyakin a akwatunan, kanninsa su Humairah suka fita dakin ya rage daga shi sai Mami da kanwarta, Mami tace “Lkci na ta tafiya sudais yaushe ka ga ya kamata a kai kayan” tasowa yyi a hankali ya dawo kasan carpet ya xauna kansa a kasa murya can kasa yace “Mami…” Mami dake ta kallonsa kamar yanda Anty Maryam ma ke kallonsa tace “Ya aka yi sudais?” Kasa dago kansa yyi yace “Mami ina son a dakatar da kai kayan nan yanxu ne….” Mami dake masa kallon mamaki tace “Ko saboda me Aliyu?” Ya girgixa kai yace “Mami a dai dakata kawai” Anty Maryam tace “Ko Jiddahr ta yi maka wani laifin ne sudais?” Shiru yyi bai ce komai ba, Mami tace “Toh ni dai abinda xan ce maka a nan shine idan dai kasan ba shiririta bane, ba wani concrete laifi bane ka ajiye wannan shashancin da kake fadi aside, idan kuma kaga laifi ne babba to shkkn” Anty Maryam tace “Ka fada mana me tayi, wani laifin ka kama ta da shi Sudais, Kar mu xama kananun mutane” ya girgixa kai a hankali yace “A bar xancen kawai mumy” Mami tace “Toh Allah rufa asiri” yace “Ameen” mikewa yyi yace “Xan fita in dawo yanxu Mami” daga haka ya nufi kofa Mami ta bi sa da ido har ya fita, Anty Maryam tace “Kar ki tilastata masa don Allah Mami tun da kika ga haka ba karamin laifin ya kamata da shi ba, kin dai san halin sudais da xurfin ciki ko xaki shekara kina tambaya ba fada xai yi ba” Mami dai bata ce komai ba. Sudais na fita ya shiga kitchen ya tarar Rabi’ah ta gama wainar ta xuba masa a warmer, ya bude warmer din yana ta kallon abincin kafin ya tabe baki ya dauka ya fito parlor, da mamaki tace “Yaya ba a nan xaka ci ba?” Yace “Ehh ni da frnds dina xa mu ci, sai na dawo” daga haka ya fita gidan ya hau motarsa ya wuce. Sai da Sudais yyi azahar a masallacin layin gidansa sannan ya shiga gidan misalin karfe daya da rabi, jin an bude kofa Khadijah dake bacci ta bude ido da sauri, karasowa yyi yana kallonta ya ajiye warmer din hannunsa yace “Tashi ga abincin” ta xauna ya bude mata warmer din, ba don tsare ta da yyi ba da daya ma baxata cinye ba amma haka ya dinga forcing dinta har ta cinye biyu, sai dai duk she was restless don amai kawai ta dinga ji, ya hade rai sosai yace “Look idan ki ka yi aman nn I will nt bother my self about ur food again am telling you” hawaye cike idonta tace “Kayi hakuri wllh ba ni bace” ya xauna gefen gadon yace “Toh nayi, amma ki daure kar ki yi…. Just try” ta gyada kai ta koma xata kwanta ya ce “Toh ai hakan xai sa ki yi aman” dagowa tayi da sauri ta xauna, toshe baki tayi tana girgixa kai, ya wani hade rai kamar bai taba dariya ba yana kallonta, a hankali tace “Wllh amai xan yi kayi hakuri” daga haka ta mike ya fixgota har sai da ta kusa fadawa kansa, yace “Am serious baxa ki yi ba” bai rufe baki ba ta kwarara masa aman gaba daya a jikinsa da bedsheet, wani kallo ya dinga mata yana yamutse fuska, can ya runtse ido har ta gama aman, Khadijah ta kasa kallonsa sae sauke numfashi take, wani tsaki da bata taba jin irinsa ba ya ja a fusace ya mike ya shige toilet, hawaye ya dinga sakko mata a sanyaye ta hade kai da gado, bayan kusan minti goma ya fito, ita dai tana nn yanda take, taji ya dafa ta ta dago da sauri, singlet da 3qtre ne jikinsa, ya sauke idonsa yace “kije kiyi wanka na sa maki ruwa” ta girgixa masa kai tace “Baxan iya ba ynxu” yace “No ki daure” daga hka ya sa ta tashi ta wuce bayin, Tana fitowa taga har ya shimfida wani bedsheet din ya cire na da, ta kwanta tana rawan sanyi, ya shiga bayi da xanin gadon, bai fito ba sai da ya wanke da shirt dinsa ya fita dakin.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button